Sashe 242
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hakan ya ta'ba ran Hajja sosai ina d'aki ta same ni, ganin yanayinta ya sanya na nutsu ta zauna a gefena tana duba fuskar Usaini ta ce." Wannan tabon kamar sake rinuwa yake yi a fuskarsa Amina."
Na ce." Ni ma na lura da hakan, amma dai Dr Iliyas ya ce babu matsala in sha Allahu."
Ta sauke ajiyar zuciya a hankali kafin ta dube ni ta ce.'' Menene a tsakaninku da Hauwa, Amina kada ki b'oye mini komai wannan lamarin naku ya fara damuna ya kamata a ce kun girma tunda duka babu yaro a cikinku."
A hankali na furta." Babu komai sai alheri Hajja ranar da zan haihu ma mun yi wa da ita a sanina dai babu wata hatsaniya da ta ratsa tsakaninmu."
Ta yi shiru na d'an wani lokaci kafin ta ce." Ki gaya mini gaskiya ta shigo gidan nan tunda ki ka haihu?"
Na girgiza kaina ina fad'in." Ba ta shigo ba."
Ta furta." Ki ce kuma babu komai Amina haihuwa irin wannan akwai dai wani abu da kuke b'oye mini?'
Na ce." Hajja babu komai wallahi ni dai a nawa b'angaran ban san nata b'angaran ba."
Ta ce." Ke ai na yarda dake Amina kuma na gazgataki domin da da akwai matsala za ki gaya mini, Hauwa ba ta jin maganar kowa, ta raina ni ta raina uwarta kuma ba ta jin shawara."
Na yi shiru ban ce komai ba.
Ta girgiza kanta da damuwa a tare da ita ta tashi ta fita.
Sai ta d'an ba ni tausayi domin na gane duk fafutukar da take yi akan gidan d'anta ya gyaru da kamar wuya wai gurguwa da auran nesa Hauwa ta bari hassada ta yi mata illah a rayuwarta.
Da daddare muka yi waya da anti Yagana cewa suna tafe ita da Ya Falmata ta dawo sati biyu da suka wuce.
Na yi musu addu'ar isowa lafiya.
A daran dai da ya dawo wajan goma da wani abin ban jima da yin sallama da su Hajja ba na shiga d'aki domin gasa jikina na kwanta na fito daga toilet na same shi rungume da Hassan yana kafadarsa ya tashi daga bacci yaran suna da tsotso mussaman da daddare Usainin na goye a bayan Taburni yana bacci.
Na sanya kayan bacci a gurguje na kar'be shi domin kuka yake yi sosai na zauna nasa masa nono ya kama.
D'akin ya d'auki shiru na wani lokacin kafin ya ce." Gobe ba'kin nan da na yi za su tafi amma jin labarin k'aruwar dana samu suka ce za su zo yi miki barka wasu labarawan Madina ne sharifai ne jinin Annabi Muhammadu S.a.w suka ce wai na tambaye ki za ki ba su yaran?"
Na dube shi cikin rashin gane inda maganarsa ta dosa na basu yara kamar Yaya?"
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Sun ji irin jikokin Annabi Muhammadu S.a.W ki ke haifa kin san akwai su da kara da karamci da tsantsar ha'din kai
sun ta ya ni murna sosai da abin alheri suka ce a baki."
Dariya na yi na ce." Aikuwa na gode sosai amma dai su yi hakuri ba zan ba su ba."
Yana dariyar shima ya furta." Kai tsaye abinda na gaya musu kenan, sun ce wai ke y'ar baiwa ce ta mussaman kina haihuwar yara masu daraja da albarka."
Murmushi kawai na yi
Ya nisa kafin ya cigaba da cewa akwai kud'i da na bawa Nabila za ta had'o musu kaya akwati hud'u Hasan biyu Usaini biyu idan kin duba abinda bai yi ba ko ake buk'ata sai ki yi magana ko?"
Na dube shi sosai ina fadin." Akan me za ka bata kudi kace ta had'o mini kaya, me yasa ba ka yi shawara da ni ba ko ni ban san abinda ya dace da su ba?"
Ya ce." Hajiya sassauta mana ita ta nema ba ni naga dacewar bata kudi ta sayowa yarana kaya ba business d'in ta ne da take yi kenan da aje waje a sayo sai a saya a wajenta ko?''
Shiru na yi ban ce komai ba.
Ba zan yarda da wannan shishshigi ba duk abinda yake tsakaninsu ba ni buk'atar ji, jiki magayi ne duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwan kan doka.
Ba ha'ka mai ya kawo rami, idan ta yi wari sai mu ji ai!
Ya cigaba da cewa." 'Kiyasin kud'in nan da mutanan nan suka ba ki a matsayin alheri na haihuwar yaran nan sun haura miliyan saba'in.
Ni kuma na ba ki tukwucin 'karamin kamfanina na soap (sarrafa sabulun wanka) wanda yake mariri."
Da wani irin mamaki na dago ina kallonsa miliyan saba'in!
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Kad'an kenan daga irin alherinsu ba wani abu ba ne, kin cancanci fiye da haka Allah Ya yi miki albarka."
Na ce." Me yasa za ka ba ni kamfani guda?''
Kai tsaye ya furta." Saboda ina shirye-shiryen bud'e wani zuwan da suka yi kenan!''
