← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 263 OF 276

Sashe 263

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gidan an yi masa sabon fenti ciki da waje har da ties a tsakargidan da d'akunansu wannan aikin Usaini ne ya gyara gidan sosai bayan wanda na yi musu ya yi musu sabbin d'inkuna Babanmu tsaf da shi cikin manyan kaya ya sake murmurewa.

Sosai hankalina ya kwanta ganin yadda aka samu daidaito tsakanin matan gidan duka sun daina abinda suke yi Ummansu Saminu ta fito ana ta hidima da ita yayin da 'yan uwan Ummansu Hadiza suka cika gidan zuwa na ya sake bud'e babin gaisuwa har da rige-rige a tsakaninsu lamarin nan dai ya tabbata da ake cewa kudi suna sayan girma kuma suna kankaro mutunci.

Ma'kotan gidanmu da ada suke yin surutu a kaina a duk lokacin da Ummansu Hadiza ta yi musu gulmata sai na zama abar fadanci da gurfana tamkar wata basarakiya.

Ranar da aka d'aura auran da daddare ya kira ni yana gaya mini bai tafi ba sai gobe don haka Ayuba zai zo ya d'auke ni da yaran mu kwana can gidana na sharad'a.

Na ce masa ya bari gari ya waye domin duk mun gaji har yaran su Hassan ma sun yi bacci tun d'azu.

Ya ce a a mu Ayuba zai zo.

Haka na kintsa ina gayawa anti Yagana yadda muka yi da shi ta ce mu tafi din kawai tunda hakan ya bukata.

Wajan tara da arba'in Ayuba ya zo ya kwashe mu a mota amma banda amaryar tukkuna dole za ta yi sallama sosai da mahaifiyarta.

Kwanciyar aure zai yi da ni a daran ashe shine dalilin da ya matsanta lallai sai mun dawo dalili matar da yake d'an ragewa da ita tana can saudia basu dawo ba shi ya gaya mini tare ya biya musu da mahaifiyarta da kuma Kawunta da ya zo ya yi musu sulhu wattanin baya.

Daga lokacin na gane dalilin da ya sanya ta sassauto har take taka kyasa da k'arfi ganin ta fara samun kansa kyautar umara ya yi wa iyayenta biyu wannan kuma shine karo na biyu tsakaninta da Inna Uwanin a shekarun baya tun kafin ya kai k'arfin haka ya ba su kujerar ita da Hajja da Samira duk su hudun suka je lokacin suna soyayya kafin auransu.

Ya yi yadda yake so ban hana shi ba dalili nasan ya jure tunda kusan kwanaki biyar kenan rabon da mu had'u da safe yake gaya mini gidan da ya mallakawa Sukairaju amma ba a cikin estate din da muke ba ya d'an yi gaba da mu.

Ya nuna mini shi a waya maidaidaci ne plate wanda aka yi wa ginin zamani daidai gwargwado kuma ya ja kudi sabo ne kuma na yi masa murna sosai ya kuma tabbatar mini da cewa a shirye gidan yake shiga kawai za su yi.

Yini guda muka yi da shi a d'aki yana ta maimaita abu daya don a k'alla sai da ya neme ni sau uku bayan wayewar gari da safe bayan mun karya da azuhur ya yi sallah sai kuma da yamma wanda shi ya yi bala'in gabalabaitar da ni na yi kwance a gado ina nishi wai lallai sai an samu ciki bayan shi kansa ya san yawan yin wannan abu ba shine yake bada ciki ba.

K'addara ma a samu d'in amma ai ba mu da hurumin nunawa Allah abinda muke so idonsa gabad'aya ya rufe har na rasa inda tunaninsa yake har da cewa yana ganin a shekarar nan zai mutu shiyasa ya damu da ganin na sake haihuwa.

Baba Tabawa ita ta dinga hidima da yaran gabad'aya domin ban sauko ba sai bayan biyar da rabi a gajiya tubis ga gajiyar bikin Hadiza ga wadda ya tara mini
Ta yi abinci tsaf ta gama shirya ko'ina da yaran gabad'aya suna zaune a falo suna kallon cartoon Hasan na wasa a kusa da ita shi kuma Usaini na dafa kujera yana mi'kewa tsaye Sultan na ri'ke hannunsa.

Na zauna cikinsu zamana kuwa ke da wuya suka rufe ni kowa da abinda yake fad'i mussaman Minal duk ta kanainaye ni ta ko'ina.

Yana dawowa daga sallar magriba yake gaya mini rasuwar Malam D'aha a lokacin ne Malam Rabi'u abokinsa ya kira shi a waya ya sanar da shi amai da gudawa ya yi kwana daya don asibitin zana ya rasu.

Na kadu sosai da rasuwar malamin jikina ya mutu na zauna ina Kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un babu babu shakka maza sun tafi Allah Ya kar'bi ayyukan alherin da aka yi dominsa.

Da sassafe mu ka dauki hanya ni da shi domin samun ta'aziyya a daran dama na kira Usaini na ce cikin hikima ya san yadda zai sanar da Hajara domin kuwa tsohon ciki ne da ita haihuwa ko yau ko gobe ya tabbatar mini da cewa da wuri za su tafi shi da ita inshallah.

Aikuwa a can muka same su gidan Malam ya kacame unguwar ma gabad'aya motocin manyan mutane ta ko'ina da yake karkara ce akwai filaye sosai da aka samu damar ajiye motacin.

Hajja ma can muka same ta lokacin an gama shirya gawar za a fito da ita domin a sallace ta.

