Sashe 193
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
What'sapp group 1k Ko kuma arewaa arewa pen*
*0542382124......
Binta Umar Opey bank*
*07084653262*
*130*
Wayata na duba lokacin tara da arba'in da biyar na safiya Lallai yadda ya tashi garau din nan yana da kyau ya sanya sabbin kaya gobe idan Allah Ya kaimu da rai da lafiya.
Muna harkar huluna da takalma sosai next target dina bude shagon yaduka da shaddodi in sha Allahu amma dai yanzu ya zama lallai a nemi k'wararran tela wanda ya iya d'inki sosai ya yi masa orgent akwai su k'wararru muddin da kudi yanzu za ka ga biyan buk'ata.
Koda Hamusu ya d'aga wayar bayanin da nayi masa kenan ya ce in sha Allahu yanzu zai fita zuwa yamma zai kira ni na ce babu matsala.
Wanka na yi na shirya sannan na zauna na karya da kunu da wainar gero na ji dad'inta sosai dalili na jima ban ci taba kwanciyar hankali da nutsuwar da na samu ya sanya d'andanon bakina ya d:an dawo har ina jin bambacin sukari da gishiri.
Gama karin kummalona ke da wuya su Hajja suka fito da shirin tafiya kafin su tafi din mun d'an jima muna magana tukkuna suka yi sallama da iyalin malamin suka kama hanya suka tafi.
Ashe anti Yagana tun jiya da daddare ta zo garin sai da ta kira ni a waya yanzu na sani tana gaya mini sun shirya tsaf yanzu za su taho su uku ita da Babanmu da kuma Ummansu Hadiza.
Na ce kawai su bari idan mun dawo sai su zo gidan Hajja tunda nasan lallai nan za mu zauna kafin ya sake warware mu koma abuja.
Na yi mata cikakken bayani sosai yadda za ta fahimta tunda Allah ya tashe shi to sau'ki ya zo ga kowa Kamalu ma ya ce mini suna so su zo hana su zuwa na yi na ce su bari gobe za mu dawo gabad'aya.
Yinin ranar ana ta shige da fice d'akin malamin yau ya lamuncewa kowa tun daga kan matansa 'ya'yansa duka da surukansa babu wanda bai shiga ya duba shi ba.
Da yamma na nemi Sukairaju domin mun yi waya da Hamusu cewa ya gama had'a mini komai saboda na sau'kaka masa tafiya nace ya bari Sukairaju ya zo ya kar'ba tunda shi da mota a hannunsa.
Tsakanin k'waryar birnin kano da k'auye bunkure bai zai wuce awa daya da rabi zuwa biyu ba.
Misalin biyar na yamma ya kama hanya ya tafi bayan magriba da kad'an ya dawo da sa'kon.
Duk abinda na umarci Hamusu ya yi mini yakan yi kokarin yin iyakacin bakin kokarinsa kamar yadda na buk'ata din shadda ce kalar sararin samaniya dakakkiya zanenta irin na manyan mutane dinkin ma fitacce ne da hula zannar bukkar ta karshen tsada da takalmi daidai kafarsa maigidantsaya kamar dai yadda na gaya masa ga yadda nake so.
Na ji dad'i sosai bayan isha'i dana nutsu na kira shi a waya ina sake yi masa godiya sai hakan ya bashi dariya da mamaki yana fad'in abinda ya yi bai kai na yi masa wannan godiyar ba nafi karfin haka a wajensa.
Na yi murmushi kawai na kashe wayar cikin zuciyata nake
fadin lallai da matasan samari irin Hamsu za su zama masu tsoron Allah da Amana da an rage masu zaman banza.
Hamusu tun kafin na kai k'arfin haka yake tsaye akan dukiyata ban ta'ba kama shi da zamba cikin aminci ba ko ya danne mini kudi duk shekara muke buga lissafi a fitar da abinda aka zuba a fitar da ribar da aka samu a biya duk wanda yake da hakki hakkinsa.
Yanzu da su Kamalu suka koma can al'amarin sai ya kara bunkusa Hamusu na kula da shagon zannuwa da ma'aikatan da suke yi mana d'inki shi kuma Usaini na kula da shagon da muke harkar huluna kala daban daban.
Yayin da muka bude sabon shagon sayar da takalma cikin kasuwar kwari wanda Yusi da Saminu suke kula da shi Kamalu kuma hankalinsa ya fi karkata wajan yawon neman sani akan abinda ya shafi da'awa da hadisai Annabi s'aw shikkenan yawon bin malam sunnah yana kuma zuwa legal kwalejin addinin musulunci.
Cikin matan gidan na zauna kamar jiyya muna ta hira sosai suna ba ni sha'awa ganin yadda suke gudanar da rayuwarsu a sau'kake ba kuma su zafafa kishi ainun irin na wasu matan k'auyen ba.
Kayan suna kusa da ni Malam Rabiu yana shigowa na sanya Hajara ta yi mini magana da shi kafin ya shiga bangaransa ya zo muka gaisa sannan na bashi kayan tare da gaya masa na Yallabai ne.
Bai jima ba a wurinsa ba kuwa ya fito da kayan a hannunnsa ya nufi sashen malamin da d'an sauri.
A daran ranar na yi bacci sosai irin wanda na kwana biyu ban yi shi ba hakan kuwa baya rasa nasaba da nutsuwar da na samu da asuba da na yi sallah ban koma ba.
Gari yana yin haske Hajara ta shigo da abin kari da kuma kayan makarantar boko a jikinta litiinin ce dama muka gaisa ta ce Inno ta dora mini ruwan wanka ita zata tafi makaranta.