Na girgiza kaina a hankali na ce." A a ba zan kar'ba ba gaskiya ka haihu fa, nan gaba da ni da kai ba mu san iya adadin yaran da za ka sake haifa ba duk neman da za ka yi a yanzu saboda su za ka yi don haka ka bar shi na gode sosai da kulawa da addu'a abinda ka yi wa yarana wad'anda ba kai ka
haife su ba wallahi ya ishe ni."
Ya furta." Wanne yara ne ban haifa?'' Ya tsira mini ido da jin haushin maganata.
Na cire idona daga cikin nasa a hankali na kwantar da yaron ina fad'in." Ni dai ba ni neman fitina don Allah idan alheri ka yi niyyar yi mini ka yi daidai gwargwado wannan ya yi yawa.''
Ya ce." Abinda na yi niyyar bayarwa kenan Amina."
Na yi shiru ban ce komai ba amma zuciyata cike take da mamaki bayan zunzurutun kudi har miliyan saba'in da kamfani guda abin kamar ya yi yawa fa.
Koda su anti Yagana suka zo na gaya musu Ya Falmata ta dinga fad'in bake ki ka ro'ka ba baki ya yi akan me za ki ce masa ba kya so.
Kowace haihuwa da alherinta tunda har ya iya mallaka miki kamfani to dukiyarsa takai ta kawo wata'kila shima bai san adadinta ba, idan kin lura bayarwa yake yi tana sake ru'banya.
Allah Ya kawo wasu abokan nasa su sake baki arzikinki ya ninka na da mu abinda muke so kenan.
Ita dai anti Yagana shiru ta yi da alama yadda abin ya girgiza ni haka ya girgizata.
Ta kasa cewa komai sai kallo.
Zuwansu anti Yagana ya 'karawa gidan walwala domin dama can akwai jituwa tsakanin Hajja da ita gefe guda kuma ga Ya Falmata sarkin barkwanci da bada dariya ta zauna tana ta ba su labarin matan da suke zaman shahada a makka da yadda suke shan tiriri da wahala guje-guje itama abinda ya koro ta kenan.
A daran ranar duka muna falon an gama cin abinci sai ga Hauwa ta yi sallama ta shigo Khalil na biye da ita a baya.......
*GARKUWAR BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*161*
Ni tausayi ma ta ba ni ganin gabad'ayanta kamar a ki'dime take da wannan yanayin na rashin gaskiya da kame-kame duk a k'okarinta na kare a kanta suka gaisa da Hajja tana ta nanata musu cewa ba ta da lafiya a kwance take har yanzu jikinta babu dadi har da 'yar 'kwallarta wai an gaya mata kwanansu biyu da zuwa amma ba su je gidanta ba.
Hajja dai shiru ta yi mata kawai ta zuba mata ido Hajiya Saratu ce ta tanka mata itama ba wata magana mai tsayi da muhimmaci ba.
Yadda dai ta girba 'karya tare da d'orawa kanta ciwo duk mai hankali yasan da cewa k'arya ce tsagwaronta babu wani mashahurin ciwo a tattare da ita balle ya hana ta zuwa duba jininin d'an uwanta.
Ko ba ta zo domin ni ba tunda kishiyarta ce ta zo domin mijinta kuma d'an uwanta balle ma ni ban ga abinda na yi mata mai muni ba da zata sanyawa ranta k'iyayyata mai zafi.
Haka kowa ya bi ta da abinda take fad'i ana ta yi mata sannu da jiki
tana rantsewa da Allah wai bata da lafiya itama.
Ni kuwa na tabbatar da cewa k'arya take yi tunda halinta ne d'orawa kai ciwo haka take yi ko kunya ba ta ji.
Da haka muka gaisa da ita suka gaisa da su anti Yagana babu wanda ya nuna mata wani abu a fuska Ya Falmata ma sai tsokanarta take wai ko itama ta ci wake ne.
Ganin haka ya sanya ta saki jikinta saboda yadda aka goya mata baya cewar bata da lafiya har su Hajjan gabad'aya.
Khalil ya dinga jin dadi yaron ya d'auki yaran d'aya bayan d'aya ya kai mata tana duba su tana dariya wadda nasan ba ta jin dadi ba ce fadi take kamarsu daya da Babansu yadda ake ta fad'a haka take cewa har tana kallona mun fi ki karfin jini Amina.
Ban iya ce mata komai ba sai kallo kawai domin koyaushe sabon darasi nake d'auka daga gareta.
Ana haka maigidan ya sakko ya kuwa ji dad'i ganinmu tare da ita gabad'aya ana wasa da dariya shima ya zauna duk da akwai rashin sakewa tsakaninsa da su anti Yagana mussaman Ya Falmata kunyarta yake ji tunda yasan 'kanwar Mamana ce, bai dai za'ke sosai ba ana hira da shi jefi-jefi hankalinsa ma yafi karkarata kan yaransa da zamansa a wajan ya sanya suka kewayeshi.
Ita kuwa Ya Falmata bata suruktaka da shi ta cigaba da sakin bakinta daidai misali a yi dariya idan ta kama a kuma jajanta a cikin abinda aka tattauna.
Tare suka tafi tunda dama kwanaki d'aya kenan da kar'barta girki gobe ne zai dawo gidana ya kwana.
Washe gari da wuri yarinyar nan Lad'ifa ta zo ta zauna zaman yi mana 'kunshi ta fara yi mini jaa kimanin awa biyu aka cire ta zana mini fulawa ba'ki a kafafu da hannu.