← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 276

Sashe 46

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama.

Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.

Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki.

Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki.

Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu.

Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay
*25*
A shagwa'be na ce." Mutumin da yake da sabuwar amarya shine yake cikin damuwa, gaskiya ban yarda ba dadin baki ne."
Murmushi ya yi tare da cewa.

Za ki gayawa 'yan garinku ai."
Na ce." Baba ina Hajja ne ka gaya mata na yi kewarta Yusi kuma bana nemansa tunda ya manta da ni."
Yana dariya yake ce wa." Hajja na can wurin 'yan uwanta Yusi kuwa yanzu ya tashi ya fita zuwa wurin abokansa kin san shi da saurin sabo ya samu abokai anan din ."
Sai na tsinci kaina da cewa.

" Amma tare zaku dawo?" Gabad'aya hankalina ne bai kwanta ba nasan family dinsu babu mai kaunata sai shi sai mahaifiyarsa da 'yar uwarsa Hajiya Saratu mai sunan mamana.

Dalilin da ya sanya ma kenan na'ki binsa a lokacin da zai tafi babu irin rarrashin da bai yi mini ba na ce a a bana zuwa.

Ya ce." Ai ba tare muka tafi ba kin ga da kunya na je na cewa Hajja ta ba ni shi mu tafi ko."
A sanyaye na ce." Hakane kuma."
Kamar ya fahimci abinda yake cikin raina sai ya ce." Ki yi hakuri babu abinda zai same shi in sha Allahu rabbi."
Da sauri na ce ." Ai ban ce dama wani abin zai same shi ba baba, yanzu me kake so ka ci?"
Duk abinda ki ka yi mini zan ci, ina da yin sallar la'asar zan taso in sha Allahu."
Na ce." To shikkenan Allah Ya tsare sai ka dawo."
Cike da karsashi da kwarin gwiwa na ajiye wayar ban tsaya jinkiri ba na fara had'a abinda zan sha domin rikita masa lissafi....08089965176 Muna da ingantattun magungu
an mata masu masifar rikita maigida.

Na shirya masa towo miyar ku'bewa domin shi ma'abocin cin abincin gargajiya ne baya rabo da shan farau farau da dumame! shiyasa nake ajiye masa da safe na d'umama kafin ya fita ya ci.

Gidan ya yi mini girma sosai domin ni ka'dai na kwana da rana ne nake jin karakainar masu aiki magariba kuwa tana yi na shiga d'aki na rufe don ma gidan cike yake da masu tsaro shiyasa na dan samu sasaauci.

Na san dai tunda jirgi ya biyo ba zai wuce takwas na dare ba ya sauka, amma abin mamaki sai gashi har wajan goma da wani abu babu alamanunsa, na d'auki wayata domin kiransa na ji lafiya a kashe duka layukansa basa shiga.

Ban kawo komai ba a raina ba, amma na fi tunanin ko bai samu tashi da wuri ba.

Bashi da jirgi na kansa amma yana da alfarma dalilin matsayinsa da kowane lokaci zai iya tasowa.

Sha biyu na dare tana bugawa na fitar da raina da dawowarsa, raina a k'untacce na k'ara lalubar lambobin wayarsa har yanzu a kashe suke basa shiga.

Lokaci guda zuciyata ta fara yi mini sa'ke-sake akan canza shawara ya yi kenan bayan ya sanya ni yi masa abinci har da shan maganin mata shine zai kashe wayarsa ba ma zai kira ni ya gaya mini dalilinsa ba.

Na kwanta ina ta juyi marata ta dame ni da ciwo sai had'e cinyata nake yi ina mi'ka tsabar bu'katuwa tabbas dana san ba zai dawo ba da ban sha komai ba.

Da 'kyar bacci ya d'auke ni mara dad'i da armashi don haka kiran sallar farko na tashi sai da nayi wanka tukkuna na d'aura alwala na fito.

Ina idar da salla na sake lalubar wayarsa is switchup, cike da tsantsar takaici da b'acin rai na ajiye wayar na koma gado na kwanta ina ha'de jikina domin har yanzu a dame nake dama idan nasha hadin yakan yi sati a ko kwana biyar bai daina aiki ba.

Hawaye suka zubo mini nasa hannu na goge ina ayyanawa a raina wata'kila ita ta hana shi dawowa, ai dama an ce amarya ko ta buzuzuce sai an yi d'okinta, 'karin takaicina ma da ya kashe wayoyinsa tabbacin baya buk'atar a dame shi da bakinsa ya fad'a yana da damuwa kuma na san ko ta mecece babu yadda za a yi ya ga amarya a kusa dashi bai ta'ba ta ba.

Sai wuraran bakwai da wani abu ya kira ni.

Da kamar kada na d'auki wayar saboda yadda nake jin haushin abinda ya yi mini.

