Sashe 103
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai ta kuwa ta kada baki ta ce." Ni ma dole ce ta sanya ni zuwa ai domin kuwa abinda ka boye mini shi Yagana ta je ta gaya mini shine na ce bari na zo da k'afafuna gidan naka na ji dalilin da ya sanya ka b'oye matar mutane a gidanka, idan har za ka yi iko da yaranka Haruna wannan dai baka da k'arfi a kanta kuma babu yawuna a cikin yun'kurin da ka ke ko'karin aikatawa."
Cikin nutsuwa ya ce." Wato Yagana ce ta je ta taso ki da daddaran nan kenan, kin kyauta Yagana na ce kin kyauta." Ya fad'a yana kallonta da b'acin rai a tare dashi ita kuma sai ta yi kasa da kanta tana cike da damuwa ta furta." Baban Saude don Allah ka yi hakuri wallahi ba nufi na ba ne na bata maka rai, amma ni nasan Amina bata da wata hujja gabad'aya ma majority lefin nata ne tunda d'azu Babansu Fadila da ya zo ta gaya masa duk abinda ya faru wanda ni ta rufe mini saboda ta san ba zan goyi da bayanta ba."
Ya ce." Shiyasa ki ka je ki ka gayawa Dada kenan saboda ni ban isa na yi hukunci ba, ko kuma ni zan goyi da bayan k'arya ko?"
Ta yi shiru tana girgiza kanta alamun ba haka ba ne.
Ya gyada kansa da takaici ya dubi Dada tare da ce wa." Duk abinda Yagana ta je ta gaya miki akan Amina kada ki amince da cewa ita kadai ce take da laifi domin shi ma mijin nata da akwai tasa matsalar, kuma yana da kyau ace yarinyar nan an dubi matsalarta an kuma d'auki matakin gyara.
Ba ni da burin kashe mata aure sai dai idan har hakan ya zama dole, sannan kuma ni babu ruwana da wanda take aure dukiya nasaba ko wata d'aukaka ta mutum.
Ni namiji ne amma ba na goyon bayan mazajen da suke zalintar matansu ta kowane 'bangare.
Wannan dalilin ne ya sanya da yawa mutane suke yi mini kallon mafad'aci saboda tsage gaskiya.
Dada babu yadda za a yi yarinya ta kira ni a waya tana kuka akan wata matsalar da ta dameta na ce babu ruwana a ciki dalili wata hujja dan ban zo a b'angaran mahafinta ba to ban ga dalilin da zai sanya na ja baya akan lamarinta ba, idan na yi hakan kuwa tabbas ban dubi zumunci ba, kuma ban yi wa 'yar uwata kara ba.
Ba dalili ba ne a ce wai dangin babanta ne lallai suke da hakkin kare mata mutunci ba, to idan kuma suka gaza fa, ma'ana suka kasa ta'buka wani abu akan lamarinta shikkenan sai ta zauna a hannun wanda bai san daraja da mutuncinta ba......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.
Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.
'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.
A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*68*
Wajan ya yi tsit kowa ya yi shiru yana sauraransa.
Ya nisa kafin ya cigaba da ce wa." Tun kafin ta zo nan ta gaya mini halin da take ciki a waya da kuma ta zo ta sake jadadda mini duk abinda ya shiga tsakaninta dashi da abinda ta aikata masa da matakin da ya d'auka akanta.
Dan Kuskure ta yi kuskure kuma ban goyi da bayan ta sake aikata hakan ba ko bayan raina na gargad'eta domin hakan fasadi ne mai girma.
Ta kar'bi lefinta ta yi nadama ta tuba ga Allah kuma ta nemi gafara to me zai sanya ba za a yafe mata ba.
Wannan sune kadai matsaltsalun Amina, kuma na ja kunanta kwarai da gaske akan ta gyara ta kiyaye a gaba.
Ba wai ina goyon bayanta ba ne a yanzu ta ce ba ta da ra'ayin zama dashi cikinmu babu wanda ya isa ya yi mata dole domin kuwa ita ba yarinya ba ce ta san abinda yake mata ciwo sannan kuma tana da hujja ko a gaban alkali za ta fad'a masa dalilinta na son rabuwa da auransu saboda matsalar rashin daidaituwar jini da za a samar da yara masu ingantaciyar lafiya.
Abu ne ya zo a zamanance ba mu ce za mu yi wa Allah wayo ba, amma zahiri lalurar nan akwaita dalilin da ya sanya ma kenan aka fara d'aukar matakin kare kai daga riskar abinda zai faru bayan an yi aure.
Amma fa wannan bayanin nawa baya na nufin cewa ina goyuwa da bayan yahudawa ba ne a a ko daya domin kuwa ni kaina a lokacin da na auri iyalina babu gwaji na jini kuma ga yara na nan duka mun haifa lafiyarsu lau babu wani mai lalura daga ciki.
Saboda haka Dada ki fahimce ni anan wannan ga'bar kada a tilastawa yarinyar nan a ce dole sai ta cigaba da zama da bawan Allan nan alhalin bai san girma da mutuncin ba."
