← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 276

Sashe 24

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ke kuma kaddararki a haka take domin idan kin tada balli mijinki ya sake ki don kina hangen kema ki samu miji irin na Amina Ina ganin da kamar wuya ba fata nake yi miki ba ba, don ni kaina na so a ce daya daga cikinku ne wata take auran Alhaji Tajo, to ba haka Allah ya tsara ba, kuma kin ga yanzu Amina ta yi wa kowa nisa a gidan nan kamota zai yi wahala gaskiya don tana da zuciya mai kyau." Ummansu Hadiza ce take wannan maganar cikin alhini da damuwa.

Duk da cewa a yanzu ba su rasa komai ba sakamakon taimakon da Amina take yi wa Babansu ta hannun Hamusu Amma har yanzu idan hassadar ta motsa ita da yaranta sai sun kuka game da yadda Allah ya suturta Aminar da taguwar arziki.

Hadiza wadda ta yi firgai-furgai sakamakon irin bakar wahalar da take sha a gidan mijinta dalilin rashin haihuwa da kuma karayar arziki da mijin ya samu tuntuni sai kame kame yake yi idan ya bada na safe to fa ba zai bada na rana ba, idan kuma ya bada na rana to ba zai basu na dare ba, kowace mace a gidan tana cikin albarkacin yaranta da suke fita su nema.

Ita Hadiza bata haifa ba shiyasa take ganin tasku a gidan, wataran haka take kwana da yunwa ko kuma ta zo gidan nasu ta ci sa'annan ta tafi da dumame.

Dalilin da ya sanya kenan take yun'kurin kashe auran nata domin a ganinta idan ta fito tunda ba d'a ba jika itama zata fantama ta nemi kudi irin na amina har dai Allah yasa wani gwaska mai 'ya'yan banki kwatankwacin mijin Amina ya zo ya aure ta
Hancinta ta shak'a ta sanya hannu ta goge gumin fuskarta kana ta ce." Umma na gaji ba zan iya ba wallahi tallahi hakurina ya kare sai na kashe auran nan na fito, ban fa haihu ba, amma sai na zauna wahala ta kashe ni, don Allah ki bi ni da addu'a kawai, da sauran kuruciyata har yanzu dalilin da ya sanya ma kenan nake so na kashe auran na fito, munufar zuwa wurin Malam Lurwanu kuwa domin ya yi mini taimako akan Amina kafin na tunkareta don Ina so idan aurena ya mutu na je can Legos din wurinta na murmure sannan na samo jari mai tsoka ni ma na zo na fara business to kin san Umma kafin hakan ta faru dole sai an d'aure mata baki duk abinda na nema a wurinta ta yi mini, shiyasa fa na zo ina neman shawararki."
Gudun aure na kudi ne kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Umman tasu ta sauke numfashi tana ce wa." To ai ban ki ba Hadiza, ni na riga na dawo daga rakiyar Malam Lurwanu domin a da can wane irin kudi ne ba mu kashe ba amma babu biyan buk'ata, ko kin manta lokacin da muka je masa da bukata akan Uwargidanki matar Alhaji Halilu.

A lokacin ne fa na d'aga gidana na gado da rage mini na sayar domin a samu biyan buk'ata.

Amma da yake macuci ne babu abinda ya canza haka ya karbe mini kudi dubu dari uku da tamanin, sauran kudin suka watse a banza ba tare dana fargaba har yanzu kuma Hajiya Indo tana nan zaune daram da 'yayanta babu abinda ya same su." Shiru ta yi tana gyada kanta tabbacin har yanzu da haushin hakan a cikin ranta sai ta nisa kafin ta cigaba da ce wa."
Sai dai ki binciko wani malamin amma na yi Imani da cewa Malam Lurwanu kudinki zai ci a banza a wofi, bayan haka ma wai da wane kudin za ki tafi yawon malamai ne Hadiza, kayan dakinki duk kin sayar da su ko kina da wata kadara ne ban sani ba?"
"Katifa ta zan sayar sai kwanukana zan kai su rimi idan na hada kudin akwai wata mata amma gaskiya ita bori take yi da aljanu take aiki, tana watsa wuri ne kuma wallahi an ce ta iya zan nemi Bilki 'kawata sai ta raka ni mu je, ni ba zan yi abinda zai sabautata ba, kawai dai a sanya mata tsorona da kuma bin umarnina shikkenan abinda nake buk'ata dan gaskiya ina buk'atar jari na fi so duk buk'atar da naje mata da ita ta amsa mini babu jayayya."
Jiki a mace Umman tasu ta furta." Ki dai bi a hankali Hadiza ba zan hana ki ba, amma kada garin neman gira a rasa Ido, itama Aminar na tabbatar da cewa ba zaune take ba, kin san tun tana gida bata wasa da addu'a yawan yin sadaka da saukar al'kur'ani maigirma, kin ga kuwa tunkarar irinsu sai mutum ya shirya"
"In sha Allahu Umma zan yi nasara ke dai ki bi ni da addu'a kawai, ni ma zan gwada sa'ata wata'kila ma wanda zan aura sai ya fi nata wallahi."
Umman tasu ta girgiza kai da wani ma'kalallan murmushi a fuskarta da take nuna maganar 'yar tata lallai da kamar wuya wai gurguguwa da auran nesa.
****
"Inna Uwani ta dubi 'yar uwartata da take yin waya cikin nishadi da murmushi a tattare da ita tana ce wa." To Amina ina nan tafe in sha Allah rabbi, Ina dai fatan duk kuna lafiya ina Yusuf ai ina shan labarinsa a wurin Babansa, magana daya biyu idan muna waya zai ce Yusuf ya ce a gaishe ni."
Inna Uwani ta kawar da kanta zuciyarta fal takaici da zullumin yadda za ta yi ta raba wannan sha'kuwar da take tsakanin 'yar uwarta da kuma surukartata.

