← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 196 OF 276

Sashe 196

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na ce." Ka sanya a rushe gidansa tsaf tunda na ga na kasa ne ginin da a zamanantar dashi a gyara masa tsangarsa sannan ka samawa wasu daga cikin yaransa maza aikin yi ko da a karkashinka ne duk da zaman da muka yi a gidan na fahimci ba su da yunwa dalili duka yaransu suna fita gona amma yana da kyau a ce sun fito cikin gari sun waye sun dan yi karatun zamani da hurd'a da jama'a da kasuwanci."
Ya dinga gyada kansa yana saurarena har na gama maganata ya ce." Haka za a yi my love shawarar nan taki ta yi mini sosai za a yi duk yadda ki ka ce in sha.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[5/3, 2:50 PM] +234 803 054 1544: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.

Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.

To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.

Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu.

Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya.

Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne.

To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji.

Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba.

Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu.

In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi.

Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama.

Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.

Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki.

Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki.

Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu.

Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
Masu buk'atar a tallata musu hajarsu kofa a bud'e take za a yi akan farashi mai sau'ki in sha Allahu rabbi
*Gudun aure paid book ne 2k complete on Telegram normal What'sapp group kuma 1k ko AREWAPEN via 0542382124....

Binta Umar gtbank*
*07084653262*
*132*
Baban Saude dai lokacin da ya ji abinda matar da yake yabawa ko'kari da bajintarta ta fannin kula da miji har ma yana bada misali da ita tare da jaddada goyon bayansa akan abinda a gaya masa a kanta sai da ya ki'dime sosai.

Mutum ne shi jarumi jajurtacce wanda ko rasuwa aka yi bata gigita shi ainun domin ko lokacin da Mamanmu ta rasu ya nuna jarumta da dakiya a cikin 'yan uwanta ko yanzu a ka tashi zancenta yana tsawatarwa da masu yi mata kuka cewa ba daidai ba ne sai ga shi jin irin mugayen ayyukan da maccen da yake misali da ita tare da ko'karin tabbatar mata da aljanna ta aikata ya yi shiru yana zare ido har abin ya so ya ba ni dariya na danne ban yi ba.

Da farkon da abokin nasa ya fara bashi labarin ya dinga dakatar da shi yana nuna babu yadda za a yi ta aikata haka tunda shi kansa ya sheda soyayyar da take masa a ganinsa babu dalilin da zai sanya so ya sanya ka nakasta wanda kake so.

Ganin yadda yake rantse masa da girman Allah da buwayarsa ya sanya jikinsa saduda ya yi tsuru kawai yana sauraran bayanin da yake yi masa da yadda ya ci tsananin wahala kafin ya samu kansa a yanzu da yake zaune suna magana.

Ya jima yana girgiza kai da tu'ajibi da mamaki kafin ya bud'e bakinsa yana fad'in an yi shed'aniya amma mai suffar munafukai tana sunkuyar da kai kamar mutuniyar arziki ashe macijiya ce mai mugun dafi Allah Ubangiji ya saka muku da mu kanmu da ta jefe cikin zullumi da tashin hankali da damuwa.

Da k'yar da jibin goshi ya yarda ya kwana a gidan Hajja a cewarsa zai je ya kama hotel idan ya duba Baba Sule a asibiti sai ya d'auki hanya da sassafe tunda jibi zai komai bakin sana'arsa.

Da 'kyar ya lalla'be shi ya amince.

Da daddare gabad'aya har da ni muka je asibitin domin duba jikin Baban Sule kamar dai yadda ya fad'a.

Alhamdulillahi jikinsa da sauki wai ashe basir ne yake damunsa irin mai daure cikin nan.

Ya yi tsiro kuma yana fitar da jini sai da aka yi aiki duk ya rame kuwa ya zabge kamar ba Baba Sule ba Sunusi babban d'an sa shine yake jinyarsa.

Na tausaya masa sosai kuma ban san haka ciwo ya ci karfinsa ba duk da ba ni cikin hayyacina amma ina da hakki a sanar mini domin na bada taimakona asibitin gwamnati ne amma dole ai za a sayi magani shi kuma bashi da k'arfi asalin ubangidansa Alhaji Muntari ne kuma ya rasu don ma yaransa maza sun tashi sune suke ta dawainiya da shi da taimakon Babanmu tunda alhamdulillahi yanzu shine yake da rufin asirin da ba su dashi tun farkon samun d'aukakata dana bude masa shagon huluna yake cigaba da gudanar da kasuwancinsa.