Sai bayan da aka d'auke shi zuwa gidan sa na gaskiya tukkuna na samu sararin bin dakunan matan gidan ina yi musu gaisuwa da yaransa mata aurarru Hajara na cikinsu sun yi kuka har sun gaji na yi musu gaisuwa sosai kafin na koma na zauna wurin da Hajja take a killace muka sake gaisuwa tare da yi wa juna ta'aziyya.

Wajan biyu na rana Babanmu anti Yagana Hadiza da su Fati da Ummansu Saminu suka zo Ummansu Hadiza
kawai a ka bari a gidan Saminu da Ashiru duka tare suke Hajara da kanta ta dinga bi da su d'akuna suna yin ta'aziyya sannan mazan suka fita waje su kuma su anti Yagana muka zauna a tare a wuri d'aya.

Hajja can muka barta da za mu tafi ta ce ba zata iya wannan kai kawon ba sai anyi addu'ar uku tukkuna.

Amma ni da shi haka muka dinga wannan kai kawon muje mu dawo har sai da aka yi addu'ar uku tukkuna.

Ranar sadakar bakwai kuma shi kadai ya tafi bai ce na shirya ba sai ya dawo tukkuna yake gaya mini tare suka je da Hajja.

Kwanaki goma da rasuwar Malam D'aha muka shirya komawa abuja lokacin Hauwa ta kwana kusan shida da dawowa kira shi a waya babu adadi ya kuma gaya mata babban rashin da aka yi ba wai jin dad'i ne ya zaunar da shi ba don a ganinta tunda muna tare wata'kila ni na hana shi dawowa bayan kwanakin da ta yi a saudia ya kamata a ce ya yi d'okinta.

Ranar da muka koma kuwa a gidanta ya kwana domin hura masa wuta ta yi babu kintsi ya tafi ba cikin dad'in rai ba.

Hadiza a can muka bar ta.

Sai bayan sati daya tukkuna angon ya je ya daukota kai tsaye kuma gidanta ta sauka sai da ta kwana biyu da tarewa tukkuna na je na ga gidan alhamdulillahi Hadiza ta 'yantu ta yi gida gayun nan da ake ta nema yanzu ya samu an ci ado da kwalliya irin na amare abin dai gwanin burgewa da sha'awa nan take gaya mini Ummansu ta ce bayan ta dan yi wattani sai su shirya zuwa ganin d'aki dangin babamu da danginta na ce hakan ya yi Allah Ya sanya alheri.

Kwanaki talatin da uku da rasuwar Malam D'aha Hajara ta haihu mace tun daga haihuwar aka ce mini an yi mini takwara dole haka na shirya tafiya da gudumawar kayan baby kwanaki uku kacal na yi a daddafe domin da 'kyar ma ya bari na dawo gida tunda ba taron suna aka yi ba saboda rasuwar mahaifinta.

Amma alhamdulillahi ta haihu lafiya lau ita da baby suna cikin koshin lafiya yarinya kamar Usaini ya yi kaki ya tofa saboda tsananin kammani.

Na kudi ne littafin kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.
****
Bayan wata hud'u zaman namu ni da Hauwa yana ta tafiya a waskace babu tsari sai dai zangon 'kasa da kuma bita da 'kulli tunda nake kafata bata ta'ba taka gidan Nusaiba ba wallahi don wasu lukutan har kunyarta nake ji yarinyar har ta gaji da tambayata yaushe zan zo nakan ce mata ina tafe in sha Allahu amma Hauwa ta riga ni saboda gulma tana cin ko'kon ranta kawai yarinyar ta kira ni a waya tana gaya mini wai Hauwa ta je mata ta yini har ta kai mata mayafai biyu da hijabai irin wanda ta zo da su daga makka har tana gaya mata cewa Hadiza ba tsaran auran Sukairaju ba ce dalili karuwa ce kuma 'yar kungiyar shan jini an cutar da shi kuma ta girme shi nesa ba kusa ba wataran za a wayi gari babu shi ta nemi wani sassa na jikinsa domin alamu sun nuna zaman da ta yi gidan gyaran hali bai koya mata darasi ba don haka dole za ta matsantawa maigidan ya dawo mata da yaranta saboda tana jin tsoro kada a wayi gari babu daya daga ciki mun had'a baki mun bawa dodon tsafi tunda ni kishiyartace kuma ba ni k'aunarta zan iya yin komai domin ganin bayanta da yaranta saboda ni da 'ya'yana mu gaje dukiya.

Wallahi bakina mutuwa ya yi na rasa abinda zan cewa yarinyar kaina ya yi bala'in d'aurewa wata'kila fahimtar hakan ta yi daga wajena yasa ta shiga ba ni ha'kuri tana fad'in ba ta san hankalina zai tashi ba kuma ta yi rantsuwa da Allah ba ta ta'ba gazgata maganarta ba domin ni din ma na fiye mata ita sau dubu.

Har muka yi sallama ban iya ce mata komai ba saboda mamaki lallai wannan al'amari ya daga mini hankalina ba kad'an ba.

Duk wasu kaidi da sharri Hauwa ta yi mini na jure saboda dalilai masu yawan gaske amma ina ganin wannan kam ba zan iya ha'kura ba dalilin da ya sanya kenan yana shigowa ban ma bari ya huta ba saboda da abin na yini shima ganina a hargitse cikin rashin nutsuwa ya shiga hankalinsa na shiga gaya masa abinda kunne na ya ji wanda nake da tabbacin cewa yarinyar nan Nusaiba ba za ta yi mini karya ba.
Chapter 263 · 0% Book details