Babbar damuwarta yadda yayar tata take nuna mata zahiri bata son d'anta ya auri 'yarta Hauwa.

Ta san ta yi kuskure a can baya lokacin da suka nemi ita Hauwan ta maye gurbin 'yar'uwarta Samira bayan rasuwarta.

Mutane suka yi caaaa!

Kowa na fad'in albarkacin bakinsa mussaman daga can b'angaran mijinta cewa kada ta bashi itama zata mutu.

A lokacin ne itama ta rufe idonta ga-da-ga ta fito ta gayawa 'yar'uwarta cewa ba zata iya bashi Hauwa saboda an riga an ce mata aljana ce dashi itace masa silar arzikinsa Kuma ba zata ta'ba bari ya zauna da mace ba sai ta mutu.

To kuma yanzu gashi zaune da matarsa kusan wata biyar ba'a ta'ba bugo waya an ce musu bata da lafiya ba.

Wannan dalilin ma yasa ta kara ji a ranta dole duk yadda za ta yi sai Hauwa ta maye gurbin 'yar'uwarta don har yanzu bata da tsayayye duk masu zuwa wurinta talakawa ne babu wanda ya kamo kafar Tajo kudi da d'aukaka.

Hajja ta dubeta tana ce wa." Uwani tunanin me ki ke yi ne?

Ina ta magana shiru kin tsirawa wani wuri Ido." Ta dawo hayyacinta cikin diriricewa ta ce." Hankalina ne ya yi gida wallahi na kuma gaji da nan din tafiya zan yi a satin nan."
Hajja ta ce." To ba lefi Hakan na so a ce zaki zauna har lokacin dana shirya zuwa gidan Tajo din sai mu je tare, yanzu nan da muna waya take tambayarki na gaya mata gaki nan kusa da ni, ta ce a gaishe ki."
Cikin ya'ke ta ce." To Ina amsawa, ai ba ni ce matsalar ba Hauwa ce itace ta damu na dawo gida wai ta gaji da zama ita daya."
Hajja taja tsaki tana cewa." Ke kuma saboda kina jin tsoronta shine zaki kulle kaya ki tafi ko?

Yarinya ce ita da zata ce tana jin tsoro, ina ce gidan naku na jama'a ne, koyaushe cikin hayaniya ake idan ta damu da ganin sai ta dauro kayanta ta biyo ki, kina nan kina jiranta."
Tana 'yar dariya take cewa." Ai ba a basu hutu ba a wurin aiki ba, kin san malamar asibiti ce, kuma suna da doka mai k'arfi shiyasa."
Hajja ta ce." Ai ban san ta fara aiki ba, amma dai duk da haka kya bari mu je mu dawo tukkuna idan ma zaki tafi sai ki tafi."
Ta ce." To shikkenan zan bari, amma ya maganarmu ta kwanaki akan auran Tajo da ita, har yanzu ina so zumunci nan ya kullu wallahi, Hauwa dai kamar Samira take kamarsu daya, duk abinda Tajo yake so a wurin Samira Hauwa tana dashi Hajja."
"To ai ba a nan take ba Uwani.

Idan ya kasance Hauwa da Samira suna kama hali fa?

Ai kowa da nasa.

Na san halin kowacce daga cikinsu, Samira tafi Hauwa d'a'a, da girmama mutane bata da hayaniya, Hauwa kam ai tun tana yarinya ki ka lalata Uwani, ba zan iya cewa komai ba, anan amma ba zan hana ki yin magana da d'anki ba, tunda naga kun fara yin maganar ranar da zai tafi da iyalinsa.

Idan kun hadu sai ki tambaye shi, idan ya amince shikkenan, sai mu yi musu fatan alheri da zama lafiya ."
To hakan da Hajja ta fad'a sai ya sanyaya mata rai, wanda a da take ganin kamar ba ta son ayi auran.

Idan kuwa hakane Tajo ba shi da matsala tunda tun can ma ba kasafai yake yi mata jayayya ba.

Amma dole sai ta yi kwantan b'auna ta daina nuna k'yamar auransu da matarsa a fili muddin tana so hakanta ya cimma ruwa.

Da wannan suka rufe maganar suka shiga wata wadda ta shafi zumuncinsu
Yau asabar tun bayan da ya dawo daga sallar asubahi ya kashe wayoyinsa ya kwanta bacci.

Har na gama duk abinda nake yi bai tashi ba, abokin nasa ma Yusi da ya gaji da jiran saukowarsa fita ya yi harabar gidan wurin masu aiki domin d'ebe kewa.

Kowa ya san Yusi a gidan dalilin saurin sabonsa da kuma da yadda maigidan ya daukake shi.

Kananun kaya na sanya a jikina na shafe ko'ina da humra ta ta mussaman....08089965176 sannan na dora abaya a kan kayan, na sake komawa dubawa ko ya tashi.

Yana nan a kwance a gado yana bacci, daya saura minti arba'in.
Chapter 24 · 0% Book details