Sashe 52
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na goge hawayen da ya dan zubo mini na ce." E, ya yi aiki dashi kafin rasuwarsa."
Sai ta girgiza kanta cikin alhini ta ce." Allah Ya gafarta masa, ki samu nutsuwa kuma ki daina damuwa da hakan in sha Allah babu abinda zai faru."
Na ce." Na gode Hajja Allah ya kara girma." Ta dafa kafadata tana cewa." Ina ganin umarar nan tare zamuje ki d'an samu nutsuwa ki kuma yi addu'oi, Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu."
Na kalleta hawayen da nake ta dannewa suka fara zuba, na rasa wane irin so da k'auna baiwar Allah nan take yi mini, tana gudun b'acin raina sosai, tana kuma so koyaushe ta gan ni, cikin farinciki da walwala.
Na ce." To shikkenan Hajja sai mu tafi taren in sha Allahu."
Hauwa ce take saukowa daga bene tana sanye da kanun kaya amma ta dora after dressing akai ta yi kwalliya sosai a fuskarta kuma ta yi kyau daidai gwargwado.
Ta iso wajan da muke zaune ni da Hajja ta zauna saman kujera tana fad'in." Hajja Ina kwana an tashi lafiya?"
Ta amsa da "Lafiya lau tana dan dubanta."
Ta d'an kalleni kafin ta ce." Ina kwana." Na amsa babu yabo babu fallasa."
Hajja ta ce." Tajo bai tashi ba ne?"
Babu kunya balle tsoron Allah ta ce." Bai tashi ba jiya bai kwanta da wuri ba."
Hajja ta yi shiru tare da kawar da kanta gefe.
Ni kam maganar ta dan dake ni sai nake ganin kamar da gayya ta fad'eta."
Tashi na yi na nufi wajan cin abinci ina fadin." Hajja kin karya ne?"
Sai ta ce." Kin manta yau litinin ina Azimi."
Na ce." Wallahi na manta, Ina gyara kujerun wajan na dubeta." Hauwa ki zo mu karya."
Ta d'an yatsune baki tana cewa." Ina ga sai an jima ba na karyawa da wuri."
"Okey kawai na ce na gyara kujera na zauna a nutse na dan d'ibi abinda zan iya ci na hada tea na fara sha domin ya d'umama mini cikina.
Saukowarsa ta d'auki hankalinmu gabad'aya duk muka zuba masa ido yanayinsa kawai nake kallo kamar ba shi wanda ya shiga damuwa mai tsanani jiya ba.
Ban d'auka zai wayi gari da karsashi irin haka ba.
Kwalliya ma ya sheka sosai cikin wani irin yadi irin na manya babbar riga da yar ciki da uban aiki a gaban rigar.
Tun kafin ya k'araso wajan da muke kuwa kamshinsa ya karad'e mu.
Ya risina yana gaishe da Hajja ta amsa tana cewa." Ban jima da tambayar Hauwa ba ta ce wa ai baka tashi ba."
Yana dan gyara agogon hannunsa ya furta." Eh yau na dan so na makara ne wallahi, ina da baki a waje zan fita wurinsu yanzu za mu interview."
Ta ce." To babu damuwa." Ya nufi hanyar fita bai dube ni ba.
Abin ya sosa mini rai 'kwarai da gaske amma ban kawo komai ba illa iyaka azijanci irin na d'an adam, domin yadda ya sauko a gurguje wata'kila bakin masu muhimmanci ne.
Ni kadai nake wannan hasashen a cikin raina.
Ko minti biyar bai yi da fita ba Hauwa ta tashi ta haye sama ta bar mu a wajan ni da Hajja.
'Danjaridar ya ce.
"Da farko Allah ya taimake ka muna so mu ji daga bakinka dangane da jita jitar da take yawo a gari mussaman a kafafan sadarwa, inda kowa yake tofa albarkacin da yake bakinsa dangane da mutuwar wani ma'aikacinka da iyalinsa suka fito suna kuka akan cewa ka yi amfani da lafiya da kuruciyarsa a lokacin da yake raye domin neman dukiya karshe ajalinsa ya sauka a karkashin aikinka, ba ka je ka yi wa iyaye da iyalinsa ta'aziya ba, sannan kuma babu ihsani a tsakani, mutane da dama suna zarginka akan son zuciya da ko'karin tara dukiya domin ka gina kanka."
'Dan jaridar ya nisa kafin ya cigaba da cewa." To ana cikin wannan turka-turka a gari da sauran kafafan sadawarsa sai ga wata majiya mai toshe ta yi sanarwa kan cewa Matarka ta yanzu wadda a can baya ta ta'ba auran wani Aminu Salihi wanda ya kowa ya shaida cewa ya wahalta maka k'warai da gaske dalilin lalurarsa yana da ala'ka da abinda ya shafeka, ya kwanta jiyya ba ka duba shi ba, ba kuma ka aika wakili ba, ya fadi ya mutu ba ka je ta'aziya ba sannan ba ka yi ihsani ga iyalinsa ba.
Wannan dalilin ya sanya itama matarka ta yanzu ta fito take nemawa yaranta hakkinsu a wurinka, Allah Ya k'ara lafiya ko za a yi mana karin bayani dangane da zargin da jama'a da masu hakki suke yi maka.
A tsanake ya yi sallama da mika godiya ga Allah da salatin annabi sannan ya fara da ce wa."
Ni dai Alhaji Tajudden Ibrahimu 'Danbatta a iya sanina da hasashena babu wani wanda yake karkashina da hakkinshi yake a wuyana.
Tabbas wannan ka'idata ne kuma tsarina ne ba na d'aukar tsaffi aiki, matasa majiya karfi nake d'auka.
