Sashe 170
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mafarki nake yi ina tara dake duk dare kuma na yi wanka." Na ce
"Allah Ya kyauta."
Ya amsa da "Amin.'' Kafin ya ce." Bari zan ta'bo ki kafin na kwanta sai mu yi hira ko?"
A sanyaye na ce." To." Ina mamakinsa duk yanayin alhinin da yake ciki halinsa na fitina yana nan.
Na ajiye waya tare da yin kasa'ke gabana sai ya buga da k'arfi idan na tuna halin da naga matar nan a ciki.
Wayar na d'auka na yi saurin goge hoton ba tare da na sake kuskuran sake gani ba.
To har na kwanta ban ga motsinsa ba.
Da asuba kuwa ina gama ibada kamar koyaushe na bud'e data sakon shi ya shigo kamar iska.
"Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! dana fara gani tun kafin na bud'e sakon shine abinda ya assasa mini 'barin jiki da kakkarwar hannu.
Na bude gabana na bugawa da karfin gaske...
_"Allah Ya yi wa Maryam rasuwa a daran nan ki sanar da duk wanda ya kamata Amina."_ Abinda yake rubuce kenan
Wani irin tsananin tashin hankali da d'imuwa na shiga ina daga zaune na dinga jin tafin kafata na wani irin yammm! hannuna da ke ri'ke da wayar ya sandare wayar ta fad'i saman cinyata.
Ni kaina saukar hawaye na ji a saman dakalin fuskata suna kasa tsare da babban sauti na furta." INNALILLAHI WA'INA ILAIHI RAJI'UN!
Allah Ya jikanki Maryam, Ubangiji Ka yafe wa baiwarka, ashe ciwo ba na tashi ba ne."
Wani mahaukacin kuka mai gunji ya taho mini a guje!
Na sanya tafin hannuna na toshe bakina ina fad'in." Mun shiga uku a wannan duniyar da bata da tabbas Ya Allah!!"
Wayar na laluba da saurin gaske tabbas wannan shi zai zama izna ga Hauwa ya nuna mata cewa babu abinda yake cikin wannan duniyar face rikici da firgici tashin hankali da rashin tabbas
Bugu d'aya wayar ta yi ta daga cikin kukan da na kasa jimirin danne shi na ce." Hauwa Momi ta rasu."
Cike da rikicewar murya ta furta." Wac...wace Momin kike nufi Amina?"
Yadda ta fad'i maganar shi ya tabbatar mini da cewar a ki'dime take...
Na ce." Momi dai da kika sani matar mijinki Hajiya Maryam."
Dif ta yi sai sautin shuhhh! ne yake tashi a kunnana.
Na daga wayar na duba tana ta tafiya.
Sunanta na kira ta amsa a sanyaye "Na'am.
Na ce." Ki sanar da inna Uwani halin da ake ciki Hauwa kin ga dai duniyar ko ita kenan fa."
Ta yi shiru dai bata tanka ba.
Na ja ajiyar zuciya ina jin yadda wani kutittiran abu ya tokare mini a wuya ba komai ba ne face damuwa da tsananin kidima da tashin hankali.
Jin ta yi shiru ba ta ce komai ba sai kawai na datse kiran na nemi lambar Hajja domin ba na tsammanin ta san da rasuwar tunda a sa'kon da ya rubuto mini ya ce na gayawa wanda ya dace.
Sosai Hajja ta gigice da ta ji labarin rasuwar dan har sai da na yi dakacen sanar da ita tunda ita kanta ba ta da koshin lafiya.
Kasa jimirin sauraran kukanta na yi na datse kiran hannuna na rawa na ajiyeta saman cinyata hawayen suka sake zubo mini a saman fuska.
Hannu nasa na sharce na sake saukar waya a karo na uku anti Yagana na kira na sanar da ita domin ta gaya duk wanda ya dace a yi jana'iza da shi.
Na kira Babanmu na sanar dashi shi ma ya tabbatar mini da cewar za su kamo hanya gobe da sassafe shi da Baba Sule.
Jiki a sabule na fita falo baba Tabawa tana d'akinta sai na bita can.
Na sameta tana ninke kayanta ganin yanayina ya sanya jikinta mutuwa.
Rashin kwarin kafafuna ya sanya ni zubewa gabanta na furta." Baba Tabawa Momi ce ta rasu fa?"
"Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Kalmar da ta fara furtawa kenan kafin ta tallafe ha'barta cikin alhini da tace." Baiwar Allah nan ashe ciwo ba na tashi ba ne." Hanci na ja tare da furta " Baba tunda ranar da muka je dubata farkon ciwon Awallahi hankalina ya kasa kwanciya haka kawai daga ta fad'o mini sai gabana ya yanke ya fad'i wallahi ciwon nan nata ya tsaya mini a rai na sosai."
Ta girgiza kai cike da kasala ta ce." To a Amina abin ne da ban tsoro ga yanayin yadda hallittunta suka jirkice ba ke kad'ai ba ni kaina da ita nake kwana da ita nake tashi a rana wallahi Ubangiji Allah Ya gafarta mata ya yafe mata, halinta nagari ya bita don arzikin Annabi."
Da "Amin na amsa tare da cigaba da nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un domin samun nutsuwa da k'adaita Allah da kuma tabbatar da cewa gare shi muke kuma gare shi za mu koma.
Wannan littafin na kudi kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Mun jima muna alhini tare da tariyo kyawawan halinta ( mu kula anan kun san dai a al'ada koda mutum ya ninke (boye ) abinda ya shuka na sharri da rashin kyautawa a duniya babu yadda za a yi a ce rud'ani da razani na mutuwa ya bari mutane su iya furtawa.