Bacci yake yi har muka gama zamanmu a d'akin da yake bai farka ba da za mu tafi Baban Saude ya bawa Sunisu dubu goma ya ce a sayi magani shi kuma Yallabai din ya ce zuwa gobe zai ga sa'ko.

Jin haka ya sanya ni kar'bar lambar wayar Sunusin da ta asusun ajiyarsa nasan lallai tunda ya fadi haka zai buk'aci da na bashi details din da zai saka kudin.

Duk da dare ne ashe da yawa wasu sun ankara da shigowarsa asibitin muna fitowa kuwa jama'a suka rufe shi ni da Baban Saude muka ja gefe muna kallon ikon Allah uwar zuma kenan ki tashi a biki idan har za ka bayar to babu shakka za ka ga tarin masoya da yawa.

Sukairaju da yake bayansa ganin abin ya yi yawa ya sanya ya fara ko'karin korar mutane muka nufi mota suka biyo mu har da mata masu zaman jinyya.

Mota muka shiga gabad'aya har da shi ya bude ma'ajiyar kudinsa ya fito da kudi da d'an yawa ya mik'awa Sukairaju wani dattijo ya bawa daga ciki ya ce su kasftaa.

Ya zo ya shiga motar da saurin gaske domin ganin jama'a na sake k'aruwa a wajan.

Baban Saude tun a mota yake tsokanarsa wai zai yi kyau da siyasa ya nemi kujera gwaman Kano.

Ya dinga dariya yana fad'in abinda bai taba sha'awa ba kenan siyasa ya yarda dai ya yi gwagwarmayar ta neman kudi a ko'ina ya tara ta hanyar halak amma mafiakasari 'yan siyasar nan da suka ci suka tada kai suna bushasha da dukiyar jama'a suna mutuwa da nauyin al'umma a kan su.

B'angaran ba'ki na cikin gidan Hajja ya sanya Sukairaju ya gyarawa Baban Saude ya kwana anan da sassafe kuwa ya kira shi a waya yana fad'in shifa ya shirya.

Ba shiri muka fito harabar gidan ni da shi sai a lokacin ma muka gaisa aka yi aka yi dashi ya jira aka kawo masa abin kari ya ce a a.

Sai da ya yi masa dubara kan cewa yana da kyau ya yi wa Hajja sallama kafin ya tafi sannan ya yarda muka shiga ciki a tare anan Hajja ta sanya aka kawo masa abinci funkaso da miya da kuma kayan shayi ya sha ruwan shayin babu madara sannan na zuba masa funkason manya guda biyar zan zuba miya ya ce na cire biyu na bar masa uku ya isa.

Na yi yadda ya ce din ya sake sosai da Hajja ana hira da shi har aka ta shi labarin abinda ya faru ya kara jadadda mata mamakin da ya yi da aka ce masa Hajiya Maryam mashirika ce duk nagartar da ta nuna masa a farkon ganinta da shi bai taba tsammanin haka daga gare ta ba.

To bayan tafiyar Baban Saude da kad'an ni ina tare da su Hajja a falo muna hira har da ita inna Uwanin shi kuma ya bi bayan Baban Saude amma bai dawo ba.

Littafin kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba
Na ji maganar Hajja cikin nutsuwa tana kiran sunana.

Na amsa tare da mayar da hankalina gare ta ta ce.

"Amina."
Na ce." Naam Hajja."
Ta ce." Hauwa ta koma dakinta tun Tajo yana bunkure a kwance."
Na d'an saki fuskata ban nuna mata cewa na sani ba na ce." Ma sha Allah Hajja ai haka ya fi Allah ya kiyaye gaba."
Ta amsa da Amin Ya Allah.

Ta cigaba da cewa ita da mahaifiyarta suka buk'aci hakan ga ta a zaune hakane Uwani?"
Ta amsa "Hakane Hajja."
Sa ta cigaba da cewa." Hauwa a cewarta tana jin kunyarku ke da Tajo bisa abinda ta yi na rashin kyautawa a baya ta yi nadama ta kuma gane ba daidai ba ne.

Ta ji labarin ibtila'in da ya samu mijinku shine ta ce tunda ke kina tare dashi kina jinyarsa ita sai ta koma ta kula da yaran.
Chapter 196 · 0% Book details