← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 276

Sashe 117

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na kuwa bi bayansa da harara ban so ya kyale ni ba a lokacin na so ya tanka na amayar da b'acin ran da ya guma mini ahe da biyu yake ta abubuwa akan yaran saboda suna kama da inna Uwani da kuma 'yarta.

Hawaye suka zubo mini na haifi yaran na ci wuya kuwa ta laulayi da zafin haihuwa amma ko yatsuna babu wadda ta d'auko Allah na tuba ka yafe mini.

Gida ya watse ya rage mu kad'ai.

Ni da Hauwa muka cigaba da rainon yaran a wasu lukutan kuma Hajiya Maryam tana aikowa a d'aukar mata su, har su d'an jima a wajenta kafin su dawo.

Kwanana arba'in da takwas na shirya zuwa kano.

Amma ina jimanta yadda zan yi dawaniyar yaran ni kadai dama burina idan na isa na samu Baba Tabawa mu yi magana idan ta amince mu tafi tare domin zamanta a tare da ni zai taimaka kwarai tunda kaf gidajensa daga na Legos din har na abujan babu mai aiki mace duk maza ne.

Hajiya Maryam ce kawai naga tana da masu aiki dattijuwa mai suna Taburni Mairo kuma itace take yin dawaniya da yaran idan an akaisu can wajenta.

Ya ce Hauwa ta shirya sai mu tafi tare.

Sosai na ji dadin hakan kuwa ban yi nauyin baki ba na yi masa godiya sosai ya ce kwana hud'u kawai ya ba mu dama za mu yi mu dawo.

Kwanakin sun yi kadan amma ban iya gaya masa ba saboda Ina gudun ya ce ya fasa ma gabad'aya tunda har yanzu yana jin haushin abinda na yi masa sharewa kawai ya yi saboda yasan idan ya ce zai rama sai mun yi dan karamin ya'ki a gidan.

Ni kuma fahimtar a kusa yake ya sanya nake ta lallabawa kada ya ce ba zan je ba.

Alhamdulillahi lafiya lau muka sauka a kano.

Gidana na sharad'a muka sauka inda muka iske shi tsaf Baba Tabawa da Yusura sun gyara ko'ina har an yi mana abinci.

Na yi mamaki kwarai da gaske nasan wannan aikin ba na kowa ba ne sai Sahura domin mun yi waya da ita ana i gobe tafiyar har ta na yi mini tambayoyi ashe abinda ta shirya kenan.

Hidimar tace yin cefane mai kyau ta kuma sanya a yi mana abinci mai rai da lafiya.

Cikin zuciyata na sake kud'ire wani alheri da ya jima a cikin zuciyata.

Da daddare Ayuba ya shigo mana da kayan abinci ya kai a store bisa umarnin maigidan ne ya tsaya muka gaisa sosai kafin ya juya ya fita.

Ko da na gayawa Baba Tabawa kudirina ba ta yi jayayya ba ta ce ta amince za ta bi ni duk inda zan je, yadda na nuna mata tausayi da kulawa a lokacin da take neman d'auki yanzu ne daidai lokacin da za ta biya ni.

Ina dariya na ce mata ai ni don Allah na yi mata ba don ta biya ni ba.

Daga ranar kuwa ta shiga hidima da yaran bakid'aya.

To duk inda ya kamata na je a tsakankanin kwanakin da ya ba ni mun je ne tare da Hauwa domin duk inda na ajiye kafata itama nan take ajiye tata.

Baba Tabawa na goye da Hassana ni ina goye da Usaina ita kuma Hauwa tana ri'ke da Khalil a hannunta.

Ayuba ne ke jan mu a mota rana ta farko a gidan Gwaggo na yini sai yamma muka yi mata sallama muka nufi gidanmu anan muka yi magariba.

Sannan muka nufi gidansu Sahura dake kusa damu muka gaisa sosai da mamansu ta d'auki yara ta sanya musu albarka.

Washe gari a gidan Hamusu muka yini amarya ta zama 'yar gari Hamusu kuwa ya rasa Ina zai tsoma ransa ya kai ya kawo ya siyo wannan ya ajiye ya siyo wannan ya ajiye bayan uban girkin da ya sanya aka yi mana.

Sai da na ga abin ya yi yawa tukkuna na yi masa magana sannan fa ya dan samu nutsuwa.

Dubu ashirin na bawa amaryarsa na ce ta sayi janbaki ta kar'ba tana godiya ta rako mu har bakin gate.

Da muka fito tare da shi nake tambayarsa ya ake ciki da karatun Turmizi tunda shine ya shige gaba wajan kai shi makaranta kamar yadda maigidanmu ya yi alkawari nan yake ba ni tabbacin alhamdulillahi an samu cigaba kwarai da gaske domin hankalin yaron ya fara dawowa jikinsa domin lokacin da aka kai shi makarantar ma baya hayyacinsa dalilin irin shaye shayen da ya fara yi ya hadu da wad'anda suka fi shi wayo suka bashi kwayoyi har hankalinsa ya gushe garkuwar jikinsa ta raunana.

A Tasha aka je aka d'auko shi yana zagari da kai kawo tare da sururai.

Ya ce ko wancan watan da ya je dubasu ya same shi garau kuma ya kama karatu ka'in da na'in domin malaman a tsaye suke a kansa kuma makarantar cike take da tsaro babu ta inda yaro zai haura ya gudu.

