← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 276

Sashe 178

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daf da magriba mun d'an samu sau'ki shige da fice na mutane domin duk wanda ya je can gidanta ya yi gaisuwa sai ya shigo mini mussaman mak'otanmu dama wad'anda muke cikin estate din a tare.

Na shiga d'aki sallah na samu Anti Yagana har ta idar ta kashingida tana fad'in." Gobe ana yin addu'a da safe zan d'auki hanya da wuri Amina."
Na ce" Ba za ki ta ya ni zama ba anti Yagana kina ji su Hajja ma fa gobe suke cewa za su tafi."
Ta furta." Na so hakan Amina Amma hankalina ya yi gida saboda Fadila ban san a wane yanayi take ciki ba tunda an ce har da karin ruwa."
Na ce." Hakane kuma to shikkenan Allah ya kaimu zan gayawa maigidan idan ya shigo in sha Allahu."
Ba tace komai ba.

Na shige band'akin domin d'aura alwalar sallar magriba.

Har bayan isha'i muna tare da anti Yagana a d'aki muna tattauna mas'aloli masu yawa.

Hajja ta shigo d'akin da kanta tana fad'in." Yagana tun safe da ki ka fito mu ka gaisa ki ka auri zaman d'aki ko ba kya jin dadi ne."
Ta mike zaune tana yar dariya kafin tace." Wallahi lafiyata lau Hajja kawai gajiyar tafiya ce bata sake ni ba."
Itama da murmushi da kulawa ta ce." To ku fito mu ci abinci, ke Amina kema tun d'azu nake hankalce dake kowa ya ci abincin rana babu ke, maza ku fito mu had'u mu ci abinci yanzu nan Tabawa ta kammala har ta fito mana dashi."
Na ce." To shikkenan Hajja.''
Anti Yagana ta yi murmushi bayan fitarta daga d'akin tana fad'in."Baiwar Allah nan tana sona Amina, ko da yake k'aunar da take yi miki ne ta shafe ni."
Na ce." K'warai kuwa na sheda soyayyata da Hajja ta daban ce, amma shekarun baya anti Yagana an so a juyar mata da hankali wallahi na d'an fuskanci gizago daga wurinta da na ri'ke addu'a kuma sai abin ya shud'e kamar ba a yi ba."
Ta ce." Muddin baka nufi kowa da sharri ba Amina to ko shi ya nufe ka dashi ba zai yi tasiri ba, addu'ar nan dai da ki ka rike ki ajiye a ranki cewa itace makaminki."
Na ce." In sha Allahu anti Yagana."
Tare muka fito falon duk suna zaune wannan karon Sultan yana hannun gwaggo tana d'an jijjigashi.

Kafin na zauna na ce." Gwaggo yau kece ki ke auran kenan." Tana dariya take fad'in.'' E, ai yau yace da ni yake auran."
Ina Uwani ta yi murmushi tana cewa." An jima kadan zai ce da tsohuwar zuma ake magani ni ce uwargidansa.

Hajja da tunda suke maganar ba ta sanya musu baki ba sai yanzu ta ce." Duk ku gama yin jigila dashi yace ni yake so ko Tabawa." Aka yi dariya gabad'aya cikin raha da barkwanci.

Cikin wannan yanayin ya shigo tare da Kamalu dama a tare nake ganinsu duk lokacin da suka tashi daga kar'bar ta'aziyyar.

Ya tsaya suka gaisa da su Hajja kafin ya haye sama.

Shi kuma Kamalu ya zauna a cikinmu Hajja ta ce Baba Tabawa ta zuba masa abinci.

Saman na bi shi ina shiga d'akin na same shi ringine a gado.

Na k'
rasa na zauna gefan kafafunsa.

Ya tashi zaune yana sauke ajiyar zuciya." Na gaji tubis Amina ga'bobina ciwo suke yi mini wallahi na jima ban yi gajiya irin ta wannan lokacin ba."
Na sauke ajiyar zuciya Ina fad'in." Ya za a yi abu ne da aka asassa shi amma da yawa wasu ba sa yin wannan zaman."
Ya ce." K'warai kuwa gobe idan an yi addu'ar uku zan sanya a cire rumfunan da aka kafa kowa ya tafi kuma haka ya isa ranar bakwai zan sanya masallatai a yi mata addu'a."
Shiru na yi ban ce komai ba.

Gabad'aya tunanina na kan yaranmu.

Amma har yanzu ban ji yace komai ba akansu.

Ba ni son na yi magana ta zama fitina zan d'an jira shi daga nan zuwa ranar da za ta cika kwanaki bakwai duk wacce za mu yi sai mu yi.

Ya yun'kura zai tashi sai ya koma ya zauna.

Na ri'ko hannunsa cikin mamaki ina kallonsa lallai da gaske ya gaji.

Hannunsa da na ri'ke na ji d'umi ba kamar koyaushe ba.

Sai kawai na ta'ba wuyansa zafi rad'au zazza'bi ne.

Na ce." Zazza'bi kake yi fa Baba?"
Ya ce." Zazza'bi ne ko?''
Wai tambaya yake yi.

Na ce." K'warai kuwa zazza'bi ne ya kawo maka sagewar gabobi da ciwon jiki, ya kamata ka samu hutu fa."
Ya sake yun'kurawa a karo na biyu yana fad'in." Bari na yi wanka zan kira likitana yanzu ya duba ni tun wajan sha biyu na rana na ji yanayin jikina ya canza ina dan jin ciwon kai ma."
Na kama hannunsa muka nufi bandakin tare na hada masa ruwan wankan ina fad'in.'" Wankan ma da ka bar shi tunda ka yi da safe.

