Sashe 27
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni ma ban boye masa ba na nuna masa na yi kewarsa kwarai sa'annan kuma na gaya masa abinda nake hasashe na samuwar cikin da yake ta mafarki.
Ai sai ya kara kid'imewa Yana ta addu'ar Allah Yasa shi din ne.
Koda muka yi wanka muka sauka kasa kawai sai na ji yana gayawa Hajja cikine da ni.
A okaci guda na diririce kunya mai karfin gaske ta kama ni.
Cikin jin nauyi da kunyarsu na yi kasa da kaina.
Shi kam bai ji nauyi ba ya riko hannuna muka zauna a kujera yana fad'in." Ciki ne da ita wallahi, yanzu nan ta gaya mini, Hajja wannan ranar tarihi ce wajena ku taya mu addu'a Allah Ya sauketa lafiya.
Hajja baki a har kunne take cewa." Addu'a ta zama dole Tajo, ai ni ma ranar ta zama tarihi a wajena ba zan manta da ita ba."
Budar bakin Inna Uwani ta ce." Ina ce ita ba ta fari ba ce a wajanta ko."
Hajja ta ce." Kwarai kuwa ta uku ce, ai mu kamar ta fari ce a wajenmu Uwani."
Sai ta yi ya'ke wanda hausawa suke kira da ya fi kuka ciwo tana fad'in." To Allah Ya raba lafiya." Gabad'aya suka amsa da Amin.
Ban da ni, da na tafi tunanin abubuwan da suke faruwa.
Samuwar juna biyu a tare da ni sai ya kara janyo mini k'auna da soyayya a wurin uwar mijina.
Dashi kansa maigidan wanda a wasu lukutan har tausayi yake ba ni, idan na ga yadda yake kaffa-kaffa da ni, sam baya son b'acin raina.
Idan yana gida baya bari na yin komai kullum muna tare da juna a cewarsa yana jin d'umin abinda zai haifa.
Wasu lukutan har b'uya nake yi na share hawaye domin tunda cikin ya yi k'wari zuciyata take ta yi mini sa'ke-sake marasa kyawu.
Koda abin ya dame ni na kira Anti Yagana a waya na gaya mata ina yawan mafarkai da munanan tunanai take cewa da ni mafi akasari masu ciki sukan samu irin hakan.
Amma dai na dage da addu'a.
Ni kam cikin Yusi da Kamalu ban yi irin wannan wasi-wasin a raina ba.
Hajja ta samu wurin zama domin kuwa cewa ta yi ba zata tafi ba har sai na haihu tukkuna lokacin watansu hud'u da zuwa.
Inna Uwani ta yi ta yi da ita su tafi tace mata a'a, sai na haihu.
Sai kawai ita ta yanke shawarar tafiya domin dama kamar akan kaya take dalili ta tsani ta bude ido ta fa gilmawar matar gidan da ciki, da kuma yadda masu gidan suke ki'dime akan hakan. tana ganin komawarta gida shine maslaha a wajenta domin ta je su tattauna yadda za a yi, don ta fahimci kamar sai ta biyo ta bayan gida tukkuna ha'kanta zai cimma ruwa.
Tafiyar inna Uwani da kwana biyar.
Anti Yagana da Hadiza suka zo.
Anti Yagana sai da ta fara sauka a can gidanmu dalili ta kwana biyu ba ta je.
Nan fa Hadiza ta ma'kale mata wai lallai sai sun taho tare.
Sai a lokacin ma ta san auranta ya mutu tana cikin iddah ne.
Da ta tambayata dalili duk ta kwashe komai ta gaya mata.
A lokacin ta yi mata fad'a sosai irin na 'yan uwantaka.
Ummansu tana zaune tana ji amma ba tace komai ba, ita bakin cikinta yadda a komai yaranta ne a baya.
Kallo d'aya ta yi wa Yagana ta gane cewa lallai tana cikin hutu da jin dadi, dama kuma ko lokacin da ta auri mijinta mai rufin asiri ne.
Da sahalewar Babanmu suka kamo hanya suka taho.
Maigidan kuwa ya dinga fad'a yana cewa mai yasa suka biyo motar haya daga Kano zuwa Legos ba su kira su sanar da ni ko kudin ticket sai a basu su biyo jirgi su zo.
Duk wani abu da ya dangance ni yana mutukar daraja shi da martaba shi.
Tun da ya fahimci cewa anti Yagana itace babba a gidanmu yake girmamata gashi dai ya kusa haifarta amma idan zai gaisheta sai ya dan risina.
Dalilin da ya sanya ma kenan ta guji zaman falo take zamanta a d'aki, takan ce mini Amina mijin nan naki kunyarsa nake ji wallahi tallahi wani idan ya ga abinda yake yi sai ya d'auka kin wanke kin bashi ya shanye.
Ba na so jama'a su gazgata zarginsu akan cewa matan barno suna asiri.
Kin ga dai mutumin nan babu wani abu da muka taba yi masa na mallaka, ban sani ba ko kin yi a boye Amina abin yayi yawa.
Na dinga dariya ina fad'in wallahi ko d'aya anti Yagana shi haka yake fa bashi da wani girman kai da ma'aikatansa sai ya zauna ya ci abinci dasu.
Ni kaina dan ya durk'usa mini ba wani abu ba ne.
Ta ce." Idan ya durk'usa miki wannan tsakaninku mijinki ne, amma ni kam ina kin kunyar abinda yake yi mini.
