Sashe 89
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Magungu
a ya had'a mini tare da ba ni shawarwari da yadda zan yi amfani da maganin ya ce mini sun yi waya da Yallabai din ya ce ya iso garin amma yana dambatta wurin mamanshi zai jira zuwansa asibitin kafin ya tafi gida tunda dama aikin dare yake da shi.
Shiru na yi ban iya ce masa komai ba anti Yagana ta yi masa godiya kafin ya fita.
Ina kallonta ta je ta yi wanka ta kimtsa jikinta ta sake zama a gefana ba ta da niyyar cin wani abu bayan gashinan Baba Tabawa ta yi abinci mai kyau Ayuba ya kawo.
Na daure na yi mata magana a hankali ta dube ni amma ba ta ce mini komai ba.
Na ce." Ba ki ci abinci ba anti Yagana."
Kanta ta girgiza a hankali ta furta." Ba na jin yunwa Amina har yanzu ban daidaita ba wallahi jiyan nan na shiga rud'ani ba kad'an ba sai nake ganin kamar za ki tafi ki barni ne."
Hawaye ya sake silalo mata.
Murmushi na yi cikin raina na ce dama abinda take yi wa kuka kenan.
Anti Yagana kenan ai mutuwa kam ta zame mana dole ko na rigata ko ta riga ni babu wanda zai zauna a cikinmu..
Na daure na ce." Ni ma ban ta'ba jin ciwo mai azaba irin na jiya ba wallahi ni kadai nasan halin da nake shiga anti Yagana Allah dai ya takaita mini wahala."
Ta gyada kanta da kulawa ta furta." Gashi ma ashe 'yan biyu ne amma me yasa ba ki taba gaya mini kina da ciki ba Amina, ai ko baki sanar da kowa ba kya gayawa wanda ya yi miki jiya da muka yi waya yana ta fad'a shi bai sani ba."
A dan sanyaye na ce." Anti Yagana shurun da na yi masa shi ya fi alheri domin kuwa nasan halinsa idan ya samu labari zai hana kansa sukuni ne, ni a tawa fahimtar kawai na bari ne duk lokacin da ya zo garin sai ya gani da idonsa.
Ta ce." Wannan ba hujja ba ce ko dan gaba kada ki kara haka ai abin alherine kuma yana da hakki ki gaya masa.
Baki san hakan zai yi masa ciwo ba kenan ga yanayin yadda yake magana a wayar ya tabbatar mini da cewa ya ji haushin abinda ki ka yi......
Akwai pege din da ban baku ba kafin wanda na jiya da daddare ban san yadda zan yi ba wurin tura muku shi.
Wad'anda suke comments section zan tura can sai ku karanta mistake na yi wallahi ku yi hakuri.
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.
Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.
'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.
A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*61*
Na ce." Zan kiyaye in sha Allahu rabbi,
yanzu dai ki ci abinci ba na so na dinga ganin ki cikin damuwa da alhini duk abinda Allah Ya yi daidai ne fa anti Yagana don Allah ki daina daga hankalinki, dama can Allah Ya yi ba rayayyu ba ne."
Ta girgiza kanta da damuwar dai ta furta." Tabbas yadda Ubangiji ya yi shine daidai amma na so a ce kin haife tagwayen nan Amina, amma Ubangiji Allah Ya ba ki wasu, kin gaji Babanmu wurin haihuwar tagwaye ya yi sau biyu Hassana da Usaina da kuma na wurin Ummansu Saminu Hassanan da Usaini.. murmushi na yi tare da
Sunkuyar da kaina kasana furta." Dama ai an ce ana gadonsu bangaran uwa ko uba.
Anti Yagana Allah dai ya ba mu masu albarka."
Ta amsa da Amin babu sukuni a tare da ita.
Ni kuma na sake yin k'asa da kaina ina jin wani abu a can kasan raina
yanzu idan ba dan'uwanka na jini ba wanene zai gwada maka wannan soyayyar da tausayawa.
Tare muka ci abincin amma ni kadan na iya ci nasha maltina tana ci muna taba hirar lamarin Hadiza.
Hamusu ya kira ni a waya ya ce gashi nan asibitin ya shigo dubani domin yanzu daga can gidana yake Yusura ta gaya masa ba ni da lafiya.
Anti Yagana da kanta ta fita ta yi masa jagora muka gaisa sosai dalili tunda na dawo daga abuja ba mu had'u ba sai a waya idan na kira shi ko ya kira ni dangane da harkokinmu ya ce zai tafi amma da yamma za su so tare da Gwaggo anti Yagana ta ce masa sai dai su je can gidana domin kuwa ta ji likitan yana fad'in ya rubuta takardar sallama yana jiran zuwan Yallabai din ne.
Ya ce idan ba su zo da yamma ba to gobe da safe za su je can gidan muka yi sallama ya kama hanya ya tafi shago.
To sai bayan sallar azhar tukkuna suka zo asibitin tare da Hajja da Hajiya Saratu.