Na ce ." To na gode sosai Hajara sai dai za mu tafi baki nan kina makaranta ko?"
tana murmushi ta ce." Eh shiyasa na shigo mu yi sallama wata'kila kafin na dawo kun tafi Allah ya tsare ya kiyaye hanya."
Na amsa da Amin Ya Allah.
Har ta juya zata fita na kirata ta dawo na ce." Ajinki nawa ne?'' ta ce." Aji na uku a sakandire."
Na gyad'a kaina jakata da take saman katifar dake shimfide a d'akin na d'auka ina da kudi a ciki dubu biyar na mik'a mata ta nok'e wai ba zata kar'ba ba tana dariya ta juya zata fita na tashi da sauri na ri'ke hijabinta jakarta ta makaranta na saka kudin ni ma ina dariya na ce" Ki dinga sayan aya da rake a makaranta na gode sosai kin ji, Allah Ya ba ki miji nagari."
Ta amsa da Amin tana jin kunya ta fita da sauri.
Sai da na karya tukkuna na yi wanka na shirya tsaf na fita domin gaisawa da matan gidan da kuma bankawana.
Malam Rabi'u ya zo yana gaya mini Malam na kira na.
Na bi bayansa cikin nutsuwa dama kuma da hijabina a jikina.
littafin nan na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Koda na shiga d'akin alamu ya nuna mini tare suka yi karin kummalo da malamin domin kayan karin na gani a gabansu sun gama suna magana.
A nutse na zauna gefe d'aya na dubi malamin na gaishe shi ya amsa da kulawa kafin na juya shi ma na gaishe shi muka had'a ido.
Sosai ya yi mini kyau cikin kayan ya yi fes dashi kamar sabon ango duk da shi din ma'abocin gayu da tsafta ne amma sai nake ganin yau ya fiye mini koyaushe kyau da kwarjini.
Na ce." Baba ina kwana ya jikin." Ya amsa da sauki alhmdullhi."
Na janye idona daga kansa don ganin shi bashi da niyyar janye nasa wasu lukutan idan yana yi mini irin wannan kallon nakan ji nauyi da kunya akan kaina balle kuma da mutane a wurin.
Cikin nutsuwa ya fara yi mini bayanin rubutu da daurikan magungu
an da suke gabansa.
Rubutun cikin wata jarka ne yayin da daurikan maganin ya kasance uku daya asha da zuma kullum da safe daya kuma a tsiyayi rubutun kofi daya a zuba karamin cokali sai ya sha idan zai kwanta. dayan kuma a ruwan wankansa za a zuba duka tsayin sati hud'u.
Ya sake d'auko wata madaidaiciyar jarka itama cike da rubutu shi kuma kullum da daddare idan zai kwanta za a shafe masa jikinsa da shi.
Sosai ya yi mini bayani ya kuma ce mini na kula kada a tsallake rana d'aya.
Godiya da ni dashi muka dinga yi wa malamin har sai da ya dakatar damu yana dubansa ya ce." Har yanzu a matsayin uba nake a wurinka shin ko ka manta ala'ka da dangantakar da take tsakanina da mahaifinka.
Godiyata ga Allah da Ya sanya ina raye wannan kaddara ta same ka.
Allah Ya lamunce mini da taimakonsa aka samu mafita don haka tsakanina da kai babu godiya Tajuden yadda zan tsaya akan matsalar yarana hakan nan zan tsaya akan matsalar yaran abokan k'uruciyata."
Wannan kalaminsa ya kashe mana jiki gabad'aya muka yi sallama da shi muka fito
Wannan karon ma ya tsaya tsakiyar tsakargidan kamar wancen lokacin da za mu tafi yana yi wa iyalin malamin sallama.
Na shiga d'akin na fito da 'yar akwatina ina fad'in." Mun gode sosai Allah Ya saka da alheri Allah Ya biya ku da aljanna."
Gabad'aya suka dinga amsawa suna yi mana fatan alheri kamar koyaushe ya riga ni fita na bi bayansa Inno har bakin soro na farko ta rako ni tana fad'in." Allah Ya tsare ya kuma kiyaye hanya Hajiya Amina."
Yaransa suna jikin mota a tsaye sai suka ba ni tausayi ganinsu a jeme kwana biyar da tufafi daya a jikinsu ko sun yi wanka shi suke yi mayarwa abin ya ba ni tausayi ainun.
Amma kuma kallo daya za ka yi musu ka ga annashuwa da farinciki a fuskokinsu sai washe baki suke yi suna sallama da Malam Rabi'u da ya biyo bayanmu.
Sukairaju ya bud'e masa motar amma bai shiga ba ya tsaya suna magana da Rabi'un ganin haka ya sanya ni shiga na zauna kimanin minti biyar ya shigo da Bismillah a fuskarsa.
Ajiyar zuciya na sauke bayan mun hau titi na dan lumshe idona ina ambaton sunan Allah Ubangiji Allah kada ka kara maimaita mini wannan tashin hankalin da shiga.
Har muka isa gidan Hajja bai fi sau hud'u muka yi magana ba dalili akwai yaran shi don Sukairaju ma yana daf da shi shiyasa ya kama kansa ya dai gaya mini cewa shi ya hana su Ha
jja zuwa ayau din ita a yadda ta so su zo sai mu sake juyawa tare.
Kawunansa biyu muka samu a gidan Hajja Alhaji Sa'idu da Alhaji Haruna wanda shi baya gari ma al'amuran suka faru sai da ya dawo tukkuna ya samu labari.
sai kuma Inna Uwani ita kad'ai ce ban ga Hauwa ba sai 'yar uwarsa Hajiya Saratu.