← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 177 OF 276

Sashe 177

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi ma bai jima da zama a wurin ba suka fito can suka hange shi yana kar'bar gaisuwa daga jama'ar da suka yi dafifi domin jiran fitowarsa.

Muna zaune a falo gabad'aya har da su Hajja duk sun yi wanka sun fito ina ta kallon yadda inna Uwani take nan nan da Hajja har goya Sultan a bayanta tana ta jijjigashi duk da ba kuka yake yi ba.

Sai ta ba ni tausayi sosai domin duk tana yin hakan ne domin dakushe lefin 'yarta amma ai ba haushe yace tun ran gini ran zane Hauwa ta bata goma daya bata gyaru ba, duk da gaskiyarta babu wanda zai gani saboda abinda tayi a yanzu ya dusashe lefin da take ji an yi mata.

Suka shigo a tare su uku har da Khali da ya d'an fara tasawa abinda yake burgeni da yaron nutsuwa sam bashi da hayaniya ba za ka ta'ba cewa Tajo da Hauwa ne suka haife shi ba.

Har suka 'karaso wurin da muke zaune ban d'auke idona daga kansu ba, wannan abota da soyayyar ta Yusi da Adamu sai Allah had'uwar jini babu dangantaka ko kad'an sai ta addinin islama.

Duka muka gaisa a tsanake don d'aya bayan daya suka bi suka gaisa da kowa.

Na kasa janye idona daga kan Yusi ganin yadda ya kara zama saurayi wannan jikin da ake yi masa tsiya a kai duk ya rairaye da akwai dai amma ba kamar lokacin da yake tashar kuruciya ba.

Ganin kallon da nake yi masa ya yi yawa ya sanya ya sunkuyar da kansa yana d'an kalato murmushi ya sake fad'in ." Mama ya karin hakuri."
A tak'aice na ce." Ai ku zan yi wa ta'aziyya ko Adamu."
Ya d'an saki fuska kad'an amma bai ce komai ba sai tausayinsa ya sake kama ni.

Na ce." Allah Ya yi mata rahama Annabi ya san da zuwanta.

" Gabad'aya muka amsa da Amin har ni da na yi.

Addu'ar.

Sun d'an jima a tare damu kafin su fita Adam yana tambayar Kamalu na ce ai shi tun sassafe ya fita don ya riga ma maigidan zama a wajen.

Gabansa suka je suka zauna gabad'aya har Salim ya dube shi yana fad'in." Ku kunna wayarta ku sanar da rasuwar duk da nasan da yawa wasu daga cikin abokan nan kasuwancinta sun san ta rasu tunda an yi jana'iza da wasu amma dai
a tambayi idan da wanda yake bin ta bashi ya fad'a a sauke mata nauyi daga nan zuwa ranar da za a yi addu'ar bakwai.

Sannan ka nemi yaranta ina nufin wad'anda suke yi mata hidima ta kasuwanci idan da wanda yake da hakki a kanta ya fad'i a biya shi.

Sanin da na yi ita mai bayarwa ce amma hakan ba zai hana a bibiyi abubuwan da ta wanzar a lokacin da take rayuwa ba, wannan shine gatan da ni daku zamu yi mata bayan addu'a."
Ya amsa cikin ladabi tare da tashi da sauri can rumfar da ya hangi yaranta sun zauna jiya ya nufa wasu sun zo daga ciki wasu kuma ba su zo ba kawai sai ya nufi cikin gidan domin kar'bo wayarta dake hannun Nusaiba tunda Allah Ya taimaka har da manyan wayoyinta masu tsada ta kwashe a lokacin da ta had'a da katin cire kudinta.

Yana nan zaune jama'a na 'barkowa ta ko'ina abokanansa wasu daga cikin abokanan tsohon mijinta da 'yan uwansa dama wasu sam da bai san daga ina suke ba sukan tsuguna gabansa da tafka tafka rawaninsu a kan su suna yi masa gaisuwa.

Wani daga cikin masu rawanin ya sake komawa wajansa ya gurfana Yana fad'in." Allah Ya taimake yanzu yaron mai rasuwar na ji yana magana a wajan da muke zaune cewa idan da wanda yake bin marigiyar bashi ya fad'a, to ina daya daga cikin wad'anda ta sanya a aiki."
Ya dube shi a tsanake kafin ya furta.'' Wane aiki ka yi mata, kuma nawa ne hakkin naka?"
Ya gyad'a kansa tare da dan juyawa yana waiwaye akwai jama'a sosai don dai hayaniya tayi yawa amma duk da hakan ko da suke maganar bai fasa kar'bar gaisuwa ba tunda har yanzu shigowa ake yi.

Cikin nazari ya ce." Ko akwai buk'atar sirri ne?"
Da sauri ya d'aga kansa yana fad'in."E, kwarai kuwa Yallabai."
Sai ya ce." To babu damuwa fita waje ka tsaya jikin gate zan fito yanzu na same ka."
Ya kuwa tashi da sauri yana sa'be babbar riga ya kama hanyar fita.

Ya bi shi da kallon nazari kamar akwai rashin gaskiya a tare da shi.

Yaran duk suna gefensa a zaune ya tashi ya bi bayansa.

Ya zuba hannuwansa duka biyun cikin aljihun tazarcen dake jikinsa tare da fad'in." To ina jin ka Allah Ya gafarta Malam."
Ya risinar da kansa yana fad'in." Hakika Maryam ta sanya ni aiki babba a wannan tsukin da Ubangiji Allah Ya d'auki rayuwata.

