Sashe 274
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta ce." Saboda baki da wayo ko, ba ki tunanin d'adin baki ya yi miki domin ya rama abinda ki ka yi masa a baya wane irin cin kashi ne ba ki yi masa ba da k'yamata saboda ba shi da kud'i, ki yi nazari sosai akan hakan."
Shiru ta yi na d'an wani lokaci kafin ta ce." Inna ki daina wannan tunanin don Allah shi kansa fa dana gaya masa kudirina goyon baya ya ba ni ya ce yana da kyau na yi kokarin ganin na koma hannun uban yarana har yana jaddada mini cewa idan ba tsautsayi ba babu wani dalilin da zai sanya shi rabuwa da matarsa saboda rayuwar yara na shiga garari."
Inna Uwani ta dinga galla mata harara kafin ta ja tsaki ta furta." Ke har wani shiga garari kike hangowa yaran da suke da uba irin Alhaji Tajo.
Suke kuma da uwar riko irin Amina.
Wannan ba hujja ba ce amma tunda kin ce haka ba zan hana ki ba wata'kila gaskiya ne yana buk'atar kudin ne domin d'orawa akan kasuwancinsa tunda har ya amsa tayin da ki ka yi masa sai ku yi abin a sirrin ce yadda babu wanda zai gane da wata manufar kuka shirya auran...........
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *
ALHAMDULILLAHI*
*177*
*SADAUKARWA GA IYAYAN DA ALLAH YA JARABTA DA FITINANNUN YARA IYAYEN DA ALLAH YA JARABTA DA HAIHUWAR YARA MASU DAUKE DA LALURAR JINI SIKILA.
SADAUKARWA GA JAJURTATTUN MATAN DA SUKA YARDA DA RUSHEWAR FARINCIKI SU DOMIN JIN DADIN YARANSU.
SADAUKARWA GA MAZAN DA SUKE HAKURI DA JIMIRIN RIKON MARAYA.
SADAUKARWA GA ILAHIRIN MASOYA MAGOYA BAYANA WANDA NA SANI DA WANDA BAN SANI BA BINTA NA GODIYA NA SAKE GODIYA ALLAH YA SAKA DA ALHERI LITTAFIN GUDUN AURE BIYU NE A MADADIN DAYA DOMIN YA YI MUTUKAR TSAYI SOSAI YA ZAMA COMPLETE A TELEGRAM 2K DOMIN SAMUN DAMAR KARANTA SHI*
*0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
*177*
Wannan shine tunanin Hauwa wanda babu technology ko kad'an a cikinsa.
Lokacin da maganar ta fasu a cikin danginsu sun yi mamaki da k'ananun maganganu amma ganin yadda Sadiya ta goyu da bayan auran ya sanya kowa bakinsa ya mutu.
Ita kanta Hauwan ta yi mamaki sosai amma da ta tuna cewa auran kwangila ne sai hankalinta ya kwanta ta fara tunanin ko mijin nata ya gaya mata yadda suka shirya wata uku kacal za su yi su rabu.
Gabad'aya lokacin idonta ya gama rufewa babu abinda take da buri illah a dauran auran wattani uku suka cika ya saketa kamar yadda suka yi alkawari zuciyarta bata ta'ba yi mata kokwanton wani lamari zai iya kasancewa ba.
Ba mu da labari daka ni har maigidan sai saura kwanaki biyu d'aurin auran Hajja ta kira shi a waya muna tare a dakinsa take gaya masa Hauwa za ta yi aure Inna Uwani ta kira tana gaya mata nan da kwana biyu za a d'aurin auran.
Bai shiga wata wata damuwa ba ya yi fatan alheri suka d'an ta'ba hira kad'an kafin su yi sallama ya kashe wayarsa.
Na d'auka zai d'an nuna kishinsa ko yayane tunda sautari wasu mazan sun tsani su saki mace su ji da gaggawa ta yi aure duk da nasan babu wata soyayyar kirki a tsakaninsu amma ai sun haihu zai d'an ji wani iri sai kawai ma na ga ya d'auki Mufida yana yi mata wasa yarinyar ta yi gwa'bi babu lefi amma dai da mutukar bambanci a hallita a tsakaninta da yan uwanta tun bayan haihuwarta sau biyu kacal ciwon ya motsa mata dalili muna mugun kiyayewa da bin ka'ida cikin kowane yanayi koyaushe tana hannuna na ri'ke na goya idan ta kama.
Allah Ya jarrabe shi da masifar sonta sosai saboda dalilai bambamta sunan Mamansa sannan kuma 'ya macace mai rauni mai kuma rangwamin lafiya.
Zahiri ya so Minal amma kamar yadda Khalil ya fad'a kwanakin baya yanzu dai Mufida ce ke kan karagar mulki don ni kaina idan muna tare bai fiye ba ni lokacinsa ba.
Idan ya d'auketa sai su yi ta wasa itama ta yi sabo dashi tana ganinsa za ta dinga mik'a hannunta tana 'bangale baki ga shi kamarsu daya bayan yanayin ciwonta ta kwashi yanayinsa ta kowane sashi mussaman k'aramin jikin shiyasa abin ya yi yawa 'kank'anuwa ce sosai amma dai babu rama ta tashin hankali a jikinta a murmure take.
Na kasance sosai cikin nazari da tunanin auran gaggawar da Hauwa za ta yi k'asa da wata hud'u da mutuwar auranta babu abinda zuciyata ba ta gaya mini ba akan haka.
Wani sashi na zuciyata na gaya mini wata'kila ta samu wanda take sone kuma mai wadata da wannan nazarin na yi ko'karin ganin na mantar da kaina lamarinta tunda Ubangiji ya datse alakarmu domin ba ni fatan ta sake dawowa cikin rayuwarta har abada addu'ar da a koyaushe nake yi kenan.
