← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 276

Sashe 151

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idona na zare musu sosai na ce." Tsayuwar ta mecece idan ba za ku gaishemu ba to ku daina kallonmu, ko mun yi kama da tibi ne.''
Matashiyar mai aikin da take jigila da su tana dariya ta furta." Ke Hassana ku zo ku gaisa Mama ce fa."
Na ce." A'a rabu da ita kada ta zo mu gaisa ta tsaya." Usaina ta fito daga kicin da shafceciyar wuk'a a hannunta tana fad'in." Mairo ga wukar ki yanka mana." Shiru ta yi tana kallonmu yayin da mai aikin ta je ta da sauri ta kar'bi wukar tana fad'in." A can sama fa na d'orata yanzu Usai sai da ki ka d'aukota."
Ba ta ce mata komai ba ta nufo wurin da muke zaune tana zuwa sai ta dora kanta a cinyata tare da zura yatsanta babba a baki tana tsotsa.

Na yi shiru ina sauke ajiyar zuciya yayin da na d'ora hannuna a saman kanta.

Ganin haka ya sanya Hassana da sauri itama ta zo ta yi yadda Usainar ta yi dama tuntuni Kamalu ya gaya mini kishi ne da su, duk abinda daya tayi to babu shakka yar uwata ma sai ta yi.

Da hannu na yi wa Minal alama ta zo wurina.

Ta kuwa taho kataf-kataf domin yanzu itace take tashen ki'ba a cikinsu.

Na ri'keta sosai Ina fad'in." Ina Khalil yake?" Cikin yanayin maganarta ta furta." yana can gidan anti Nusaiba."
Baba Tabawa sai murmushi take yi tana jan su da wasa.

Hassana da Usaina iyayen miskilanci ne, Minal din ta fi su sakin fuska da son mutane.

Tunda suka dora kawunansu saman cinyata babu wadda ta dago sai da suka ji muryar Babansu tukkuna.

Tare suka fito da Momin kallo daya na yi mata gabobin jikina suka shika wata irin rama ta yi mai ban tsoro kanta yana nema ya rinjayi gangar jikinta abinka dama da siririya idanuwanta sun yi kuru-kuru ta d'ashe k'warai da gaske ta yi fau, babu shakka babu k'arya a cikin lalurarta yadda mijinta ya dinga jadadda ciwon ya ci karfinta yanzu na sake gazgata kammaninta duka sun canza ta hadu da ciwuka masu hatsarin gaske sugar da hawan jini.

Ta zauna tare da taimakonsa suka zauna kujera d'aya yana dan gyara mata 'kafafunta ko daga inda nake zaune Ina kallon yadda jikinta yake rawa.

Ban ji haushinsa ba ko kad'an domin a yanzu dai babu maganar kishi ga matar da take cikin irin wannan yanayin na halin ciwo mai tsanani.

Ta dinga fara'a a zahiri tana nuna jin dadinta.

Muka gaisa cikin kulawa da mutunci.

Na yi mata sannu da jiki haka zalika ma baba Tabawa ta dubata sosai.

Ta dinga dariya ganin yadda twin's suka yi mini farincikinta ya kasa 'boyuwa ta ce." Ai maigidan yake gaya mini ba ku ji labarin na kwanta a asibiti ba, ku yi hakuri don Allah da yake ni kaina lokacin ba ni hayyacina sai da na kwana na yini tukkuna na fara gane wanda yake kaina.

Ko da na tambayi Nusaiba da Nabila shin an sanar daku suka ce mini eh sun sanar daku halin da ake ciki, na gode sosai Amina Allah Ya bar zumunci."
Cikin nutsuwa da kulawa na ce." Allah Ya sawwa'ke yasa kaffara ne amma maganar gaskiya babu wanda ya gaya mana cewa baki da lafiya balle mu ji cewa kin kwanta a asibiti na tsayin wannan kwanakin." Na yi shiru Ina mayar da numfashi kafin na cigaba da cewa." Tabbas da mun sani me zai hana mu zuwa asibiti mu duba ki, babu niyyar wulakanci ko kuma nuna wariya a tsakaninmu dake kuma ciwo ake ce kin ga kuwa lalura ta kori komai, Ubangiji Allah Ya sawwa'ke, Hauwa ta ce a duba ki da kyau kuma tana yi miki sannu da jiki itama kwana biyu da yake ta yi nauyi sosai ba ta jin dad'i ne."
Yanayinta ya nuna alhini da damuwa a zahiri abinda ta nuna kenan.

Sai ta gyad'a kanta a hankali ta ce." Babu komai Amina komai ya wuce kuma na ji sau'ki sosai wallahi sai dai rashin 'kwarin jikin da yake d'an damuna yanzu, a cewa da Hauwa ina amsawa Allah Ya raba lafiya."
Na ce." Za ta ji in sha Allahu rabbi."
Tun kafin mu yi sallama take yi mini godiya har sai da jikina ya mutu tsabar tausayin halin da take ciki.

Mairo ita ta janye yaran ta tafi dasu tana yayyanka masu mangwaron da tun farkon shigowarmu suke he rigima a kansa....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *2k ON TALGRAM*
*VIA 0542382124...

BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
*V-VIP AREWAPEN*
*Wsp Gruop 1k*
*103*
Duk abinda muke yi bai ce mana komai ba, mun dai gaisa amma tun bayan gaisuwar bai sake magana ba, sa'i da lokaci dai yakan amsa waya idan an kira shi.