Mun gama magana da ita akan kudin kayan aiki da duk abinda za a buk'ata wurin biyan buk'ata dubu dari bakwai da ashirin to sai ta kwanta ciwon nan da bata tashi ba daga shi kuma ba ta turo mini kudin ba ni kuma na juya dana hannuna na fara aiki domin nasan bata da wasa akan samun biyan bukatarta wallahi yanzu haka daf nake da kammala aikin kwatsam sai rasuwarta na ji kuma dama a satikan da suka wuce ba ni samun wayarta hankali ya tashi wallahi domin na riga na juya mata kuma kaf abinda yake hannuna kenan."
A tsanake ya ce." Wane aiki ne? kuma nawa ne kudinka."
Ya yi dan Jim kafin ya ce ." Duka dubu dari bakwai ne da ashirin kamar yadda na gaya maka da farko abinda ya ja kud'i shine rago mai tozali da muka nema akan aikin.

Sai fatar karsana sannan mun nemo zuciyar jemage, akwai kuma kaji da muka saya jan zakara, wake-wake ba'kar kaza da kuma turarukan da muka saya wurin yin aikin."
Shiru ya ratsa wajan bayan gama maganarsa.

Ya ce." To, na ji wane aiki aka yi akan hakan."
Ya yi shiru tare da yin kasa da kansa sai da ya kara maimaita tambayarsa tukkuna ya ce." Alhaji a zahirin gaskiya ni ina daya daga cikin manyan Malam Hajiya Maryam kuma duk lokacin da ta buk'aci wani aiki muna ko'karin ganin mun gudanar dashi duk rintsi domin samun biyan buk'ata.

Wannan sirri ne tsakani na da ita amma yanzu ta ta 'kare sai dai mu ro'ka mata gafara wurin Ubangiji.

Dole ta sanya ni neman ha'kkina domin dai aiki gaf nake da kammala shi rasuwarta ta katse na taho.

Kuma kudin hannuna sun yanke Hajiya Maryam aiki ta sanya ni na yi akan wata baiwar Allah mai suna Hauwa.

Yadda take gaya mini cewa tunda take a duniya ba a ta'ba yi mata tozarcin da matar ta yi mata ba shine dalilin da ya sanya take so a d'ora mata jinyya mai tsanani ko kuma a shafe ji da ganinta ta yi mutuwar tsaye babu ji babu gani cikin biyu tace ayi daya.

Duk abinda na lissafo maka da farko na saya na kuma fara aikin sai dai ban kammala ba, Allah ya yi mata rasuwa.

K'warai da gaske ya tsorata tun lokacin da mutumin ya fara magana.

Mazantaka kawai ya nuna tare da gogewa ta fannin mu'amula bai nuna masa razani ba.

Ya ce." Yanzu ya ake ciki idan ka koma za ka kammala aikin ko kuwa?"
Sai ya gyad'a kansa yana fad'in." Zan dakata gaskiya tunda Allah ya yi ikonsa akan wadda ta sanya ni sai dai da iska (jinnu) muke yi su kuma ba alkawari ne da su ba, idan na gaya musu mu tsaya da yin aikin bai zama lallai su tsaya kai tsaye sai sun gindaya abinda suke buk'ata amma ba zai wuce yanka ba."
Ya girgiza kansa cikin d'an karan mamaki da al'ajabi cikin zuciyarsa tana nanata istigifari.

Ya dube shi kafin ya ce." Ka kyauta da ka d'auki aniyyar dakatawa zan kuma biya ka hakkinka.

Amma ba yau ba ina so ka dawo bayan sadakar bakwai kud'i hannu da hannu."
Ya risinar da kansa yana ta godiya.

Shi kuma ya yi ta nazarinsa cike da madaukakin mamaki gashi cikakken mutum cikin manyan kaya da kamala har da rawani ashe mushiriki ne ta'babbe ne, wato iskokan da suke yi musu aiki sune masu biyan buk'ata ba Allah ba.

Ya sanya hannu cikin aljihu dubu ashirin ya bashi kafin ya ce ." Ka yi kudin motar komawa gida amma kamar yadda na gaya maka bayan an yi addu'ar bakwai ka zo ka kar'bi kudinka."
Ya kar'ba da sauri yasa a aljihu yana ta godiya ya mika masa hannu wai su yi sallama bai kar'ba ba kawai sai ya daga masa hannu yana fad'in "A sauka lafiya." Daga haka ya koma cikin gidan cike da tunani da nazari..

Ya samu Bashir tare da su Salim da Yusi a zaune.

Kallo guda ya yi wa yaron ya hangi kama sosai da Maryam domin duk irin fuskarsu daya sai dai shi fuskarsa ta yi duhu sosai da lebensa tabbacin wiwi ta ratsa shi.

Ya dinga sunkuyar da kansa kasa kamar munafiki ya fara gaishe shi cikin ladabi irin wanda suka saba.

Ya amsa yana dubansa tare da fad'in." Ko kaine Bashir din ne?''
Da sauri ya ce." Ni ne, eh ni ne?''
Ya fad'a yana wata dariya da sosa kansa.

Shigowar Alhaji Sulaiman gidan da iyalinsa ya d'auke masa hankali, da kansa ya tafi domin tar'barsa tun kafin ya karaso rumfar da suke zaune.

Tare muka yini da Hajiya azizi da abokiyar zamanta mai suna Hajiya Salamatu da Halisa 'kanwarta da ta ba ni labarinta kwanakin baya.

Muka yini dasu a gidan sai wajan uku na rana bayan sun ci abinci sun yi salla muka yi sallama da su kan cewa za su shiga can gidan Maryam din domin yi wa danginta ta'aziyya na yi ta mamaki ashe ba su shiga ba sai yanzu da suka tashi tafiya.

Alhaji Sulaiman ya shigo har gida ya yi mana gaisuwa ni da Hajja ya d'an jima a tare da Hajja suna hira kafin ya yi mana sallama ya fita.
Chapter 177 · 0% Book details