← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 243 OF 276

Sashe 243

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya Falmatace za ta yi mini kitso idan sun cire lallan da aka yi musu domin ita da anti Yagana sun ce suma ba za a bar su a baya ba.

Wajan biyar na yamma sai ga tawagar gidanmu Gwaggo ce kawai babu domin bata jin dadin shine dalilin da ya sanya ba ta samu zuwa ba tabbas da nasan tare za su taho da su Hajja.

Mamaki ya kama ni sosai mota suka biyo ta haya hakan kuwa bai yi mini dadi ba tunda da sun kira ni sun gaya mini nasan idan na gaya masa zai iya sanya direba ma daga can ya d'aukosu duk yawansa.

Sahura da Yusura da yaronta da ba su jima da yin arba'in ba.

Ummansu Hadiza da Ummansu Saminu Fati da Hassana da Usainar gidanmu sai matar Hamusu itama amma ba ta zo da yaran ba suna can wurin Gwaggo Yusi shine jagora.

Da kuma Ummatu babarsu Sunusi uwargidan Baba Sule kuma k'anwar Ummansu Hadiza ce ubansu d'aya.

Sai Fiddausi yarinyar da ta zauna a hannuna lokacin bud'e gidana na kuntau ita da Yusura a lokacin da na ta fi umara ta farko kaddarar aure ta ratsa tsakani muka rabu ta koma gidansu.

Duk ga su yau dalili ya kawo mini su.

Ita kuma amarya Hajara matar Usaini ana can babu lafiya yadda Fati take gaya mini suna zargin ciki ne da ita ciwo take yi sosai har da su k'arin ruwa.

Ikon Allah kenan
Wannan zugar da suka yi ta tabbatar mini da cewa dama sun shirya sun kuma tsara yadda tafiya za ta kasance amma rashin gaya mini shine abinda ya b'ata mini rai.

Sashenmu na ba'ki dake gidan na sanya aka gyara musu 'yan gidanmu kenan suka yada zango a can su Baba Tabawa na ta hidima da abinda za su ci.

Sahura da Yusura kuma muna tare da su.

Ita kadai ce na san da zuwanta a yau din saboda kayana da za ta kawo mini tunda mun yi waya da Hamusu ya ce mini ya kai mata tun kwana biyu da suka wuce amma shima bai gaya mini matarsa na tafe ba.

Sun yi mini bazata kuma na ji dad'i masu k'orafin ba su ta'ba zuwa ba dalili ya kawo su.

Amma har yanzu ni dashi ba mu tsayar da ranar walimar ba.

Kwana shida da haihuwa a yau din kenan gobe yara za su sake amsa sunansu amma ba ni tsammanin a ranar za mu yi taron walima kamar yadda ya saba duk haihuwar da za a yi masa alamu sun nuna akwai shirye shiryen da yake yi.

A daran da ya shigo na bi shi saman duk da ba girkina ba ne na Hauwa ne amma wasu lukutan yakan shigo ya yi sabgoginsa kafin ya fita kamar yadda idan ya je can yake yi, kuma ban ta'ba kalubantarsa ba ganin yadda shima yake takatsantsan da gujewa abinda zai kawo masa rikici yana wanka na zauna ya fito da ya gan ni a zaune sai ya d'auke kansa ya tafi ya tsaya gaban mudubi kad'an ya shafa basiline a jikinsa ya fesa turare ya sanya kayan shan iska fuskarsa ta nuna mini akwai abinda yake ji wa haushi.

Gaishe shi na yi ya amsa tare da zama gefena na d'an tsura masa ido ina kallonsa shima yana kallona kafin na ji ya furta." Zan ga ranar da zan yi miki abu ki yaba mini Amina har yanzu ban iya ba a wurinki na gode k'warai kin kyauta."
Na ce." Wani abu ne ya faru kuma?" Da wani irin yanayi ya ce." Saboda na baki wani abu da bai kai ya kawo ba shine ki ke bin 'yan uwanki kina gaya musu menene abin magana akan abinda na yi anan a gaya mini hujjar da ta rahamta mini yin kyauta da abinda nake so da dukiyata.

Ke na ce na bawa wannan wuri ba 'ya'yan da muka haifa tare ba.

Ko na ta'ba yi miki wata babbar kyauta duk tsayin zamana dake bayan wannan?"
A d'an sanyaye na ce." Wa na gayawa ka ba ni kyauta?"
Don har ga Allah ban yi tunanin su anti Yagana za su yi masa wata magana ba tunda ni su kadai na gayawa Babanmu bai sani ba haka zalika ban sanar da Baban Saude ba.

Ya gyad'a kansa yana fad'in." D'azu da safe kafin na fita 'yar uwarki ta same ni a haraba tana yi mini wasu maganganu shin me kuka d'auke ni ne? jahili wanda ba shi da ilimin addini ko me? kyauta ke na bawa ba yara ba.

Ko kuwa idan na yi Hauwa ko a ahalinta alheri sai kowa ya sani.

Za ku nuna mini yadda zan yi da abina ne Amina.

Duk abinda nake yi ina sane babu wani yaro da zan haifa walau ke ki ka haifa ko ba ke ki ka haifa ba na fifita shi akan d'an uwansa.

Ko an ce dole idan na kwanta dake a daren girkinki itama sai na kwanta da ita.