Misalin takwas da wani abu muka fito daga gidan tun a hanya muke alhinin yanayin da muka risketa Baba Tabawa dai kasa daurewa ta yi a hanyarmu ta shiga gida ta fashe da kuka da sauri tasa gefan jihabinta ta rufe fuskarta .

To ni ma dai kukan zucci nake yi domin na shiga rud'ani ba karami ba ganin yadda Allah Ya mayar da baiwarsa.

Idan kudi na sayan lafiya nasan da ba wannan maganar ake yi ba.

Wannan da duniya ta yi mata sheda cewa mutuniyar kirki ce wadda tun a duniya mijinta ya ce ya yafe mata itace cikin irin wannan yanayi to ina ga wanda ya shure umarnin Ubangiji kuma, Ubangiji Allah kasa mu dace Amin.

A haka muka shiga gidan Hauwa na kwance saman kujera 3str tana kallo abinta.

Ganinmu sukuku ya sanya ta tashi zaune tana tambayar lafiya.

A takaice na ce." Lafiya lau." Na shige d'aki domin yadda kafafuna ke rawa ba zan iya tsayuwa a wurin ba.

Na zauna gefan gado tare da rafka tagumi wani abu ne ya zo ya tsaya mini a wuya na tsananin fargaba da tashin hankali mace ta koma sai kace mai cutar kanjamau! ko mai farfadiya sai an rirriketa.

Hawaye suka fara sauka a kumatuna.

Haka kawai na ji duniyar ta fice mini daga raina gabad'aya.

Shigowarta ya sanya na daga kaina na dube ta.

Ta zauna gefana babu babu fallasa ta ce." Ashe kema kukan ki ke yi Amina." Sai ta sa dariya kafin ta cigaba da cewa." ga Baba Tabawa can ma tana yin nata, ni kam matar nan ko dame take yawo wallahil-azim kurwata tafi tata d'aci, wallahi ni zan yi maganinta."
Na gyada kaina ina ko'karin ture kutittiran abinda ya tsaya mini a wuya na ce." Hauwa k'ullaci da tsananta gaba da k'iyayya wallahi babu inda zai kai ki sai tashar dana sani.

Matar nan dai duk rashin Imanin mutum ya ga halin da take ciki sai ya tausayata mata don Allah mu dinga sassautawa kanmu Hauwa."
Ta ja tsaki tare da furta."lalura fa kowa yin ta yake yi, wallahi na fita jin jiki, ni mai yasa ban lanjare ba, saboda ba ni da hakkin kowa a kaina, ita kuwa bari na gaya miki abinda ta shuka ne take girba tun a duniya hakkin mutane ne wallahi."
Na jima ina kallonta tare da auna maganganunta.

Yadda take tabbatar da abinda ba ta da tabbas akai shine abinda ya fi daga mini hankali da lamarinta.

Wace irin kiyayyace wannan.

A ganina wannan abin da take yi jahilci ne tsantsa da rashin sanin abinda ya dace.

To ba ni da bakin magana domin kuwa yadda ta yi nisa irin haka babu wani kalami da zan yi mata ya sanya ta sassauto daga irin kiyayyar da take yi wa matar nan wadda alherenta suke dabaibaye damu bakidaya.

Ganin ban ce mata komai ba ya sanya ta tashi tana fad'in." Matsantawa kai ne kawai kowa ya kashe wutar gabansa.

Shi kuma ai hakkin rai tun a duniya Ubangiji yake fitar da shi wallahi tallahi yanzu ta fara gani.

Sai kawai na saki bakina ina kallonta har ta fice daga d'akin ban d'auke idona ba.

Na jima a zaune Ina tufkewa da warwarewa kafin na tashi jiki a sabule na shiga bandaki domin watsa ruwa a jikina.

Gabad'aya cikina ya cushe babu dandano a bakina ko kad'an yunwar ma sam ba na jin ta, daga zarar na tuna halin da muka riski matar nan a ciki sai hankalina ya tashi.

A haka na shirya cikin kayan bacci ina tsaye gaban madubi ina busar da gashin kaina.

Ya turo kofar d'akin ya shigo.

Ban yi zaton shigowarsa ba.

Muka had'a Ido ya nufo wurin da nake tsaye daf da ni ya tsaya na gama abinda nake yi yana ta kallona ta madubi na juyo kirjinmu ya hadu waje daya.

Kusan a tare muka sauke ajiyar zuciya.

Ya riko hannuna muka zauna gefan gado.

Yanayin fuskarsa kadai shi ya nuna mini cewar ya ji dadin abinda na yi.

Ya furta." Kin kyauta sosai kuma na ji dadin abinda ki ka yi, idan haka kuke yi mini kara akan abinda nake so mai zai sanya ni ma na 'bata muku ai babu abinda ya fi zaman lafiya dadi ko."
Kanzil ban ce masa ba. amma maganarsa ta d'an dake ni wato shi baya jin nauyin gaya mana irin son da yake yi wa matar nan tasa.

Ya d'ora hannunsa a tudun kirjina wanda tun zaman da muke yi a wurin hankalinsa yake kai.

Ya nisa kafin a kasalance ya furta." Momi ba ta da lafiya Amina cikinta da wajenta wallahi, tausayinta nake ji sosai domin lalurai sun gama dabaibayeta."
A nutse na furta." Allah Ya yaye mata, da sauran al'ummar musulmi."
Ya amsa da Amin kafin ya dora da cewar." Kin san yanzu wani result din ya sake fitowa bayan gwajin da aka yi mata satin da ya wuce cancer bakin mahaifa."
Da saurin gaske na dube shi.
Chapter 151 · 0% Book details