Sashe 163
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya furta." Tuntuni na mayar da ita ai tun kafin ta haihu har yanzu tana nan a matsayin matata."
Ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in." Alhamdulillahi yanzu ka je can bauchi wurin Uwani ka basu hakuri don ta fusata sosai har suna fad'in ka aiko musu da takarda domin su ajiye sheda."
Ya ce." To yadda ki ka ce haka za a yi in sha Allahu."
Tare da 'yar uwarsa Hajiya saratu suka shirya tafiya Bauchin da wajan la'asar bayan sun yi sallah tafiyar mota za su yi suna fitowa harabar gidan Hajja Yusi ya shigo akan sabon machine wanda Hamusu ya saya masa domin shige da fice zuwa makaranta da kasuwa tunda sun bud'e sabon shagon sayar da takalma na mata da maza a kasuwar kwari to Yusin ke kula da shagon shi da Saminu.
Cike da kwarin gwiwa ya je ya kafe babur din shi kuma Baban sai dariya yake yi ya zuba hannuwansa duka biyun cikin aljihun tazarcen dake cikinsa.
Gabad'aya hankalinsa yana kan yaron fuskarsa kamar gonar audiga.
Ya 'karaso wurin da suke tsaye da sassarafa sai suka rungume juna.
Ya d'an dinga dukan kafadarsa yana fad'in." Abokina." Shi ma yana abokina?"
Suka cika juna amma hannunsu a hade yake ya risina yana fad'in." Baba barka da yamma yaushe ka zo ne?"
Ya dafa kafadarsa yana fad'in." Ban ji ma da zuwa ba, ni ma ina zuwa na tambayi Hajja tace mini ka fita tun safe mutumin ya zama d'an kasuwa."
Yasa dariya yana cewa." Wallahi ai da na san da zuwanka da sai na zauna domin mu gaisa sosai."
Ya ce." Idan kana so mu gaisa sosai ka zo abuja idan ka d'an yi free tunda nasan kana karatu ga kasuwa ko ta hana ka zuwa ne?"
Ya yi shiru yana murmushi kafin ya juya gefan da Hajiya saratu take tsaye tana ta dariya ganin yadda suke cafkewa dama tuntuni akwai wannan sha'kuwar mai karfi a tsakaninsu.
Ya d'an risina yana gaisheta ta amsa tana dariya kafin ta wuce wajan motar da Sukairaju yake tsaye yana jiran zuwansu ya bud'e mata gidan baya ta shiga ta zauna.
Ya ce." Yanzu Bauchi muka nufa amma ina so ka zo abuja kamar yadda na gaya maka duk lokacin da baka da wani uzuri ka duba Momi bata da lafiya, ta kwanta a asibiti jiya muka dawo gida.
Amma alhamdulillahi ta ji sau'ki akwai buk'atar ka zo ka dubata ko?"
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Zan zo in sha Allahu Baba, mun yi magana da Adam kwanciyarta ta farko asibiti shi ya kira ni ma yake gaya mini ban samu zuwa ba.
Ya yi fushi bai gaya mini ba yanzu, in sha Allahu idan Kamalu ya dawo da daddare zan gaya masa."
Ya ce." Hakan yana da kyau, amma baka ba ni amsar dana tambayeka ba mamanka ce ta hana ku ziyartarmu."
Ya ce." Ko daya wallahi Baba, ba ita ba ce kawai dai tunda muka dawo nan din ne ba mu samu zama ba shine kawai dalili amma idan ya dawo zan gaya masa zan kuma sanar da Baba Hamusu."
Ya ce." To madallah aboki Allah Ya ba da sa'a, Allah Ya sa ina gari lokacin da kuka shirya zuwan."
Ya amsa da "Amin Baba."
Wajan motar suka nufa a tare Sukairaju ya d'an matsa da sauri kafin ya bud'e masa motar Yusi ya yi saurin riga shi.
Ya shiga ya zauna kusa da 'yar uwarsa da bismillahi yana fad'in." A gaishe mini da Kamalun idan ya dawo a gaya masa sa'kon Mamanku cewa tana gaisheku gabad'aya."
Cike da ladabi ya ce." In sha Allahu zan sanar dashi Allah Ya tsare Baba."
Ya d'aga masa hannu Yana amsawa da "Amin."
Koda suka sauka a garin bauchi Hajiya Saratu ce kadai ta yada zango a gidansu Hauwa domin shi kam tun a mota ya ce tunda dare ya yi Sukairaju ya kai shi hotel din da ya saba sauka idan ya shiga garin suka kwana da safe a hadu.
Hajiya Saratu ita kadai Sukairaju ya kai gidansu Hauwa bayan ya zartar da umarin da aka yi masa.
masu karanta littafin nan ba ku biya ni hakkina ba ina binku bashi ba wai don baku dashi ba ne.
Na kudi ne yi kokari ki sauke hakki domin abu kad'an da ake rainawa sai ya hana ki kwanciyar hankali.
Allah Ya datar damu.
Dama Hajja ta sanar da Inna Uwani zuwan na su don haka da ta ga Hajiya saratu ita kadai ta shiga tambayarta mai gayya mai aikin ta ce mata tare suke Amma da safe zai shigo kamar yadda ya fad'a.
Inna Uwani sosai ta marabceta ta yi wanka ta yi salloli ta ci abinci Hauwa tana kwance a cikin d'aki ba ta fito ba ta gaisheta ba kuma tana jin motsinta.
