← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 276

Sashe 9

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ranar aka d'aura auran bayan an idar da sallar Juma'a.

Shi kuma uban gayyar wanda tunda ake turka-turkar bai tofa tasa ba kawai dai yana ta bin mu da ido, duk abinda mahaifiyarsa ta ce masa ya yi zai ce mata to.

Ganin hakan yasa ni ma na sasauta kyamatar lamarin a gabansu.

Idan na cigaba da yin tutsu hakan zai nuna cewa na fi karfin mahaifina kamar yadda mutane suke zargi.

Manyan mutane ne suka halarci d'aurin auran a massalaci bayan an idar da sallar juma'a wanda sarki mai zamani a lokacin shi ya daura auran a massalacin Annabi Muhammadu S.A.W.

Na samu gudumuwa sosai daga wurin abokanansa larabawa da suke hurd'a kudi da gold masu yawa.

Kafin kice kwabo labari ya watsu a duniya gidajan yada labarai jaridu da social media sun samu abin yi.

Sahihin gidan jaridar da jama'a suka aminta dashi sune suka fara sanarwa a shafinsu na fecebook.

Alhaji Tajudden Ibrahimu shararran dan'kasuwar nan ya auri 'yar gwagwarmaya kuma 'Yar kasuwar nan Amina Salisu mai-hula.

Mahafiyar yaron nan Kamalu wadda a kwanakin baya ta yi dogon rubutu na zagi da 'batanci a kansa ashafinta na fecebook.

An d'aura auran ne yau juma'a a madina massalaci Annabi Muhammadu S.a.w inda shahararrun mutane suka samu damar halarta.

Amarya ta samu gudumuwa sosai daga hannun abokanan ango.

Allah Ya basu zaman lafiya.

Wannan dogon bayanin sun yi shine tare da hotona da nashi a had'e......
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram akwai normal What'sapp group #700 ga wad'anda karatu a talgrm yake yi musu wahala hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.

Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.

To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.

Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu.

Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya.

Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne.

To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji.

Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba.

Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu.

In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi.

Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama.

Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.

Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki.

Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki.

Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu.

Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay
*6*
Lamarin da ya janyo hayaniya da kace-na-ce, mussaman a social media kowa na fad'in albarkacin bakinsa.

Wasu na ganin Alhaji Tajo alfarma ya yi mini ya aure ni.

Wad'anda kuma suka san tarihinsa na baya suna ganin kawai kwanana ne ya k'are tunda har kud'insa suka rude ni na aure shi bayan nasan matsalarsa.

Ni dai tunda aka d'aura auran nake ta zubar da hawaye gabad'aya na rasa a da wane ma'auni zan auna lamarin.

Wace irin k'addara ce wannan mai sammatsi.

Ina zaune a wani d'aki da yake cikin gidansa domin tun jiya da muka zo ni da Baba Hajjan tace mu zauna kawai kayanmu ma dake can masaukinmu sai turawa akayi aka d'aukosu.

Ina jin messages (sakkoni) na ta shigowa wayata ban duba ba dalili na riga na san ba ni da nutsuwar da zan bada amsa abinda dai na yanke a zuciyata shine duk wanda ya tambayi ya akayi hakan ta faru zan ce masa ban sani ba.

Shigowar Hajiya Saratu d'akin da kaya a hannunta ya sanya da sauri na goge hawayen kumatuna.

Sai ta girgiza kanta ta karaso wurin da nake tana fad'in." Ki yi hakuri don Allah ki daina wannan kukan Amina.

Wallahi tallahi kin ji rantsuwar Muslimi ba zamu cutar dake ba.

Duk abinda hajiyarmu ta kaunace shi ya zame mana dole mu 'kaunace shi.

Kuma albishirin da zan yi miki shine kin yi miji, ba don Tajo d'an'uwana ne ba nake gaya miki haka, mutum ne da rabin mutum.

Zai baki kulawa sosai, kuma zaki samu jin dadin rayuwa dake da yaranki.

Ki kwantar da hankalinki, kuma jita-jita na mutane ya daina damunki ki barwa Allah lamarinsa tunda ke kanki idan ki ka yi wa lamarin nan duba na tsanaki za ki san shirin Allah ne."
Murmushi kawai na iya bakina ya yi nauyin da ba zan iya ce mata ba na son d'an'uwanta ba.

Gashi kuma ina jin nauyinta domin tana da irin sunan Mamana.