Kamalu kuwa farkon watan da zamu shiga zasu sallameshi da izinin Allah dama kuma shi mun gama magana dashi zai zauna a hannunsa domin taimaka masa da cigaba da gudanar da harkokin da muke yi na kasuwanci.

Rana ta uku kuwa da wuri muka fita saboda gida biyu nake so mu je, gidan Sahura da gidan Alhaji Muntari can muka fara zuwa saboda nasan idan gidan Sahura muka je da farko bai zama lallai ta bari mu fito da wuri ba.

Alhamdulillahi na ji dadin ganin yadda anti Maimuna ta samu nutsuwa ta kafa sana'a kala uku tana sayar da itace manyan d'auri sannan ga buhuhunan gawayi anan a jibge kusa da itacen sai manja da man kulli da take sayarwa galan-galan.

Lokacin da muke je duka yaran suna makaranta tunda da safe ne.

Na tambayeta Salima ta ce itama ta samu koyarwa a wata nursery dake bakin titi gaskiya ne a lokacin da Babansu yake raye ya yi kokarin sanya su a makaranta da wannan yarinyar ta tsira gashi har wasu suna amfana da iliminta kuma tana samun kwabo da dari.

Na tambayeta Jamila ta ce mini ta ji dai kwanaki an ce ta yi aure amma kuma tana zaune aka zo aka gaya mata wai an ganta a wani hausa film da ta yi bincike sai ta tabbatar da itace din auran ne ya mutu ta shiga wasan hausa.

Sai abin ya ba ni dariya da mamaki cikin zuciyata na ce to Allah Ya kyauta.

Yini zur muka yi a gidan Sahura ta dinga yi mana soye-soye har da su wainar fulawa.

Ta soya mama dubalan cikin bokiti wai mu tafi dashi.

Da daddare kuma ta
hana mu tafiya sai da gama awara nan ma ta cika mana fulas wai idan muje gida sai mu ci a madadin abincin dare.

Sahura kenan sarakan kirki da kyauta......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.

Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*78*
Washe gari ranar da za mu tafi kenan da wuri ya yi waya ya ce sha biyu ta yi mana a filin jirgi domin ya gama yi ma shiri, dama na gaya masa tare muke da Baba Tabawa ya ce babu damuwa, don haka da wurwuri muka shirya na ce Ayuba ya kai ni gidan Baba Sule domin shi kad'ai ne ban je na gaishe ba, ita kanta Hadiza na so na kai mata ziyara amma lokaci bai ba da damar hakan ba, sai da na bawa Ummansu kudi na ce a yi mata siyayya a kai mata.

A gurguje muka gaisa da Baba Sule da iyalinsa na yi musu alheri daidai Gwaggwo sannan muka nufi gidan Hajja wanda daga can din sai kuma mu wuce airport.

Hajja bakinta kamar gonar audiga ganinmu a tare kanmu a had'e sannan ga 'yan jikokinta da take ta burin Allah ya nuna mata su.

Ita kyautarta dama ta turarece domin idan ta je saudiya su take sayowa da dayawa duk wanda ya ziyarceta ta bashi, ta had'o mana da yawa na jiki dana wuta tana ta yi mana addu'a da fatan alheri cikin tsananin farinciki mara misaltuwa.

Ganin da sauran lokaci da muka fito daga gidan Hajja na ce da Hauwa mu je gidan Hajiya Saratu don ni sai na ce zuwana gidanta d'aya tunda nake tunda bata fiye sabga ba yaranta duka biyu maza ne kuma babban yana can Egypt yana aiki da matarsa da yaransa.

Mai bin sa kuma yana chana yana aikin koyarwa a wata makaranta, da yake wanda take aure dan boko ne sosai.

Shiru ta yi mini ba ta ce komai ba yanayinta ya nuna dai kamar ba ta son zuwa.

Nan na fahimci cewa har yanzu akwai rashin jituwa a tsakaninsu tun daga lokacin da suka samu sa'bani akaina basu daidaita ba.

Zaman amana muke yi a yanzu dole a tsakaninmu duk wanda ya hangi kuskure daga b'angaran d'an uwansa idan har da amana bai kyautu ace ya yi shiru ba mussaman idan aka yi duba da cewa ta dalilina suka samu matsala gashi zumunci ne mai karfi a tsakaninsu.

Tun kafin mu shiga mota na nuna mata fa yana da kyau ta gyara domin kuwa kaf Hajiya Saratu ba'asar yin ta ba ce, ta wuce matsayin Yaya a wurinta sai dai uwa, gashi kuma yayar mijinta ce dole ita za ta yi hakuri ta nemi hanyar daidato domin su gyara zumuncinsu tun kafin yaranta su fahimci halin da ake ciki.

Jikinta ya mutu sosai a lokacin da nake yi mata maganar ba kuma ta yi mini jayayya ba ta ce mu je din, dama ai ita bata d'auka da zafi ba, ita Hajiya Saratun ce ta ga kamar har yanzu bata huce ba domin koda ta haifi Khalil ba ta je mata barka ba.

Na ce mata kada ta duba wannan kawai ta yi 'ko'karin gyara kuskuran da ta yi a baya.
Chapter 117 · 0% Book details