Dada jikinta ya yi sanyi sosai duk karsashin da ta shigo dashi gidan babu shi a tare da ita a sanyaye ta ce." To yanzu na ji abinda kace Haruna, amma ya za ka yi ka hadu da mijin nata kasan dai shi ba yaro ba ne idan ma ka girme shi ba yawa kuma sannan ba irin mazajen yaranka ba ne da kasa ba yi musu tsawa da gindaya musu sharad'ai."
Dariya ya yi irin ta manya a tsanake ya furta." Ai na girme shi Dada, kuma yana auran 'yata duk kudi da wani abinda yake ji dashi ya zame masa dole ya ajiye a gefe guda kafin ya tunkaro inda nake muddin yana so mu daidaita.
Ni wani kudinsa ba zai rud'a ni ba, ke kan ki kin san da wannan Dada."
Wani irin sanyi na ji ya sauka a zuciyata ta yi fes lallai Baban Saude ya shirya kare mini mutuncina.
Ya dubi anti Yagana babu fara'a ya ce." An ce yana kiranki a waya to na gargad'eki duk lokacin da ya sake kiranki akan lamarin ki ce masa ya nemi inda nake kuma ki sanar dashi daf nake da komawa wurin neman abincina domin ina sa ran a satin nan da za mu shiga asabar ko lahadi zan tafi muddin kuwa ya bari na tafi bai neme ni ba to sai na dawo kuma"
Cike da damuwa da kar'bar umarni ta ce." To shikkenan in sha Allahu don d'azu ma mun yi waya da shi har yana sake jadadda mini cewa shi bai saketa ba bayan wanda ya yi mata a baya shi kad'ai ne ya san w
nda ya yi har yanzu akwai sauran igiyoyin auransa biyu a kanta."
Gyada kansa ya yi yana gyara zamansa ya ce." wannan kuma abinda ya shafe shi ne, ki yi dai yi kokarin bin umarina idan ya tuntubeki akan matsalarsa ki ce masa ya nemi inda nake domin kuwa matarsa tana hannuna."
Ta ce." To in sha Allahu rabbi."
Kwanan farinciki na yi a ranar saboda irin tsayuwar da Baban Saude ya yi akaina na ji dad'i kwarai da aniya kuma na yi masa addu'ar samun lada a wurin Allah.
To kwana uku a tsakani zuwansu Anti Yagana da safe ina bacci Sayyada ta shigo tana tashina wai Baban Saude yana kirana.
Da zullumi na tashi na fita na wanke bakina sannan na nufi d'akinsa da yake can gefe da tsakargidan na yi sallama a nutse na shiga yana zaune da tukunyar shayi da mangal a gabansa ya gama dafa shayin yana tsiyayawa a kofi.
Na sake gaisheshi duk da cewar d'azu kafin na kwanta mun gaisa.
Ya amsa yana d'an motsa shayin da cokali kafin ya dube ni a tsanake ya ce." Jiya Yagana ta kira ni a waya ta gaya mini mijinki ya bu'kaci da a bashi lambata shine take neman izini na ce ta bashi babu komai to shine yanzu nan ya kira ni a waya yake gaya mini cewa yana nan tafe gobe juma'a komai dare zai shigo akan maganarku shin ya kike gani.
Ni ba zan yi miki dole ba fa Amina domin kuwa ba kowane yake zaune da mutumin nan ba sai ke, idan har kin ga da 'kwara da cutarwa a ciki to ni don na ce masa ya sawwa'ke miki ba abu ne mai wahala ba a wajena.
Idan kuma kin ga kina so ki cigaba da zama dashi sai a ja masa kunne tare da gargadin wannan ya zama na farko ya kuma zama na 'karshe idan har bai daina ba a gaba sai a d'auki matakin rabuwa ko yana so ko baya so tunda akwai al'kalai, shari'a kuma tana kan kowa da mai kud'i da kuma mai mulki.
Shiru na yi ina nazarin maganarsa.
Babu shakka Baban Saude ya cika jarumin namiji domin kuwa abinda ya yi a yanzu ba kowanne zai iya yi ba dalili shi wanda za a titsiye din mutum ne wanda Allah Ya wadatashi da farcen susa ya kuma rataya masa taguwar arziki.
Na ce." Baban Saude idan har na rabu da auran mutumin nan duniya za ta zage ni.
Sannan anti Yagana za ta 'kullece ni tunda har yanzu ta kasa fahimta.
Ga 'kawata aminiyata Sahura mun samu matsala da ita duk ta dalilin haka.
Zan cigaba da hakurin zama dashi muddin an nuna masa cewa abinda ya ke yi mini ba daidai ba ne, idan har ya gyara kuskuransa ni kuma na yi maka al'kawarin in sha Allahu rabbi zan yi kokari wurin ganin mun zauna lafiya, kuma zan kiyaye abinda zai sake kawo sa'bani a tsakaninmu kamar yadda ka yi mini nasiha."
Gudun aure littafin kudi ne kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.