An tilasta mini cewa idan na yi jima'i da Hauwa yau gobe sai na yi da Amina?."
Shiru kawai na yi ina kallonsa da mamaki.

Lallai anti Yagana ashe shiyasa ta yi shiru bata tanka mana ba ashe da akwai abinda ta kud'irta a ranta yadda dai ransa ya 'baci hakan ya tabbatar mini da cewa ta fad'i maganar da ta tunzura shi kamar yadda yake nanata cewa dukiyarsa ce kuma duk abinda yake yi yana sane shi ba jahili ba ne.

Ya cigaba da cewa."
Babu d'ayanku da nake da ta'kidin takewa ha'kki ko na fifita yaranta duka ni na haifa kuma babu wanda bana so a cikinsu ina kuma addu'a Allah kada ya kama ni da hak'kinku, hakan kuma baya na nufin na sarayar da iko da mutuncinta ba duk wadda ta yi mini ba daidai ba a cikinku zan yi mata hukunci daidai gwargwadon abinda ta aikata mini.

Idan har ba ki son abinda na baki shikkenan kada ki kuskura ki kara wata magana da wani zai tsaya gabana ya kalubalence ni.

Na duba dacewa da cancanta a kanki ne Mutum nawa ne suke 'kasan ki? kuma mutum nawa suke ci da sha a karkashinki? mutum nawa ki ka tallafa suka tashi? ko kuma kin d'auka haka nake zaune dake kara zube ba ni bin abubuwan da ki ke gudanarwa
arziki na Allah ne amma menene makomar yaranki da koyaushe ki ke nanata mini cewa ba ni ne ubansu ba.

Idan yau na fa'di na mutu a shari'a ba su da gadona.

Idan na d'auki abu na baki sai ya zama lefi da tiri-tiri da magana kamfanin majizai na baki ne Amina?"
Na kudi ne don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Har yanzu bakina a mace yake na kasa cewa komai saboda mutuwar jiki da mamaki duk yadda yake ganin k'ima da mutuncin anti Yagana yau ta kai shi bango tunda gashi yana ba ni sa'ko zuwa wajenta.

Na rasa abin cewa kawai sai na yi shiru da bakina domin ba ni so kuma lamarin ya girmama shi da ita anti Yaganar babu wanda zan za'ba tana da hujja shima yana da tasa hujjar kamfani kuma muddin ana so na kar'ba akashe shi ya daina aiki koma gabad'aya a sayar mini da shi a bani kudin na had'a da wanda suke hannuna alherin da abokansa suka yi mini na nemi plaza cikin kasuwa na saya ko Kuma na sanya k'wararru su gina mini na sake fad'ada harkokina wannan shine magana.

Adamu ne ya kira shi a waya ina ji suka gama magana yana gaya masa gasu nan shi da Yusi za su kawo sa'ko in ji anti Nabila ita ba ta kira shi ba saboda tasan yana gida sai ta sanya yaran.
ya ajiye wayarsa to a nan ne na magantu cikin had'e rai na ce." Ka ajiye wannan kaya domin kuwa yarana ba za su sanyasu ba Allah shine d'aya ko kuma kawai ku yi tanadi kai da ita idan kun yi aure kun haihu shikkenan kun huta.

Ko sun kawo kayan nan a banza, idan lallai sai Nabila ce za ta sayowa yaran nan kayan sanyawa a bar shi kawai zan saya musu a matsayina na uwarsu."
Bai juyo ya dube ni ba ya ce." To shikkenan ai tunda kin ce haka ta riga ta sayo sai a ce mata me? ki a ajiye kada Allah Ya sa ki yi musu amfani da shi din."
Na ce." Ba kuwa zan yi ba, ai ga shawara nan na baka za su yi maka amfani idan kun haihu."
Ya dube ni yana fad'in." Kina da hankali kuwa
Giwa da wa zan haihu?"
Na tare shi da sauri ina ce wa." Da ita mana ko ka d'auka shashashai ne mu, ka ji kunya wallahi."
Ya 'bata ransa yana fad'in." Yanzu ke tsakani da Allah ba ki ji kunyar yi mini wannan maganar ba, duk kalolin matan da suke duniyar nan Amina na rasa wadda zan aura sai wannan matar me zan yi da ita?"
Na ce" Me yasa zan ji kunya tunda kai ba ka ji ba.

Haba Malam babu wata magana da za ka fad'i wallahi tallahi na yarda da kai, ina ruwanka da ita da business dinta ka sayi kaya a wajanta saboda kana tausayata mata ko akwai shagunan sayar da kayan baby's cikin garin nan da yawa me yasa ba za ka je da kan ka ka sayo ba, ka bi dare da rana ka samar da cikinsu sayo musu kayan da za su sanya ne zai gagareka."
Ya girgiza kansa yana ce wa." Ba zan shiga shago sayan kaya ba.

Ni ma wanda nake sanyawa telana ne yake kawo mini su a dinke ya san irin yaduka da shaddodin da na fi so ko tafiya na yi kin ta'ba ganin na sayo muku abu, idan kina ganin za ki iya zuwa ki sayo musu abar maganar don Allah don Annabi zan baki kudi wannan din kuma sai a ajiye idan Allah Ya sanya na samu wasu biyun daga wajan Hauwa shikkenan na huta.

Ta'be baki na yi tare da d'auke kaina ban ce komai ba.
Chapter 243 · 0% Book details