Itama kuma inna Uwanin ba ta yi mata magana ba ai ko babu komai tunda ta ganta a gidan tasan akwai dalilin zuwanta Kuma ko banza ta girmeta ta kuma girmi mijin nata yayarsa ce.
Hajiya Saratu abin ya yi mata ciwo sosai amma sai ta share tunda sulhu suka zo bai kamata ta yi wani abin da zai sake harzuka zuciyoyinsu ba.
Da yake d'akuna uku ne a d'akin d'aki daya inna Uwani ta gyara mata da katifa da mashinfidi ta shiga ta kwanta sai da asubahi tukkuna da suka gaisa suka fara tattauna maganar inna Uwani tana fad'in." To dukansu dai babu yaro idan sun yi hakuri sun rungumi auransu sai sun fi kowa mora kuma yaransu su tashi cikin annashuwa tare da tsalle da dara a gidansu domin duk inda uwa da uba suka rabu yara sukan kasance a lalace.
Kuma ban ga dalilin da zai sanya Tajo ya dinga kwashe musu yara yana bawa wata ajiya ba, Saratu ki dubi lamarin nan fa da kyau ki ga ni akwai son zuciya, ba ni so na fiye magana a ga kamar ina goyon bayanta, tana da gaskiya a wannan ga'bar domin abu ne mai wahala uwa ta yarda a d'auki danta a bawa kishiyarta cikin gadara da iko, a kuma biyo ta da ba'kar magana da zagi."
Ta ce." Ni kaina ban goyi da bayan hakan ba Inna wannan dalilin ne ma ya sanya da Hajja ta ce masa ya zo nan din ya baki hakuri na ce ya bari mu zo tare domin bibbiyu tafi dad'i amma tsakani da Allah ita abinda ta yi ta kyauta Inna ki fadi gaskiya.
Daga kowane bangare fa akwai lefi ko musulunci abinda ta aikata rashin imani ne da yin butulci ga Allah."
Inna Uwani ta ce." Umm! to ni dai gaki nan ga Hauwa Saratu idan tana ganin ta gaji da zama da Tajo bisimillah sai ta share d'aki ta zauna.
Idan kuma za ta koma auransa sai ki tambayeta ni dai babu wanda ya isa ya shiga tsakanina da 'yar uwarta a cikinsu."
Tana gama fad'in haka ta tashi tana fad'in.
A dama miki kunu ko kuma shayi za ki sha."
Ta ce." Kunun dai zai fi dama-dama Inna amma a turo mini Hauwan mu yi magana."
Ta juya ta fita tana fad'in." To bari na turo miki ita."
Ta shigo sanye da hijabi babu yabo babu fallasa ta zaune gefan katifar da take zaune ba ta kalle ta ba ta ce." Ina kwana."
Hajiya Saratu ta'ki amsawa tana fad'in." Ba zan amsa ba Hauwa ai kin nuna mini matsayina kamar ni na zo gidanku domin ke amma har na kwana ban isa ki fito ki gaishe ni ba, ke ba za ki canza dabi'u ba ko."
Ta yi shiru ba ta ce mata komai ba.
Sai ta girgiza kanta tana fad'in." To magana ce akan abinda yake faruwa ta kawo ni nan, Hauwa duk wani abu da ki ke jin an yi miki ki yi hakuri ki koma dakinki domin shine farincikin iyayenmu, tare muke da Tajo nasan an jima kadan zai shigo, ya tabbatarwa da Hajja cewa ya mayar dake tun kafin ki haihu kin ga yanzu baki da wata hujja da zata hana ki komawa." Ta nisa kafin ta cigaba da cewa." Yanzu ke ba ki ji kunya ba a ce bare wad'anda aka auro a waje sun fi ki matsayi da shiga zuciyarsa.
Ke ya kamata fa ace kin fifita a cikinsu amma kina wasa da damarki.
Zan gaya miki gaskiya ba ki kyauta ba, abinda ki ka yi ba daidai ba ne, kuma kin ba mu mamaki, yanzu Hauwa
ko da babu aure a tsakaninki da Tajo ba za ki iya kula masa da yara ba?
Ko daga waje ya auro ki bai kamata ki yi abinda ki ka yi...........
Ta katseta kafin ta k
rasa tana fad'in." Anti Saratu ban ga lefinki ba don kin kare shi, ai nasan babu wanda zai ta'ba goyon bayana balle a nuna masa cewa bai yi mini adalci ba, ya kyare ni, ya tsangwame ni a gidansa, ya fitar da hannu ya dake ni, ya kira ni jahila mara tarbiya duk a gaban matayensa .
Ya nuna musu kan dole yake zaune da ni, na haihu ya nuna mini iko akan abinda na haifa baiwa ce ni, ko kuma jaka ce, ai kudi na hauka ba ne, kuma itama Amina ai ubanta talaka ne mai yasa ya fifita ta a kaina, mai yasa yake rangwanta mata.
Idan ya daukaki Maryam domin yana ganin tana da dukiya daidai take da shi, ai ta wani gefan na fi Amina usuli tunda kaf dangin mahaifina fana uwata babban family ne, ya za a yi na yi rayuwar 'yanci da jin dadi a tsakanin kishiyoyin da aka nuna sune suke da mutunci a kaina."
Ta sassauta tana fad'in." Ita Aminar ce ta gaya miki cewa ta daban ce a wurinsa.
Ko kuwa kina ganin ta wuce ya yi mata shegantaka idan har tsiyarsa ta motsa, to idan har ma kina tunanin haka ki bari domin kuwa babu wata mace da za ta gaya miki cewa mijinta na yi mata yadda take so ba tare da yana guma mata ba.