← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 276

Sashe 47

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Me yasa baka sanar da ni tuntuni ba sai yanzu da kake gudun kada asirinka ya tuno shine ka kira ni kake ko'karin kare kanka, ban yarda da kai ba Isiyaku bakinku daya da Sammani, kuma wallahi tallahi idan na yi bincike na tabbatar da gaskiyar abinda kuka aikata ran kowa sai ya baci a cikinku."
Ya kashe wayar bai saurari abinda yake cewa ba.

Hajja ta ce." Wani abin ne ya faru kuma?"
Babu sukuni a tare dashi ya ce.'' Hajja ki dubi tsayin shekarun da nayi da Sammani amma yau an wayi gari yana daya daga cikin mutanan da suke kokarin kai ni kasa tare da janyo mini zagi a duniya."
Ya gyada kai cikin damuwa ta ce.'' Sammanin kuma me ya yi maka, ka yi bincike sosai kada ka yanke hukunci cikin rashin sani, Ina ganin Sammani ba zai cutar da kai ba.

Murmushi kawai ya yi ya ce." Hajja kenan, mutum fa ya kan iya canza hali a wasu lokotan saboda wasu dalilai amma yanzu ace kamar Sammani da na d'auki ragamar kula mini da harkokina na bashi shine zai dinga danne ha'kokin mutane ya gina kansa da gumin marayu.

Kwanaki ya kira ni yake gaya mini rasuwar wani ma'aikacinmu, a ka'ida ne daman duk wanda yake aiki a 'karkashina namiji ko mace ya rasu na kan fitar da kudi masu kauri na bawa magana, ko kuma idan ina buk'atar sabbin ma'aikata zan sallami wad'anda karfinsu ya kare na kuma basu jari domin su juya dan cigaba da kula da iyalinsu.

Lokacin da ya sanar da ni rasuwar 'Dayyabu Haruna jajirtacen ma'aikaci na ne wanda kwazonsa ma ya sanya muke shiri sosai na fitar da kud'i miliyar biyar na wakilita shi Sammanin kamar koyaushe ya je gidan marigayin ya yi ta'aziya a madadina ya kuma basu wannan kud'i dana bayar ashe sai ya sanya a lalitarsa, sai yanzu ake sanar da ni iyalan marigayin sun shiga gidan redio suna koke-koke tare da aibata, jarida har ta fita yanzu haka."
Sukairaju daya daga cikin escot d'insa ya shigo da jaridu biyu a hannunsa.

Tun kafin ya k'araso wurin da muke yake fad'in." Kin gani ko, Hajja kin ga maganar da nake miki."
Sukairaju ya rusina tare da mika masa da sauri ya kama hanyar fita ba tare da ya ce komai.

Ni kam idona kansa a lokacin da yake duba jaridun ransa a tsananin b'ace don sai na ce ma wannan shine karo na biyu da naga tsananin fushinsa na farko lokacin da na kai k'ararsa wurin Hajja na biyu kuma wannan abin da ya faru.

Jiki a mace na yi kasa da kaina kwalla ta ciko idonsa ashe zargin mutumin nan kawai nake yi da farko ban fahimceshi ba, da gaskiyar wannan matar da muka ta'ba haduwa a daidaita sahu inda take cewa duk ma'aikacin da ya mutu a karkashin kamfaninsa yana taimakawa iyalinsa.

Hawayen suka zubo nasa hannu da sauri na goge domin Yaya Aminu ne ya fado mini a cikin raina.

Ya duba duk wajan da sunansa ya fito ya kuma duba hoton yaran mamacin hadda mayafiyarsu tana kuka.

Ransa ya sake b'aci ya dubi Hajja cikin damuwa ya furta." Yanzu idan Sammani bai taimakawa wad'annan bayin Allan ba ai bai kamaci ya take musu hakkinsu ba, ban ji ciwon maganganun da suka yi akaina ba abinda ya daga mini hankali yadda shi Sammanin yake zambatata, menene bai mallaka ba a karkashina, shi kansa yanzu yana da halin da zai taimakawa mutane saboda damar da na bashi Allah ya bashi, amma na san abinda zan yi masa."
Hajja a sanyaye ta ce." Hakika Sammani ya yi mini bazata kuma ban ta'ba tunanin zai aikata hakan ba, amma ka yi hakuri ka ji ko, ai ka saba d'aukar irin wannan matsaltsalun ba tun yau ba, ka yi masa hukunci daidai gwargwado amma kada ya yi tsanani, Allah ya yi n
Maka albarka, ya kara tsare mini kai."
Gabad'aya muka amsa har da amarya.