Kawai sai na sunkuyar da kaina kasa.

Ta ajiye mini kayan da ta shigo dashi tana fad'in." Ki shirya yanzu nan ya kira ni a waya na gaya miki za su shigo tare da abokanansa za a yi hoton tarihi."
Tana gama maganarta ta juya ta fita daga d'akin a gaggauce.

Ledojin na bude dogayen riguna ne manya irin na larabawa da hijabai masu kyawun gaske.

Da band'aki a cikin d'akin na shiga na yi wanka na fito na zura d'aya daga cikin dogayen rigunan a jikina.

Na d'auki karamin hijabi iya kafad'a nasa.

Turare na d'auka akan madubi na fesa a jikina na nemi wuri na zauna zuciya gabad'aya a cunkushe.

Sa'kkonin da aka turo mini ta inbox na fara dubawa.

Wanda na yi wa duban tsanaki na Anti Yagana da Sahura.

Tambayata suke yi shin labarin da suka ji yana yawo a gari da gaske ne.

Kuma ya akayi hakan ta faru.

Na basu amsa da gaske ne.

Amma ni ma ban san yadda aka yi ba, kawai su taya ni da addu'a.

Idan kuma kwanana ya kare suka kula mini da yarana."
Nasa hannu na goge hawayen da ya shiga zarya a kumatuna wanda ya yi daidai da lokacin da aka turo kofar d'akin a bazata na daga kaina muka yi Ido hudu.

Ya mayar da kofar ya rufe ruf.

Ya nufo wurin da nake cikin shigar larabawa harda alkyabba irin tasu.

Gabana ya dinga bugawa da k'arfi da k'arfi.

Zuciyata tana harbawa kamar zata faso kirjina ta fito.

Daf da ni ya tsaya masifaffen kamshin turaransa ya fara surnanowa hancina.

"Amaryar Tajo." Maganar ta daki kunnena.

Hanci na ja ban dago kaina ba balle na kalle shi.

Wannan littafin dai na kudi ne Hajiya kada ki karanta mini muddin ba ki biyani hakkina ba, mu kula sosai hakki komai kankantarsa sunan hakki.

"Na gode sosai, da wannan sadaukarwar taki, kin daraja mahaifiyata.

Kin kar'bi ro'konta, wannan dalilin ya sanya na baki gurbi mai girma a zuciyata.

Ba ni da ra'ayin aure a yanzu saboda tarin matsalolina.

Amma ba ni da k'wanjin yin turjiya ga umarnin mahaifiyata.

Kada ki damu yaranki ki zo tare dasu, ai d'a duka na kowa ne, Allah Ya raya su, ke kuma Allah Ya ba ki hakuri da juriyar zama da ni."
"Ba zan iya zama da mazina ci ba.

Ba zaka same ni ba har abada.

Aure an d'aura dai amma zai zama na kwangila.

Zan zauna a gidanka zan cigaba da hurd'odina na yi hakan ne saboda mahaifiyarka, amma ni ba ni da burun auran irinka, abinda yake cikin zuciyata na fito na gaya maka.

Kana da damar auro wata, amma ni kam ba zan iya had'a jiki dakai ba."
Ido cikin Ido na gaya masa haka domin tun yanzu gwara ya san manufata.

Haka kawai nake masa kallon mai cutuka a jiki.

Domin duk mutumin da yake zina ba zaka raba shi da matsaltsalu ba.

Ya jima yana kallona kafin ya nisa.

Ya daga kafadarsa yana fad'in." Ai aure ba abin wasa ba ne, ni ba munafiki ba ne, kuma ba zan fara a kan wannan karamin dalilin ba.

Ni ya kamata na kyamace ki saboda mazan da ki ka yi tarayya dasu a baya.

Amma har kina da bakin fad'a mini magana.

Ki zauna a shirye duk lokacin da na tashi kar'bar sadakina zan turo miki likita ta auna ki.

Domin ni har yanzu saurayi ne babu wata mace da na sani."
Wani irin kallo na yi masa a watse na ce." Sai dai a auna mu a tare don wallahi ba zan yarda ka shafa mini 'kanjamau ba."
Sai ya fashe da dariya irin wadda ban ta'ba ganin ya yi ba.

Ya nuna kirjinsa da hannu yana cewa." Ni ne mai kanjamau!"
Murgud'a bakina na yi na kawar da kaina gefe.
Chapter 9 · 0% Book details