Ku sani ko kafiri ne ya mutu a matsayinka na musulmi kaga gawarsa sai ka shiga hankalinka lokacin ne za ka tuna lallai fa ni ma akwai wannan ranar za ta zo mini ba tare da na yi shiri ba.
Zan mutu za kuma a haka rami a binne ni.
Amma ita mutuwa ai mai tonan asiri ce idan an shuka kairan za ta nuna idan sharrin ma aka shuka duka zata nuna.
Mu bi a sannu a hankali a daina yanke hukunci don Allah kuma a fahimci sa'kon da ake so a isar a wannan littafin ta kowace siga zai fita yadda kuke so)
Sahura na kira a waya na gaya mata.
Itama dai kamar yadda yake faruwa a al'ada a kidema take fad'in." Da gaske ta rasu Amina?"
Na ce." An ta'ba wasa da mutuwa dama, wallahi ta rasu da gaske.
" Ta dinga nanata kiran sunan Allah tana istigifari da fad'in Allah ka yafe mana.
Na ce." Mutuwar matar nan ta dake ni wallahi
Sahura ba ki ji yadda nake ji ba a raina na tsorata da wannan duniyar gabad'ayanta.
Ita kanta Hauwa tana can cike da gigita domin kasa magana ta yi da na kira ta a waya na sanar da ita sai kashe wayata na yi domin bakinta ya mutu murus ta kasa magana."
"Ai Amina mutuwa wa'azi ci ga duk wanda Allah Ya sa zai hankalta, duk d'aukaka da sharafin mutum a duniya ba iya tsallaketa.
Mu 'yan adam ai muna da mantuwa shiyasa muke ganin kamar ba za ta zo kanmu ba, a yadda dai kike ba ni labarin irin abinda Hauwa take yi wa matar nan wallahi ita ya fi kamata mutuwar ta dake ta, ta kuma ji tsoron Allah har ta mutu bata nemi afuwarta ba Allah baya yafe hakkin wani akan wani har sai wanda aka zalinta ya ce ya ya yafe, aikin banza ai kishi ba hauka ba ne, ni kaina Hauwa ta ba ni mamaki kuma na raina wayo da iliminta domin jalihi ne kadai ba zai fahimci cewa ba hassada take yi wa baiwar Allah nan ba, misali dani daku duka hasashe muke akanta domin ba mu da tabbas a duniya muke ji ana fad'in mashirika ce amma ai ba mu ta'ba ganinta tana yi ba.
Idan ma tana yi din wannan ita da mahallicinta ne, ni yanzu tsoron duniyar nan nake yi wallahi Amina kowa ya kashe wutar gabansa."
Shiru na yi ina ta auna maganganun da take yi.
Ni kaina na kan zauna na yi ta nazari akan mai yasa Hauwa ta zafafawa matar nan da yawa.
Kishi ne ko hassada mai yasa komai sai ta mayar da shi rigima da sa'insa lefi ni aka yi wa amma ban yi irin abubuwan da take yi ba, tabbas dole a dora ayar tambaya a kanta koda kuwa ba hakan ba ne a zuciyarta ni kaina ba zan fita daga zargi ba tunda yan uwanta da yawa suna ganin cutar da ita muke yi ta hanyar hade mata kai da yi mata tawaye tare da fito da kishi muraran.
Idan zan kwana ina rantsuwa da Allah kan cewa ba ni yi mata hassada da b'akinciki babu wanda zai yarda.
Haka dai muka yi sallama cikin yanayi na damuwa da tashin hankali.
Baban Saude ya kira ni yana tabbatar mini da cewa suna kan hanya suna da d'an yawa.
Na kira Babanmu ya ce mini shi ma sun taso su uku har da Ummansu Hadiza.
Wanka na yi na kintsa na fita falo cikin hijabi har kasa na samu Baba Tabawa itama cikin hijabin da carbi ta kammala abin kari da d'an dama.
Da asuba na ce ta yi abinci da yawa saboda bakin da suke tafe.
Muka gaisa tare da sake yi wa juna gaisuwa.
Masa'udu tare da
Sale suka shigo da akwati kafin shigowar Hajjan Kamalu ne ya fara shigowa tukkuna suka shigo Hajja da Gwaggo da Hamusu a biye a bayansu.
Bakin kofar na isa da sauri ina yi musu barka da zuwa.
Na kar'bi jakar dake hannun Hajja ina fad'in." Gwaggo sannunku da hanya Hajja kun yi sauri sosai fa kamar a hanya kuka kwana."
Suka zauna a kujera tana fad'in." Kina fad'in rasuwar na ce Kamalu ya sanar da Gwaggo maza ta shiryo mu taho
kuma dai Garba ya k'ure gudu sosai shiyasa Allah Ya kawo mu."
Na nutsu sosai muka gaisa a tsanake Hamusu dake can saman kujera mai cin mutum d'aya ya gaishe ni na amsa tare da tambayar iyalinsa da yaronshi Arif da bai wuce shekara uku ba ya ce mini duk suna lafiya.
Baba Tabawa bayan sun gaisa da yi wa juna ta'aziyya na ce ta kawo musu abinci domin bayan karin kummalon da ta yi da yawa har ta kammala na rana
Na dubi Kamalu dake gefe a tsaye jikin labule ya sake girma da fad'i sosai suffa ta mazantaka ta bayyana a tattare dashi har da gemu ya fara ajiyewa.