← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 276

Sashe 116

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tubarkala ma sha Allah shine abinda kowa yake fad'a a kansu domin kuwa yadda Allah ya gina musu jiki da lafiya tun a ciki ba wanda zai d'auka cewa 'yan tagwayene dalili wasu akan haifesu da rashin lafiya irin ta jarirai ko yan'kwanewa da yamushewar fata, su kam kalau suka fito cikin mahaifa daya kamar kuma an tsaga kara babu ita inda suka yi bambanci.

Tunda aka haifesu ake ta hasashen da wa suke kama wasu suce da ni, wasu kuma su ce da babansu.

Ita Hajja ma cewa ta yi da inna Uwani suke kama mai gabad'aya kenan.

Jin haka ya sanya ina Uwani kasa rufe bakinta daga zarar an yi magana sai ta ce ai da ita suke kama.

Can dangin Hajja suka kwaso domin ni kaina basa kama da ni balle kuma Babansu Hajja ta ce suna kama da inna Uwani shi kuma ya ce da Samira suke kama matarsa ta farko.

Ni dai dariya kawai nake yi musu domin ba ni da ta cewa ganin yaran daidai da yatsuna ba su d'auko ba.

Umara ya tafi a tsakankanin haihuwar ya je ya nuna godiyarsa ga Allah subahanawu-wata'ala.

Satinsa daya ya dawo ya ce zai shirya walima domin sake nuna godiyarsa ga kyautar da Allah ya yi masa.

Ban so ba saboda ba na so abinda zai kawo rud'ani a zamanmu na ce masa lokacin da aka yi masa haihuwar fari ma bai yi ba sai yanzu ya kamata ya bar shi kawai umarar ma da ya yi ta isa.

Fad'in haka ashe lefine a wurinsa yana fad'a na kyaleshi ya yi yadda yake so kudinsa ne kuma yaransa ne ba zan tsara masa abinda zai yi ba, Yana da kyau ya nunawa Ubangiji godiyarsa ta sigogi da yawa tunda Allah Ya yassare masa to babu ruwana idone nawa.....

Humm
Mu je zuwa dai.

Tsugonan ta kare ko bata 'kare.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.

Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*77*
Rabuwa na yi dashi kawai na daina mayar masa da martani ganin iyayensa Hajja da inna Uwani a gidan, kuma daidai gwargwado suna nuna mini kulawa da kara tare da yin tiriri da yaran mussaman inna Uwani da motsi kad'an idan ana maganar kammanin yaran take amshewa tare da tabbatar da cewa da ita suke yin kama.

Dukkaninsu daga ita har Hauwan na kasa fahimtar menene a can kasan zuciyarsu domin duk yadda na kai ga so lallai sai na hango cewa abinda suke yi mini ba don Allah ba ne na kasa sun 'boye sosai kuma ko da da wani kulli a ransu ba su nuna ba, amma zahiri Hauwa ta yi kyan kai da ta iya jimirin kawar da kanta daga jin haushin d'igimin da ya d'auka adalalin samuwar yaran, don gabad'aya tunda aka yi haihuwar ya rasa sukuni haka zalika mu ma haka don motsi kad'an za a yi zai ce ba a yi masa daidai ba ko kuma wata daga ciki ta yi kuka ko yana sama idan ya ji sai ya sauko Yana tambayar dalili har kunya da nauyi nake ji wani lokacin domin inna Uwani ce take dauwaniya da su Hajja tana dan taimaka mata kadan.

Gefe guda kuma Hauwa na hidimar d'orawa da saukewa yini take yi a kicin saboda ba mu da mai aiki mace sai maza, na dai kudire a raina duk lokacin da na je kano to kafata kafar baba Tabawa
Sannan ni kaina Hauwa hidima take yi mini ta fannin abinci ga maigidan da tsofffin iyayenta.

Lokacin da ya dinga fad'a akan me zan hana shi yin abinda yake so sai da iyayensa suka ji 'kananun maganganun da yake yi sai nema yake yi ya mayar da abin rigima da na gaji kawai sai na rushe da kukan b'akinciki ya ina cikin d'aita da rintsin haihuwa a sanya ni a gaba da tijara, kawai saboda na ce kada a yi walima shine lefi da fad'in bakaken maganganu.

Hajja da inna Uwani suka shiga maganar.

Akan na rabu dashi ya yi ai abin alheri ne a tara mutane a ciyar dasu a kuma yi addu'a, dama walima aka sani a tsarin addinin musulunci ba wani abin ba ne.

Ganin yadda ya samu goyan bayansu akan hakan ya sanya ban sake wata magana ba, sai da muka yi kwana biyu ba mu yi magana ba sannan muka shirya don shine ma ya dinga neman shirin ganin da mutane a gidan na kula shi domin kada suga kamar ina da mugun hali.

Amma ba wani ya'ke masa baki nake yi ba don mugun haushinsa nake ji akan abinda ya yi mini.

Amaryarsa Momi akwati biyu ta yi da kaya kowacce shake wai Hassana daya usaina ma d'aya.

Wallahi rasa bakin magana na yi a lokacin da na bude kayan ina dubawa.