" Ya ce." Ai ba zan iya bacci ba idan ban yi shi ba Amina, kada ki damu bari na yi na fito ki kawo mini abinci."
Na ce." To a sanyaye na fito na bar shi a toilet din na sau'ka kasa cikin 'yar damuwa ya jima kuwa bai kwanta ciwo ba tun bayan zazzafar murar da ya yi a gidana sakamakon ruwan saman da ya dake shi a shekarun baya.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *Gudun aure paid book. 2k complete on telegram.

What'sappa Gruop 1k Via 0542382124....

Binta Umar gtbank*
*07084653262*
*121*
Lokacin da na koma d'akin bai fito ba na zauna ina jiransa ya fito a rikice da d'ari irin na zazzabin ya sake ninkuwa kaya masu d'an kauri na d'auko masa ya kar'ba yana ko'karin sanyawa ya ce na d'auko masa hular sanyi duk a cikin kayan nasa ina fad'in." Abinda nake ta gudu kenan.

Ya gama sanya kayan jikinsa ya zauna gefan gado cikin yanayi na ciwo da kaina na shafa masa basiline a jikinsa gabad'aya.

Ya sanya hular har ta rufe kunnuwansa.

Kafin na fara zuba masa abincin ya d'auki wayarsa ina jin ya kira likitansa ya yi masa bayani ya bashi tabbacin cewa gashi nan zuwa yanzu.

Cokali biyu ya iya ci na abincin ya dakata.

Gabad'aya ni ma sai na ji zazzabin yana nema ya rufe ni.

Babu zato ba tare da tsammani ba na ji yana fad'in." Kira mini Hauwa a wayarki Amina."
Da mamaki mai yawa nake dubansa.

Ya d'an lumshe idonsa kafin ya bud'e yana gyad'a mini kai.

Ban iya cewa komai ba na tashi a hankali na sauka kasa da nazari a k'wanyata.

To ko dai an daidaitasu ne ban sani ba wata'kila kafin mu fito daga d'aki ni da Sahura mahaifiyarsa ta zauna dashi akan hakan zuciyata ta dinga yi mini sa'ke-sa'ke.

Na koma d'akin na same shi a takure a gado ga blanket din bai rufa ba.

Na zauna tare da rufe masa k'afafunsa har zuwa saman kirjinsa sannan a tsanake na fara neman layin Hauwa.

Bugun farko ta daga ta kama sunana.

Na amsa kafin mu gaisa ban ji ta sake yin gaisuwa ba kawai ta yi shiru sai na daure na ce." Maigidan ne yake son magana dake?"
A yatsine tace." Kamar yaya menene a tsakanina da shi, kuma ai yana da lambata mai ya sanya sai kece za ki kira ni.''
Na danne b'acin ran da nake ji yana taso mini na furta." Haka dai ya ce ni na kira ki Hauwa."
Ta ja siririn tsaki wanda ya yi mini ciwo sosai a rai amma ban katse wayar ba na mik'a masa yana daga kwance don bai tashi ba ya kar'bi wayar yasa a kunnansa.

Sunanta ya kira ta amsa a dakile.

Ya d'an yi jim ban sani ba ko yana jiran gaisuwarta ne ko kuma yana jiran ta yi masa ta'aziyya ko daya dai ba ta yi ba.

Ya furta." Kina lafiya ko?''
"Umm" Ta ce cikin basarwa.

Ya yi shiru na d'an wani lokaci kafin ya furta." Idan kin ji wani canji ko yaya ne a jikinki kada ki yi shiru."
Na yi zugum ina kallonsa da mamaki wai yau Hauwa yake rarrashi har yana fad'in idan ta ji canji na ciwo a jikinta kada ta yi shiru ta sanar da shi.

Duk ina k'iyayyar da yake fadin yana yi mata.

Mamaki ya kasa bari na janye idona daga kansa har sai da suka yi sallama ya miko mini tare da lumshe idonsa.

Na daure ina fad'in." Alhamdulillahi na ji dadin wannan abin da ya faru, Ina fatan Allah Ya sa ya zama na karshe."
Ya yi shiru bai ce mini komai ba.

Ni ma na yi shiru ina d'an duba wayata sai dai can kasan zuciyata wani takaici ne na dinga tunanin daga ina yake ai ni nake so Hauwa ta dawo mu cigaba da zama to mai zai sanya don ya yi waya daya da ita yau na ji haushi idan hakane kuwa gaskiya zuciyata bata kyauta mini ba.

Ban iya tashi na fita daga d'akin ba har sai da likitansa ya zo ya duba shi sosai ya yi masa BF domin yana kuka da ciwon kai sosai jinin
sa ya haura amma ba sosai ba, dama kuma yana da hawan jinin sai dai ba kasafai yake tashi ba sai da damuwa kamar shakarun baya da ya motsa masa lokacin ina amarya yana neman hanyar da zai samu kaina ni kuma na'ki bada fuskar hakan tun zamana na farko Legos kenan a iya sanina tun daga lokacin bai kara motsa masa ba sai yanzu.

Suka yi sallama yana fad'in " Za su tafi da Sukairaju yanzun domin ya bashi magungu
a.

Ya ce mini lallai ya ci abinci sosai kafin ace ya sha maganin.

Da kyar da jibin goshi kamar wani yaro ko d'an yayen da yake rigima ya ci cokali biyar bayan biyun da ya ci da farko yana fad'in bakinsa babu dad'i, ba zai iya ci da yawa ba.

Haka nan na ha'kura na kyale shi tunda iya naci da magiya na yi masa akan ya kara yace a a.

Sukairaju ya kawo magungu
an ya tsaya ya yi masa sannu kafin ya fita.

Na duba kowanne akwai yadda za a ba shi.
Chapter 178 · 0% Book details