← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 262 OF 276

Sashe 262

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka dai ya dinga kaucewa neman fitinata domin so na yi ya tanka na fad'i abinda yake raina sai ya'ki biye mini ya kira ta a gabana yana fad'in ta turo Ladidi ko yaron dake bawa shokokin gidanta ruwa ya d'aukar mata.

Ya kashe wayarsa.

Ya dinga jana da hira a lokacin da nake zaune a gefansa yana aiki a computer na ki biye masa ni ma.

Sai ya ja bakinsa ya yi shiru tsayin minti ashirin da biyar ya gama abinda zai yi ya rufe Loptop din Yana kallona ya ce." In banda dole sai an janyo mini tsiya a gidana ya za a yi rigima akan zogale Amina wai don Allah menene yake damunku ne?"
Na dube shi ina fad'in." Halin tsiya ai yana wajanta Allah Ya yi maka mai kyau duniya da lahira ni ai ban ce komai ba, ka ce a dibar mata zogale an yi yadda ka ce din to kuma sai ya zama lefi."
Ya gyad'a kansa still idonsa a tsaye a kaina ya furta." Shine na ce ai kuna nema ku ba ni kunya saboda rashin tsinkaye da tunani ita tana can tana surutai na banza bisa wani zargin da bashi da toshe ke kuma gaki ba ki da fahimta wato cewar da na yi a dibar mata zogalen da Masa'udu ya kawo sai ya zama a lefi a wurinki Amina har ki dinga ko'karin zagi na."
Da sauri na ce." Yaushe na zage ka don Allah?"
Ya nuna kirjinsa da yatsa yana fad'in." Kin san dai ba zan yi miki k'arya ba ko, ai ni ba kurma ba ne na ji lokacin."
Kasa'ke kawai na yi ina kallonsa da mamakin yaushe ya koyi 'karya mai lasisi irin haka.

Nasan dai gwani ne shi wurin juya magana idan yana so ya kare kansa ko ya kashe wata rigima yanzu nan zai sar'kafe ya cukurkud'a magana ya kuma dage shine da gaskiya yanzu ma abinda ya shirya yi kenan uana so ya d'aure ni da jijiyar jikina ban zage shi ba amma gashi yana fad'in na zage shi ai ba mahaukaciya ba ce ni.

Ya cigaba da sakin maganganu." Duka kun raina ni wallahi saboda na yi sanyi ina bin kan kowacce da abinda take so babu wadda nake tsoro na yi miki ta bafulatani aradu na d'aga 'kafa ne kawai don ganin yarana suna girma nan da shekaru takwas twins dina sun zama cikakkun 'yan mata 'yan 16years lokacin ko ina raye ko ba na raye Allah ne ka'dai masani."
Ya sassauta maganar cikin alhini tare da 'kura mini ido.

"Hum kawai na ce kafin ajiyar zuciya ta biyo baya na furta." Allah Ya kyauta dai Ina ganin dai ko tsufa muka yi gaskiya da wahala matarka ta canza domin ko kai kasan yadda nake hakuri bisa dabi'unta yanzu don girman Allah menene don ta kira ni ta ce tana son zogale kai ba ka yi tunanin cewa akwai wani abu a zuciyarta ba har yanzu."
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Yadda ba zata canza ba haka zalika kema ba za ki janza ba giwa.

Na san halin kowacce a cikinku. tunda Ubangiji na ya jarrabeni daku a matsayin abokanan rayuwa dole na yi hakuri mussaman kuma da kuke ha'kuri da ni."
"To yanzu dai idan na fahimta ka goyu da bayan abinda ta yi kenan tunda na ga kamar kana kare ta."
"Ban goyu da bayanta ba Amina na nuna mata cewa tana da ikon shiga kicin dinki ko kuma ta tambayeki ba ni son kumbiya-kumbiya fa wasu lukutan daga cikin dabi'unki na burge ni domin ba ki da rufi kuma ba ki da munafurci na gane shine dalilin da ya sanya idan an yi miki hakan yake yi miki zafi."
Na janye idona daga kansa ba tare da na ce komai ba.

Ya saki ajiyar zuciya yana fad'in." Kafin na shigo Sukairaju ya yi mini bayani har results din duka ya nuna mini.

Na yi murna na kuma yi addu'a kwarai abinda za a yi yanzu da kaina zan tashi zuwa Kano wajan Baba domin nemo auran hakan ya yi ko?"
Na d'an saki fuskata ganin yadda ya karrama ubana har yana kiransa da Baba na ce hakan ya yi sosai Allah Ya tabbatar da alheri."
Ya amsa da Amin yana fad'in." Idan kuna da idon sanin can garin nasu Sukairaju hakkinku ne domin fad'ad'a bincike a kansa da zuriarsu domin sake gazgata abinda muke hasashe da wanda na sani a kansa."
"Gaskiya ba mu da kowa a garin wallahi, amma komai na Allah ne kuma tunda ka ba da tabbacin akansa da zuriarsu ai ba sai an sake wani binciken ba alheri dai muke ta addu'a akan Allah Ya wanzar musu damu gabad'aya.''
Ya ce." To hakan ya yi in sha Allahu rabbi cikin satin nan zan shirya zuwa Kano kuma babu buk'atar d'aukar dogon lokaci tunda dukkaninsu babu yaro a ciki."
To idan Ubangiji na ikonsa babu wani mahaluki da duk iko da shahararsa a duniya da ya isa ya dakatar buwayar Allah domin kuwa rahamominsa suna da yawa.