Da yake duk a gabansu ne Hauwa har tana cewa kada matar nan ta rusa jarinta akan yi wa 'ya'yan miji gwaninta.

Ina dariya na ce ko daya tunda ki ka ga tana irin wannan kyautar ta yi nisa ne wata'kila yadda kike d'aukarta ta wuce haka.

Hajja ta ce kuma ma dai mai son yi ce domin wasu akan su bayar sun gwammace wuta ta cinye domin Ubangiji yana duba duk wanda ya azurta baya fitar da kazantar dake cikin dukiyarsa da kansa zai fita ta hanyar tashin gobara ko ta wata sigar ta daban.

Ta nisa kafin ta cigaba da cewa mijinku shi yake gaya mini cewa har gidan marayu ne da ita a can garinsu jos din tana d'aukar nauyinsu bayan makarantu da massalatai da ta gina duka hobbsi ga tsohon mijinta da ya rasu.

Wannan dalilin ya sanya ni jin kaunarta a cikin raina domin kuwa macace ta gari, ina kara horarku ku zauna lafiya da ita, kuma kada ku dauketa a matsayin kishi sai yayarku domin ta girmeku ku muntata da kyau.

Sosai jikina ya kara yin sanyi da sha'anin matar wato mutane suna daukarwar kansu zunubi a duk lokacin da suke munana zato akan mutum alhalin ba su da sheda kawai zargi suke yi da k'age.

Sai na tuna irin maganganun da Sahura ta dinga fad'i a kanta a lokacin auransu da maigidan ya zama dole kuwa Sahura ta yi nemi gafarar Allah domin kuwa ta yanke hukunci akan abinda ba ta ta'ba ga ni ba.

To walima ta kyau sosai, kuma ta samu halartar manyar mutane malamai da ma'aikatan gwamnati har ma da 'yan siyasa.

Sahura ta samu zuwa itama yan gidanmu kuwa Babanmu ya samu halarta tare da Baba Sule sai anti Sakina da Fati.

Anti Yagana da Yafalmata sun zo Baban Saude kuma a lokacin baya gari sai da ya kira ni a waya ya yi mini barka ya kuma kira maigidan shima ya yi masa barka.

Hamusu ma ba a bar shi a baya ba ya zo shi kadai Amma domin da ya gaya mini za su zo tare da Gwaggo na ce masa a a saboda tafiyar mota ce Kuma bata da lafiya sosai na yi alkawarin idan na yi arba'in da kaina zan kai mata yaran ta sanya musu albarka.

An yi hidima sosai yara sun samu alheri irin wanda ba zai misaltuba hotonsu kuwa yana ta yawo a kafafen sadarwa tare da yayansu Khalil da ya yi wayo har yana gudu da kafafunshi.

A daran ranar gajiya ta kayar da ni, ana yin sallar magriba da kad'an baccin gajiya ya kwashe ni.

Maganarsa ce ta tashe ni na bude ido Ina kallonsa yana tsaye sai kuma ya zauna a gefana na tashi zaune ina d'an hade jikina tare da d'an matsawa.

A tak'aice na ce." Ina yini." Ya amsa cikin kulawa yana ta kallona har na tsargu.

Na ce." Wani abu ne ya faru?"
Ya girgiza kansa a tsanake ya furta." Na gode mini giwar gidana."
Murmushi na yi wanda babu nisha'di a cikinsa na ce." Godiyar ta mecece?"
Ya fito da wayarsa hotonan yaran yake kallo yana murmushi kafin ya nuna mini na kalla ban ce komai ba.

Sai na ji ya ce." Kin biya ni Amina, na kuma yafe miki abinda ki ka yi mini abaya." Ya nisa kafin fuskarsa ta sake yalwata da annashuwa ya furta." Da ki ka tashi ba ni yara sai ki ka ba ni biyu kuma masu kama da Samira Amina na gode, na gode wallahi idan na kalli yaran nan ina jin wani irin farinciki mara misaltuwa."
Don Allah kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Sosai na iya danne tsaki da harshe da gand'ar bakina ke ko'karin furzarawa.

Na ce." Na farko dai ba ni za ka yi wa godiya ba Allah za ka godewa domin shine ya baka ba Amina ba.

To ai yanzu ka fadi dalilin da ya sanya ka dimaucewa akan yaran bawai a karan kanka ba ne, a a saboda suna kama da wata can daban.

Hakan bai dame ni ba dama hausawa sun ce kyan d'a ya gaji ubansa, ka daina gode mini ka godewa Allah ko ka je ka tashi Samiran daga kabarinta ka ce kana yi mata godiya dalili yaranka sun yi kama da ita." Tunda na fara maganar ban tsahirta ba sai da na dire tukkuna tsakin da nake ta dankwafewa sai da na furzar dashi domin idan bai fita ba akwai matsala, na koma na kwanta abina.

Ya jima yana kallona da yanayi na mamaki da takaici kafin ya ce.'' Yanzu ina Samiran take Amina?"
Na ce." Oho!

Sai ya gyad'a kansa ya tashi yana fad'in." Ni ba zan yi rigima dake ba domin na gane so kike ki tsinka ni a cikin mutane don haka ki huta lafiya." Ya juya da niyyar fita.
Chapter 116 · 0% Book details