Ya dube ni yna cewa." Ki kawo mini dumaman towon nan."
Na amsa tare da tashi a nutse na nufi kicin din ina fitowa ya ce ki kai mini sama sai ki zo ina da magana daku."
Ba tare da nace komai ba na nufi saman nasa da kayan abincin hannuna.

Lokacin dana sauko Hajja ta shiga d'aki domin hud'u saura a lokacin na san salla za ta yi....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram.

Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*TALLAH*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.

Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.

To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.

Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu.

Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya.

Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne.

To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji.

Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba.

Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu.

In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi.

Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama.

Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.

Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki.

Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki.

Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu.

Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay
*26*
Su biyu na samu a zaune suna dan magana 'kasa-'kasa.

Na k
rasa na zauna wurin da na tashi ina dan jin wani abu a cikin raina.

Ya dube ni a nutse kafin ya furta." Na san dai duk wata nasiha Hajja ta yi muku, ke Hauwa tun muna can na ji anata yi miki fad'a da nasiha kala kala akan aure da kuma ha'kuri da juriya.

Ban cika son fitina ba dalilin ma da ya sanya kenan nake ji a raina zan iya kare rayuwata tare daku biyu rak muddin kuka samar mini da farinciki.

Amina ga kanwarki nan Hauwa dukda ta girmeki da shekaru amma yanzu a matsayin k'anwa take a wurinki don Allah na baki amanarta."
Da sauri na dube shi jin yana had'a ni da Allah wannan mai wankakken idon zai ba ni amana.

Na mayar da kaina kasa ban ce komai ba ya cigaba da maganganunsa wasu akan ka'ida wasu kuwa sun sa'ba da tunanina kamar dai amanar da yace ya ba ni, ban kar'ba kuma zan gaya masa hakan domin wani abu ba zai faru ba ya zo ya tuhume ni a kan wane dalili matar da ta girme ni ta fini gogewa da ilimin boko zai ba ni amana.

Ita kuwa sai gyada kanta take yi tana murmushi tare da cewa." To shikkenan in sha Allahu, duk abinda ya fad'a sai ta ce.

"To za a kiyaye."
Ya ce." To ke ban ji kin ce komai ba."
A nutse na ce." Ni ma na yi alkawari in sha Allahu za mu zauna lafiya, kai kuma Allah ya baka ikon yin adalci a tsakaninmu."
Ya ji dad'in lafazina sosai kuwa.

Ya dubeta Yana fad'in." Sukairaju ya shigo miki da kayanki ko?"
Ta ce." E ya ajiye su a wancan d'akin." Ta fad'a tana nuna d'akin da yake kallon nawa."
Sai ya ce." To babu lefi hakan duk dai mai girkin zata same ni a samana." Ta d'an gyara zama da wani kyataccen murmushi a fuskarta tana kashe masa ido ta ce." My na ce ko dai zaka ba ni waje a saman naka kasan ina da matsalar ciwon kirji bana iya zurga zurgar
hawa bene ko a wajan aiki ne idan na tsananta sai ciwona ya tashi, Ina ganin idan ba damuwa ka ba ni d'aki a kusa da kai zai fi mini sauki."
Sai ya ce." A don wannan ai mai sau'ki ne Hauwa sai ki hau ki duba wanda ya yi miki babu matsala." Ya fad'a yana d'an duban inda nake zaune."
Yanayina bai canza ba sai dai na tafi tunanin manufarta na son zama a kusa dashi don ban yarda da abinda tace ba wata'kila akwai wani abu a cikin ranta.

Ni ba zan yi abinda ta yi ba balle tace ina gasa da ita, ina da 'kiba ina buk'atar motsa jiki babu wani sama da zan hau don ganinta a can, amma ya zame mini dole na zuba ido sosai a kansu gabad'aya.
Chapter 47 · 0% Book details