Mutumin da manya suke zube masa amma idan zai gaishe ni sai ya rankwafa."
Na ce." Anti Yagana duk wanda ya dangance ni to wallahi yana da daraja a wurinsa.
Karin abin ma kuma wannan cikin na jikina ya sake janyo mini girma a wurinsu da mahaifiyarsa.
Wallahi ban yi masa komai na gusar da hankali ba."
Ta girgiza kanta tana fad'in.
" Lallai Amina Allah ya share miki hawaye sai kiji tsoron Allah , ki kyautata masa kamar yadda yake kula dake, ki tsare masa mutuncinsa da dukiyarsa.
Na tabbatar da cewa son da yake yi miki na Allah da Annabi ne, ki yi iyakacin bakin kokarinki wajan yi masa biyayya."
Na ce." In sha Allahu Anti Yagana na gode."
To duk wannan zantukan da muke yi Hadiza tana zaune ba ta ce komai ba illa zare Ido ta kalli bakin wannan ta kalli bakin wannan haka ta dinga tana ta sakin ajiyar zuciya.
Hadiza kenan duk wani motsi da zata yi na san manufarsa domin kuwa tare muka tashi a gida daya daki daya, babu yadda zata yi ne shiyasa ta sakar mini domin kuwa Allah ne yake ikonsa.
Anti Yagana da Hajja jininsu ya hadu sosai idan suna hira tamkar uwa da 'yarta.
Halinsu ya zo daya sannan kuma tunani da nazarinsu ya zo daya.
Ina jin dadi sosai a duk lokacin da na gansu a tare suna hirarraki irin na rayuwa.
Ita kuwa Hadiza dama ta samu bata aikin komai sai ci da kuma bacci abinda take so ya samu basu cika wata biyu ba ta murje ta yi bul daidai da fatar jikinta sai da ta canza.
To ko yaushe tana cikin Ac ga abinci mai kyau.
Lokacin da anti Yagana ta shirya tafiyarsu sai Hadiza ta yi tsalle ta dire ta ce ba zata ta tafi ba sai na haihu tukkun.
Hajja kuwa ta goya mata baya.
Maigidan ma haka ya ce ta zauna tunda bata da aure.
Ni dai ban ce komai ba domin na riga na san ba don ta kula da ni ta nace sai ta zauna ba domin biyan bukatarta ce.
Na yi ta dariya ina kallonta a lokacin da suke ta jayayya da anti Yagana tana cewa ba haka Babanmu ya bata umarni ba, don haka dole sai sun tafi tare.
Maigidan ya sauko daga sama da yake asabar ce baya fita da wuri ya riski jayayya.
Ya ce anti Yagana ta yi hakuri zai kira Baban namu ya yi masa bayani.
Ba don ranta ya so ba ta ha'kura.
Aikuwa muna shiga d'aki ta rufe Hadiza da fad'a tana cewa." Ba zai yiwu daga zumunci mu tare musu a gida ba.
Ina lefin wata biyun da mukayi ai ya isa.
Tun Hadiza na daurewa har sai da ta fashe da kuka tana cewa." Anti Yagana menene don na ce zan zauna na kula da 'yar uwata.
Ba ni fa da nauyin kowa a kaina ba miji ba yara.
Ko don ba ciki daya muka fito tare ba shiyasa zaki dinga nuna mini banbanci.
Ko ina da wani aibu ne."
Cikin rashin jin dadin abinda Anti Yagana ta yi mata na ce." Hadiza ba haka ba ne, ba ki fahimci Anti Yagana ba, amma kada ki yi mata wannan fassarar don Allah, menene babu komai ki yi zamanki mana, na gode sosai da kulawarki a kaina, Allah ya bar zumunci."
Anti Yagana tana jin mu ba tace uffan ba sai aukin tsaki da take ja.
Na riga na gama fahimtar duk inda ta dosa.
Tana jin tsoron zaman Hadiza ne kada ta zo ta aikata wani abin da zai sanya girma da mutunci mu ya zube a idon maigidan.
****
Duk wani shirye-shirye na tafiyar anti Yagana maigidan ya kammala mata domin cewa ya yi a jirgi zata koma gida in sha Allah dan ba kasafai ya fiye son tafiyar motar nan ba.
Gudun aure na kudi ne Hajiya kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Saura kwana biyu ta tafi rikici ya balle a tsakanina dashi domin har ga Allah nayi iyakacin bakin kokarina wurin ganin na danne abin a zuciyata hakan ya gagara.
Tun lokacin da muka sasanta jununmu nake masa soyayya ta tsakani da Allah irin wadda ba na so ko kuda ya kusanceshi.
A zahiri tashi ce ta fito fili, amma ni gani nake yadda nake bala'in sonsa da kishinsa baya yi mini kwatankwacin hakan.
Kuma ina ganin komai na rayuwata zan iya bud'a masa ya san dashi ba zan rufe masa ba, zan iya bayyana masa sirrina ganin yadda ya d'auke ni, da kuma matsayi maigirma da ya ba ni a zuciyarsa.
Duk wanda zai ba'kunce mu na second guda zai fahimci cewa akwai k'auna sha'kuwa da mutuntawa a tsakaninmu.
Dalilin da ya sanya ma kenan na ajiye hakan a raina cewa.
Babu wani abu da ya dangance shi da zai boye mini sai gashi yau ya nuna mini cewa namiji ne fa shi kuma dabi'ar nan fa ta kumbiya kumbiya da Allah ya hallice su da ita ba zata canza ba.