← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 276

Sashe 139

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba Tabawa da kanta ta d'auko mini takalmin da da nake amfani da shi a d'akina ta kawo mini na sanya na tashi ina fad'in.'' Ladifa alwala ai ta zama dole da fatan babu matsala ko." Tana murmushi ta ce." Babu matsala anti."
Kai tsaye d'aki na wuce na had'o mata Turaruka da sabulai.

Fitowa ta yi daidai da lokacin da ya shigo yana daga bakin kofa suna magana da yarinyar kamar sun d'an saba da juna ko da yake shi din ba ma'abocin shariya ba ne idan yau kuka hadu to zai mu'amulanceka kamar kun yi shekara da sanin juna, mutum mai sau'ki hali da nuna shi ba wani ba ne a rayuwa.

Wannan dabi'un nasa na zahiri sune suka danne ba badi'ini wanda mu da muka dangance shi kuma mafi kusa dashi yake yi mana.

Amma kaf jama'a da ma'aikatansa yana mu'amulantarsu ciki sau'ki babu wata izza da nuna ni wani ne.

Abinda anti Yagana take fad'a kullum kenan domin ita kanta ladabi yake yi mata ko magana suke yi baya iya had'a ido da ita wai ai yayata ce wasu lokacin har anti Yagana yake ce mata kamar yadda nake kiranta abin ya yi ta bani takaici da b'akinciki.

Makirci sai kace babbakakken dan duniyar da ya gaji da yawon bariki kaf ya saye mini dangi har da Baban Saude domin sai da ya san yadda ya yi ya 'kulla abota da shi mai karfi.

Amma nasan Baban Saude mutum ne mai tsinkaye da hangen nesa kuma ba zai ta'ba take gaskiya ya d'auki karya ba idan duk duk duniyar nan za a ba shi yana da taurin kai da ra'ayin rikau!

Ledar hannuna na mik'a mata ina cewa "Ki gaishe da mutan gidan, tunda kin ki kar'bar kudi ga wannan sai ki yi amfani da su, na gode kwarai."
Ta kar'ba tana godiya sosai kafin ta kama hanya ta fita cike da nutsuwa.

Baba Tabawa ta wuce dakinta itama.

Sai mu biyu a falon na daure na ce." Barka da shigowa."
Don girman Allah kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.

A takaice ya amsa kafin ya nemi hanyar matattakalar samansa.

Ban yi kasa a gwiwa ba na bi bayansa.

Ya shiga bandaki nasan alwala zai yi ya fito yana gyara hannun rigarsa dake tattare.

Kallo daya ya yi mini ya kama hanya zai fita na ce." Idan babu damuwa Ina son magana da kai."
Bai juyo ya dube ni ba ya furta." To, bari na dawo daga massalaci." Ya fice a gaggauce.

Na samu gefan gado na zauna babu wani karsashi a tattare da ni, nasan da ban yi masa magana ba, bai zama lallai idan ya fita ya dawo ba, shigowar nan ma nasan ya yi ta ne akan dole domin sanin halin da muke ciki.

Idan yana irin wannan nuk'ufurcin da d'aukewar kai wani irin damuwa nake shiga mara dad'i don ni kuma gaba damuna take yi idan na fara ma bana iyawa gwara kawai a yi fito na fito a shirya amma ba ni son kisan mummu'ke da ba'kin rai.

To ban yi tsammanin amsa min din da ya yi ta bogi ba ce sai da naga har an yi Isha'i ta shige bai dawo gidan ba ya barni zaune a inda ya bar ni ina dakon shigowarsa.

Bakwai saura ya fita yanzu gashi takwas har da minti ashirin na samu kimanin awa d'aya da wani abu zaune zuru a d'akinsa.

Na tashi na sauka kasa raina a dagule haka kawai nake kasa jimirin jure shariyarsa akaina duk dauriyata gazawa nake yi, kuma da na ce ina son magana da shi zahiri ko ya dawo din wallahi ban san abinda zan ce masa ba.

Waya na d'auka na kira shi, bai yi jinkiri ba kuwa ya daga yana tambayata menene.

Daburcewa na yi kafin daga bisani na daure na ce." Ka zo."
Ya ce." Akan wane dalili."
Shiru na yi ina d'an tunani sannan na ce." A lissafin da kake yi yau kwanan wanene a cikinmu?"
Kai tsaye ya ce." Kwana kamar yaya."
Na ce." Kwanan girki mana, wacece take da kai?"
Ya ce." Momi ce take da ni ma, saboda itace nagartacciya matar da take gudun fushina ita nake ganin zan iya kwanan aure da ita, domin zahiri da bad'ininta babu mugunta ko zagon kasa balle zalinci a tare da ita."
Shiru na yi maganarsa na dukan kaina.

Na daure na furta." To mai kake nufi?"
"Ba na nufin komai, kawai dai ya kamata a ce na yi nesa daku dalili ban san menene a zuk'atanku ba ke da ita Hauwan mai aikawa a sayo miki maganin wankin mahaifa."
Maganar ta yi mini nauyi sosai, dama nasan abinda yake ta sa'barsa kenan.