Haka kawai sai na tsinci kaina da kasa had'a ido dasu gabad'aya domin hausawa suka ce mara gaskiya ko a ruwa gumi yake yi.
Gabad'aya na kasa nutsuwa domin sai nake ganin kamar za a gane na yi wani yun'kuri a baya.
Hajja sai sannu take yi mini tana fad'in an auna arziki ai tunda cikin ya fita ba tare da wata matsalar ba.
Hajiya Saratu ma ta jajanta mini sosai tana cewa idan da rabo a kusa sai a kara samun wani.
Shi kuwa ogan yana tsaye a gefan kaina tunda muka gaisa ya yi mini sannu bai sake magana ba yanayinsa dai ya nuna jimami da damuwar abinda ya faru.
Jikina ya kara yin sanyi sai na kasa daga kaina na dube shi a lokacin da likitan ya shigo d'akin yana tambaya ko da matsala na girgiza kaina alamun babu komai.
Ogan ya dora hannunsa a saman goshina sai likitan ya dube shi yana cewa." Da zu da muka yi magana da ita ta ce mini jiri ne kadai yake damunta amma in sha Allahu shi ma zai gusa nan da kwanaki uku tunda an dubata sosai babu wata matsala sai ta rashin kwarin jiki, bayan haka kuma ga magungu
an nan masu kyau na hada mata."
Hannu ya ba shi suka yi musabaha da juna yana yi masa godiya yayin da likitan yake jadadda masa cewa babu godiya domin kuwa aikinsa.
Tare suka fita sai hakan ya haifar mini da damuwa don sai nake ganin kamar akwai wani bayani da likitan zai yi masa wanda yake b'oyewa.
Hira suke yi a d'akin tsakanin Hajja da Anti Yagana dama akwai shak'uwa a tsakaninsu tun zuwan da anti Yagana ta yi wajena a lokacin da ina Legos.
Ni kuma jikina duk ya yi la'asar hankalina na can tunanin abinda zai faru domin kuwa nasan ko likita bai gaya masa wata magana ba na tabbatar da cewa sai ya tuhume ni dalilin da ya sanya na yi shiru ban gaya masa samuwar cikin ba tsayin wattani uku da satika.
La'asar a gidana ta yi mana tare gabad'aya muka dunguma har dasu Hajja a ka yi sa'a kuwa Baba Tabawa tana ta hidimar abinci koda ta fito suka gaisa cikin barkwanci take cewa da maigidan towo take yi saboda ta ji labarin zai zo kuma ta sanya an samo mata daddawa da kuka masu kyau tunda ta fahimci ya fi k'aunar miyar kuka fiye da sauran abin ka'di.
Ya dinga godiya kuwa cikin kulawa da sakin fuska wannan dabi'ar tasa ta rashin 'kyama tana kara masa martaba.
Hajja fadi take yi kin kyauta kuwa Tabawa sai ki tu'ka towon da yawa ni ma na tafi dashi na d'umama da safe.
Tashi ya yi ya nufi d'akinsa dake saman bene wanda ya jima a rufe tunda ni duk dabdalata a kasa nake yi ban sake hawa saman ba tun washe garin ranar da na tare a gidan.
Duk da rashin jin kwarin jikina hakan bai hana ni tashi na bi shi bayan shi ba.
Waya yake yi da Sukairaju a lokacin da na shiga d'akin tare suke zo dama tunda shi ya d'auko mu a mota ma.
Na nemi kusa dashi na zauna a hankali Ina nazarin d'akin bai yi wata 'kura ba tunda ko'ina rufe yake da tagogi irin na gilashi da narka narkan labuleye a kewaye babu ma wata kofa da k'ura za ta shigo sai dai idan an dan gyara wasu guraran hakan ba zai zama lefi ba.
Ya kashe wayar yana dubana a tsanake ya furta." Ya gajiya da jikin kuma?"
A hankali na furta." Na ji sauki kai ma ya gajiyar hanya."
"Ban gaji ba." Yafada idonsa a tsaye a kaina.
Sai na yi kasa da nawa idon ina dan jin fargaba kad'an zan yi kokarin ganin na kare kaina ta kowace siga domin kuwa na fahimci zallan rikici da fitina a cikin kwayoyin idonsa."
"Ina so ki gaya mini abinda ki ka taka, kada ki rufe ni Amina domin kuwa babu abinda na tsana a rayuwata sai zamba cikin aminci.
Na kan ji na tsani mutum tsana ta har abada muddin na fahimci cewa yana zaune da ni da wata zuciya ta daban.
Ki fito fili ki gaya mini me kike nema a wajena?
Menene a can kasan zuciyarki dangane da zama da ni."
Cikin nutsuwa na furta." Ban gane inda maganganunka suka dosa ba Baba."
Ya tsira mini ido da b'acin rai a tare dashi kafin ya gyad'a kansa ya ce." Kin san idan wani likita zai b'oyewa kowa wani lamari da ya shafe shi tsakaninsa da mara lafiyarsa ni dai alfarmata da yadda Ubangijina ya karramani a nan gidan duniya ba za a rufe mini wani lamari da ya dangance ni ba.