Na daga a can kasan makoshi na ce." Ina kwana?"
Da sauri ya amsa yana cewa." Allah Ya taimake ki na yi lefi ko?"
Cikin dauriya na ce." Lefin me?"
"Jiya mun yi dake zan dawo ban samu tahowa ba saboda inna Uwani ta ce mini na tsaya kawai mu taho tare da amaryar tana sallama da 'yan uwa ne, shine dalilin da ya sanya ki ka ji shiru."
A nutse na ce." Shine dalilin kashe waya ko?

Ai ka bugu ka gaya mini halin da ake ciki." Babu wata damuwa a tare dashi ya furta." Na yi lefi ki yi hakuri, na kashe wayar ne saboda ina buk'atar hutu don wallahi kin ji na rantse miki sallar Isha'i ma sai da tsakiyar dare dana farka na yi ta, domin bacci ne mai nauyi ya d'auke ni."
"Humm! kawai na ce domin har yanzu ban yarda da abinda ya fad'a ba.

Ya cigaba da cewa." Ni na kammala shiryawa tsaf ita nake jira kin san shirinku na mata, tare ma za mu taho gabad'aya harda Hajja wai ta fasa zama."
Na daure zuciyata na ce." To Allah Ya kawo ku lafiya, na d'umama maka towonka ko?"
"Ki d'umama mini idan mun sauka zan ci in sha Allahu."
"Shikkenan to sai kun dawo." Na kashe wayar ban jira ya sake cewa komai ba, domin duk bin k'wakwkwafina ya'ki ya nuna mini yana zumudin amaryarsa wanda ni Kuma zan kafa masa hujja da hakan.

Kishi ma sai ya dinga sanya ni wasi wasi ina tunanin wata'kila ma tana zaune a kusa dashi ya kira ni yake tsarana ni da dadin baki.

Ina aiki abin yana cigaba da damuna a zuciya gabad'aya a rikice nake don tunda nasha maganin nan jiya nake cikin matsananciyar sha'awa, abin ya hadu ne da jin dadi da kuma adadin shekarun na da nake a yanzu ina kan g
niyar buk'ata, bayan haka kuma ya yi mini mugun sabon da mutukar bai kasance ni ba a kullum zan iya shiga wani haliin.

Falalu na kira domin ya cigaba da abinda na fara don yanayin jikina ba zai barni na ayi abu daidai ba.

Wannan littafin na kudi ne sister kada ki karanta mini shi ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Ina wanka ina tunanin halin da zan kasance tunda dole dai na ha'kura dashi tsayin sati tunda budurwa ce abinda musulunci ya bata kenan.

Ban san yadda zan yi ba don gaskiya ba abinda nake buk'ata sai namiji a cikin yanayin da nake ci.

Sai wajan uku na rana suka sauka.

Ban yarda yanayin da nake ciki ya sanya mini nawa da kasala ba balle wani daga cikinsu ya ga kamar kishi ne.

Na tar'be su da fara'a har ita amaryar da samu kujera ta 'kame ta ci uban gayu kamar wadda zata je gasar sarauniyar kyau harda alkyabba.

Shi bai tsaya ba kaitsaye samansa ya nufa domin kallo d'aya na yi masa na fahimci akwai gajiya a tare dashi.
a daidai lokacin dana fito daga kicin da tire a hannuna na ji tana ce mata "Ai ni ma tafiya zan yi, dama dalilin zamana goyon cikin Amina ne to ta haihu Allah ya tabbatar da aurenki da Tajo zaman me zan yi kuma, Ina dai kara gaya miki kada na ji kada na gani Hauwa nasan halin kowa daga cikinku don Allah ku zauna lafiya."
A nutse na ajiye Tiran abincin na ce." Haba Hajja ya na ji kina fad'in tafiya za ki yi, ki yi zamanki mana."
Ta girgiza kai tana ko'karin d'aukar gorar ruwa na d'auka na bude mata ta furta." Gwara na tafi Amina ai daka ke har ita Hauwan ba yara ba ne na san ba za ku ba ni kunya ba."
Cikin nutsuwa na ce." In sha Allahu rabbi Hajja."
Ta ajiye gorar ruwan bayan ta 'kurba a nutse ta ce." Dama ba ni da matsala dake Amina tunda zama ya had'a ni na ga halinki, itama Hauwa haihuwarta ne kawai ban yi ba kowa yana da dabi'a mai kyau a cikinku, don haka don Allah ku ri'ke amanar junanku, ku zauna lafiya kada ku yarda ma'kiya su ji halin da kuke ciki."
A daidai lokacin da take wannan maganar ya sauko daga saman yana waya ya yi wanka yana sanye cikin farar jallabiya idonsa da gilashinsa as'usul.

Ya zauna kusa da Hajja Yana cigaba da wayar da yake yi.

Duk muka yi shiru domin yanayin yadda yake fad'a a wayar shi zai tabbatar maka da cewa akwai matsala.
Chapter 46 · 0% Book details