Na ce." Ai ba haka kawai ta aika a ka sayo mini maganin wankin mahaifa ba sai da dalili, idan ma kana ganin da hannunta a wannan case din to ka d'auki hakkinta wallahi."
"Ita din mutuniyar arziki ce kenan?" Ya fad'a da izgili." Na yi shiru ban bashi amsa ba domin yadda ya fadi maganar ya nuna mini cewar a fusace yake.

Jan tsakinsa na ji kafin ya datse kiran.

Na cire wayar daga kunnena raina a kuntacce na tashi na shiga bandaki domin gyara jikina.

Da kyar na iya cin abinci duk kuwa da dokin sakawarar da na yi amma takaici bai barni na ci da yawa ba.

Hauwa kam ko dand'ane ba ta ce ba a daran sai da Baba Tabawa ta yi mata fatan wake da manja da kifi ga uban attaruwun da ta ce a zabga mata saboda yanayin bakinta.

Sai bayan goma na dare tukkuna muka yi sallama kowa ya shiga domin ya kwanta.

Lokacin kiran Hajja ya shigo wayata can saman dirowa romat na d'auka na rage murya domin koda na shiga d'akin kallo na kunna domin idanuwana gabad'aya a soye suke da zallan b'acin rai da damuwa
Na shiga zullumi da nazari sosai a lokacin da na ga kiran Hajja domin sai nake tunanin ko ya sanar mata da wata magana ne.

Yanayin yadda muka gaisa da wasa da dariya ya sanya na dan ji sanyi a raina sosai ta yi mini tambayoyi masu cike da hikima irin ta manya ni na na bata amsa cikin hikima ban yarda na sanar da ita akwai matsala ba tunda bai gaya mata ba, to fadarta daga bangarena takan iya janyo mini matsala babba......
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.

Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*TALLAH!*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl
Momyn Hajara GHT supplements
Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan kowacce irin matsala in sha Allah
Hadin Amare
Hadin Ango
Hadin jego
Hadin uwar gida
Hadin babbar mace
Hadin maida tsohuwa yarinya
Muna da Maganin sanyi kowanne iri
Muna da maganin ulcer
Muna da maganin Asthma
Muna da maganin ciwon zuciya
Muna da maganin ciwon Hanta
Muna da Maganin hawan jini
Muna da Maganin ciwon Ido
Muna da Maganin rashin haihuwa
Muna da Maganin skeler
Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah
Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki
Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya
07012621175
Register 8000 ne kachal
*96*
Ta ce." Ga Yusi dai muna tare dashi anan falo duk ba mu kwanta ba, Kamulu kuma ya ce mini zai shiga cikin gari can gaba da gidanku rijiyar zaki ya ce mini idan ban manta ba an gayyace shi bude wata sabuwar makarantar islamiyya ya ce mini zai kwana a gidan Gwaggo da safe sai ya wuce can din."
Murmushi na yi a tsanake na ce." To shikkenan Hajja, Allah dai Ya saka da alheri na gode sosai, Allah Ya kara lafiya da nisan kwana."
Ta amsa da Amin Ya Allah.

Kafin ta bawa yaron wayar na ji maganarsa yana fad'in." Mama barkanmu da dare.

Na ce." Barkanmu dai Yusi ya kuke?" Ya amsa da "Alhamdulillahi Mama." Shiru ya biyo bayan maganarsa.

Gabad'aya tunda abin nan ya faru yaron baya sakewa da ni.

Kamalu ne ma ya kira ni a waya shi ma sau daya sai ka ce wad'anda aka yi wa wata hud'uba akaina.

Kai na girgiza a hankali na ce." To tunda ba ka da abin cewa sai an jima ko.".

Yana 'yar dariya ya ce." Mama kenan, na yi shiru ne ai ina sauraranki ko da abinda za ki ce mini."
Na ce." Da yake ni ce sarkin k'orafi ko?"
Shiru ya yi bai ce komai ba, amma ina jin sautin murmushinsa.

Na ce." Malam kashe waya ka bawa mai ita."
Da sauri ya amsa da "To Mama." Amma ban ji ya kashe din ba, nasan jira yake yi ni na fara kashe tawa.

Murmushi kawai na yi na ajiye wayar a gefena tare da sauke ajiyar zuciya.

Washe gari kiran wayar Baban Saude ne ya tashe ni da yake jiya na jima ban yi bacci ba idona ya soye da tsabar tunani tare da neman mafita.

Wannan shine dalilin da ya sanya da baccin ya kwashe ni bai ajiye ni a kusa ba domin ni kaina tunda nasan ba ni da tsarki sakin jikina na yi sosai motsin kirki ba na so na yi.

Hannu na kyarma na d'aga wayar lokaci guda idona ya yi tarmazai wani irin yanayi na shiga na fargaba kiran wayar Baban Saude a irin wannan lokacin yana da ala'ka da abubuwa da yawa.

Walau mutuwa ko wata mas'alar domin kuwa nasan a cikinta muke
Muryarsa radau ya amshi gaisuwata ya dora da fad'in gani nan kan hanya domin kuwa daf nake da shigowa garin abuja.
Chapter 139 · 0% Book details