Ina ganin status dinta jefe jefi tunda har yanzu muna da serving din lambar juna ban goge ba itama bata goge ba amma ba mu ta'ba yin magana ba idan ta d'ora ma ba ni dubawa saboda har abada ba ni buk'atar abinda zai k'ara had'a ni da ita.
Dalilin da ya hana ni goge lambarta kuwa saboda yaranta a duk lokacin da Khalil ya buk'aci magana da ita zan bashi lambar tunda duk tsiya ai ba canzawa towo suna dole itace uwarsu kuma ba zan d'auki aniyar datse alakar da take tsakaninsu ba kamar yadda koyaushe Babansu ke gayawa yaron ko za su je bauci wajenta sai sun girma ba yanzu ba yaron har ya gaji da bibiyar lamarin ya ha'kura abin yana yi masa ciwo ainun yadda ya damu da ganin irin rabuwar da iyayen nasa suka yi wadda duk wanda zai bud'e baki zai gaya masa cewa babu sauran gyara kuma sun karanta karatun a islamiyya.
****
To wani abu da Hauwa ba ta sani ba shine har yanzu Naziru yana sonta dama a rashinta ne ya auri Sadiya tunda a wancan lokacin ta raina samunsa k'aramin 'dan kasuwa ne yana sana'ar sayar da leda a kasuwa da abinda ya danganci buhu da bacco sai dai inda Allah ya taimake shi shagonsa ne ba haya yake yi ba.
Kuma ya yi kokarin ganin ya gina gidansa mai d'akuna uku da shago a waje d'aya yake kiwon kaji biyu Sadiya take amfani da su shagon waje kuma yaransa da yake duk maza ne yanzu sun zama samari su hud'u suna amfani da shagon amma dai band'aki d'aya ne duk da shi suke amfani a cikin gidan.
Haihuwar da ta yi ne a yanzu ta haifi mace wadda gabad'aya suka d'auki son duniya suka d'ora mata.
D'akin nan da yake kiwon kaji shi ya gyara mata aka yi sabon fenti da sumintin kasa amma dai duk da haka d'akin yana warin kaji tunda ya jima yana kiwon shekara da shekaru d'akin ya game da wari abin sai addu'a.
Ranar da aka d'aura auran ta tare suka kwana a daddafe shi a wajansa hakan ba komai bane tunda ya saba sha'kar warin k'ashin kajin da yake kiwo wanda suka hadu da dusar abicinsu.
Ita kam a wajanta sabon lamari ne da take ganin ba za ta iya jura ba mussaman da wata gaisuwar kirki bata ratsa tsakaninta da Sadiya ba da gari ya waye ta yi tafiyarta wajan aiki gidan kaca kaca gashi bashi da wani girma k'udaje sai shagalinsu suke yi daga cikin d'akinta tana iya jiyo zarnin fitsarin samarin gidan da ya had'u da warin masai yake fitar da wata irin k'alla tunda na gargajiya ne.
Sai shi da kansa ya zuba ruwa a bokiti ya wanke bandakin tukkuna ta iya shiga ta yi wanka yadda ya nuna ai hakan ba komai ba ne tunda ya riga ya saba Sadiya ba ta yin aikin gida sai ta dawo daga aiki to balle kuma yanzu da take ganin ba ita kad'ai ba ce matar gida.
Da wannan matsalar aka fara domin dai rige-rigen shiga band'anki ake yi a gidan samarin yaransu duk nan suke uzurinsu har ma da abokansu idan sun zo wataran ma tana ciki tana uzuri za ta ji ana buga mata kofa wai ta yi sauri ta fito.
Yaran da ada can suke ganin girmanta dalilin amincin da yake tsakaninta da Mamansu yanzu ko kallo ba ta ishe su balle su gaisheta.
Aka dinga fafata rigima sadiya ta yi duma ta barta da yaran sai rashin kunya suke yi mata ita kuma duk abinda take yi na kasuwancinta bata fasa ba gari yana wayewa za ta tafi aiki ranar hutu kuma ta shiga kasuwa sare sare kayan da take sayarwa.
Sai ya zamana Hauwa ke aikin gida ta yi girkin rana da dare koyaushe idan ta yi masa korafin cewa babu ajadanar haka a shara'din auransu sai ya bita da lallami da dadin baki yana ce mata idan bata saki jikinta ta nuna auran soyayya suke yi ba mutane za su fahimci manufarsu.
Hakan ya sanya take gyara gidan har ta yi griki ta kuma wanke bandaki Sadiya na wajan aikinta ta dawo kuma ta d'ibi abinci ta ci ta k'oshi ta yi mata
duma kamar babu sanayya a tsakaninsu
Babu wata maganar arziki sai kame-kame sai hakan ya kara tayar mata da hankali gashi tun farkon tarewarta ta bashi dubu dari biyu da hamsin akan ya kama mata haya koyaushe idan ta yi magana sai ya ce mata gidan ne ba a samu ba.
Haka ta yi wata biyu a daddafe a gidan lokacin sun yi fito na fito da Sadiya uwarka ubanka sun kuma yi wa kansu tononan silili har Sadiyan na fad'in indai Naziru ne gata nan gashi nan ai ba tomo ba ne kuma ta kama kafar wala tunda duk mazajen da suke gari ta rasa da wanda za ta yi auran kisan wuta sai da mijinta.
Lokacin ne maganar ta fasu a dangi iyayensu maza kowa ya san dalilinta nayin auran kisan wuta don ta koma gidan tsohon mijinta ne.