Ni dai ban taba tunanin wai akwai dangantaka ta aure tsakanin Hadiza da Sukairaju ba sai yanzu da Allah ya bankad'a abinda yake rubuce a kudirarsa.

Kamar yadda nake wannan tunani da mamakin itama nasan haka take cikin wannan tunanin na kasantuwar auransu da Ubangiji Allah yake shirin tabbatarwa.

Bayan zuwansa wajan Babanmu an samu nutsuwa sosai da fahimtar juna tare da amincewa daga kowane bangare domin kuwa ba su riga ma sun tsayar da maganar d'aurin auran ba sai da kawunan Sukairajun suka zo su biyu daga Zamfara aka yi zaman dasu tare da bada sheda da tabbacin cewa sun kar'ba bisa amana.

A take a lokacin ya biya sadakin Hadiza bisa jagorancin kar'bar auran da ya biyo ta hannunsa.

Hadiza ta yi goshi dubu dari biyar sadaki suka tsayar da ranar d'aurin aure ranar takutaha ranar da aka haifi manzon Allah s.a.w domin samun falala da dacewa.

A ranan da daddare Ummansu ta kira ni a waya godiya kamar za ta yi kuka har sai da na ji wani iri a raina na dinga tausarta domin dai kukan da ta dinga dannewa sai da ta yi shi a cikin waya da kyar muka to sallama.

Na kira anti Yagana a gaban Hadizan na sanar mata da yadda aka yi itama murna kamar ta zuba ruwa a k'asa tasha.

Hadiza na gefe sai murmushi take yi domin tunda na gaya mata mun yi waya da maigidan ga yadda ake ciki ta rasa yadda za ta yi da ranta saboda farinciki.

Kwanansa hud'u a kano ya dawo da daddare tare suka je da angon dama.

Na tarbe shi sosai tare da yi masa bangajiya da godiya a daran kuwa ya samu tar'ba mai kyau mai tafe da sabon salo wanda bai san shi ba.

Muka shirya tafiya kano kafin zuwan ranar ni da ita da yaran duka tunda an yi musu hutun boko da islamiyya mun shirya walima domin nuna farincikinmu ga Allah anti Yagana ma tana can tana shiri domin ta ce kaf yaranta da su zata zo.

Saura kwana biyu mu tafi Hamusu ya kira ni yana gaya mini Sukairaju ya sanya shi had'a lefe akwati shida tambayata yake yi aure zai yi?"
Hadizan tana zaune a gefena a lokacin da muke yin wayar na gaya masa aure zai yi kuma Hadizar gidanmu ya kuwa shiga farinciki sosai yana ta fad'in ta samu lefe domin milayan shida ya tura ya ce a had'a lefe na kece raini kuma a shagonmu." Lamarin ya yi mini dadi sosai na juya ina kallonta tana murmushi bayan mun yi sallama da shi na dube ta kafin ma na yi magana ta furta." Kudin ya ce zai ba ni sai kawai na ce ya yi magana da Hamusu ya kuma tura masa shi zai had'a komai."
Da murmushi a tare da ni na furta." Na taya ki murna Hadizan gidanmu ta yi goshi kin zama bazawara mai kafasiti yanzu abinda ya rage muna dira kano a yi gyaran jiki sannan na kai ki gidan GARKUWAR MATA ta had'a mini ke da kyau!

Ta kuwa fashe da dariya sai ka ce wata shashasha.

Na shiga taya ta sai muka zama kamar sakarkaru rayuwa kenan bayan wucewar kalubale mabambamta da 'kin jinin juna tare da 'kyama ashe akwai ranar da Hadiza za ta k'aunaci cigabana duk son kud'inta sai ta ce a a gwara a yi sayayya a wurina saboda na cigaba.

Lallai bahaushe ya yi gaskiya da yake fadin ranar naka sai naka.............
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*172*
Duk abinda ya kamaci Hadiza na gyaran jiki ni na d'auki nauyi don har tana cewa za ta gayawa angon ya bata kudin gyaran jikin na ce a a kada lalacewar ta yi yawa yadda ya fitar da kudi masu kauri domin yi mata lefe irin na budurwa mai jini a jika bai kamata a ce ya bada wasu kudin ba.

Sosai na yaba masa dangane da abinda ya yi mata duk a kokarinsa na ganin ya dakusar mata da damuwa kuma da alama yadda Allah Ya jarrabeta da sonsa haka shima yake k'aunarta domin matar so ai ake yi wannan hidimar a matsayin dai Sukairaju tsayayyan namiji mai suffa da mazantaka ina da tabbacin ba zai rasa 'yan mata da suke kawo masa caffa ba.

Amma shi so babu ruwansa Hadiza ya hango cikin dubbanin 'yan mata da zawarawan da suke a wannan duniya.

Anti Yagana ta riga mu zuwa domin da muka isa kanon a gidana na sharad'a muka sauka sannan gari yana wayewa muka yi gidan GARKUWAR MATA yini muka yi a tare da ita ta sabunta ni ta kuma sabunta Hadiza da ciccibi tare da dahuwar 'yan shilla aure biyu da duk wani abinda ya kamata.

Kuma Koda muka gama da ita gidana muka sake komawa sai da gari ya waye bayan mun kintsa muka nufi can gidan na mu gabad'aya ni da ita da Baba Tabawa domin tare muka zo da ita saboda yaran Mairo da Taburni suna gida Abuja muka bar su.
Chapter 262 · 0% Book details