A cikin matasan ma muddin na fahimcin gazawar wani nakan sallameshi na maye gurbinsa da wanda na tabbatar da cewa za mu taimaki juna.
Ma'aikatu nake dasu ba gwamnati ba ce ni.
Babu yarjejiyar fansho da garatuti a form dina.
Duk wani ma'aikici na ya san da wannan ya kuma amince da hakan.
Ra'ayina ne yin alheri ga duk wanda na sallama saboda wani dalili, ra'ayina ne yin alheri da ihsani ga iyalan wanda ya rasu a karkashina, amma abinda nake so mutane su fahimta anan shine ba dole ba ne, ba kuma tilas ba ne in d'auki kudi na bawa wanda ya mutu ko wanda na sallama daga aiki kamar dai yadda na fad'a da farko ni ba gwamnati ba ne.
Kuma maganar da mutane suke yi akan ba na zuwa ta'aziya ko dubiya wannan sharri ne aka yi mini.
A duk lokacin da wani lamari ya faru muddin ina gari na kan yi kokari na je, idan kuwa wani uzuri ya rike ni na kan tura Alhaji Sammani da 'yan tawagarsa wad'anda duk suke a k'arkashin ikona kuma da alheri mai yawa.
A lokacin da Aminu Salihi ya rasu ba na gari, kuma Allah ne shedata na tura a je a yi musu ta'aziyya tare da miliyar biyar domin a bawa magada, wannan shine abinda na yi.
Ina so na gayawa duniya cewa' duk wannan maganganun da suke ta yawo akaina ba ni da hakki ila iyaka wanda na d'auki Amana na d'amka masa shi ya zambace ni.
Babu wanda bai san yadda nake da Alhaji Sammani ba.
Yau na fito na gayawa duniya cewa Sammani ne ya haddasa wannan lamari kuma ban fadi hakan domin na 'bata shi don na wanke kaina ba.
A duniya kana iya zama da mutum da zuciya daya har ka dinga ya'kini a zuciyarka ba zai ci amanarka ba amma daga baya a samu matsala.
Abinda ya faru kenan a tsakanina da Alhaji Sammani sai gashi lokaci kan'kani yana nema ya kai ni 'kasa, to saboda haka masu zargina da zagina ku bari domin ba ku da hujjar yin 'batanci a gare ni, sai ma dorawa kanku zunubi mai girma da kuke yi."
Cikin sanin makamar aiki d'anjaridar ya ce." To Allah Ya taimake ka za mu su mu ji karin bayani daga bakinka dangane da maganar da fita jiya da daddare wanda ake ta jita-jitar cewa da yawun Uwargidanka maganar ta fita, masu bibiyar sha'anin za su so su ji wani karin haske daga bakinka"
Dariya ya yi kafin ya ce." Babu yawun matata dangane da maganar jiya.
Ni asalima ban san cewa tsohon mijinta ya yi aiki da ni ba sai da maganar nan ta fita, idan ma da yawunta a maganar ban ga aibu ba domin ta fito ne a matsayinta na uwa tana nemawa yaranta hakkinsu kamar dai yadda sauran mutane suke fitowa.
Da ita da sauran iyayen marayun da suka yi magana na yi alkawarin bawa kowaccensu miliyan biyar biyar domin dogo da kai, kuma su kula da yaransu.
Wannan na yi ne saboda Allah, sannan kuma har yau hanya a bud'e take ga duk wanda yake da k'orafi akaina zai iya tunkarata kaitsaye idan kuma hakan zai yi masa wahala zai iya isar da sakonsa ta kafafan sadawarsa domin korafinsa ya isa gare ni, a shirye nake da bawa matasa gudumuwa muddin sun bu'kaci hakan daga wurina."
Wannan maganar tasa ta k'arshe ita ta karya karsashin d'anjaridar duk k'wakwarsa sai ya rasa abinda zai fad'a domin kuwa an riga an dabaibayeshi da halin girma da dattako.
To abinda ya dinga tashe kenan a kafafan sadarwa.
Wasu na fad'in hirar a rubuce ya yin da wasu ke d'ora bidiyon hirar a shafikansu ana ta zuba sharhi da cacar baki da bawa hammata iska idan aka samu b'angaranci daga mabiya dake comment section.
An nufe shi da sharri sai kuma Allah Ya juyar da lamarin mabiyansa suka kara ninkuwa sakamakon hirar da aka yi dashi kuma yawancinsu duk matasa ne majiya karfi wanda suka rasa abin yi.
Ni kaina na ji dad'i sosai dana saurari hirar mussaman wurin da ya wanke ni daga zargin da jama'a suke yi mini, duk k'wakwar d'anjaridar bai yarda ya soke ni ya soki iyayena ba, yana ta ko'karin kare mini mutunci amma hakan bai hana shi azabtar da ni ta karkashin kasa ba, gigin sabon aure ne ko tasirin asiri na kasa gane wanda yake dawainiya dashi sai sha mini kamshi yake yi
abinda na lura dashi shine tun ranar da Hauwa ta kwana a dakinsa wasu daga cikin al'amuransa suka canza.
Mussaman daga 'bangarena.
Bai iya tsayawa ya 'bata lokaci mu yi magana ba.
Yau kwana uku kenan tare suke kwana na riga na san hakan dole zai faru tunda kwanaki bakwai musulunci ya tanadar mata shiyasa kwanansu bai daga mini hankali ba
Yadda dai ya canza a lokaci kan'kani shine abinda ya fi damuna tun washe garin ranar da suka kwana lamarin ya sauya salo.
Zuciyata ta dinga yi mini sa'ke-sake akanta domin dai Ina ganin akwai hanyoyin da tabi wajan janye masa hankali ko asiri ko amfani da maganin mata.