Sashe 182
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana shigowa estate din Sukairaju da 'Dahuru suka yi ram da shi Malam Isiyaku ne Malamin Hajiya Maryam da ya zo kar'bar kudinsa kamar yadda aka al'kawaranta masa.
A mota suka zura shi tare da zuge gilashin motar sai ya fara zare ido na k'aduwa da tashin hankali.
Sukairaju ya ce." Maigidanmu ne ya ce mu kai masa kai can gidan hutawarsa za ku tattauna wasu batutuwa ko ba kaine malam Isiyaku ba."
Ya gyad'a kansa da saurin baki ya furta." E, ni ne, Malam Isiyaku."
D'ahuru da yake driving ya ce." To kada ka damu lafiya za ka fito in sha Allahu."
Ya yi shiru yana zazzare Ido.
To ai shi ba haka ake yi da shi ba me yasa za a yi masa kamun kazar kuku magana aka yi akan mai hakki ya fito ya fadi hakkinsa a ganinsa hakan da aka yi masa tozarci ne tunda shi ba 'barawo ba ne.
Gabansa suka dire Malam Isiyaku da tunda suka isa guesthouse din suka sanya shi a tsakiya babu wata hanya da zai samu ya fece..
Suka fita cike da bin umarni.
Ya dube shi a nutse Yana fad'in." Nutsu sosai ka kwantar da hankalinka.
Na buk'aci ke'bewa da kai anan ne saboda muhimmanan batutuwan da zamu tattauna da kai, ai komai yana buk'atar sirri ko."
Ya gyad'a kansa kamar k'adangare kana ganinsa za ka gane a tsorace yake ko ina aljanun nasa suke oho.
Wato ashe duk karyar banza ce."
Ya gyara zamansa a gabansa kamar wani mai d'aukar darasi ba malamin da yake da 'kumaji da dulmiyar da al'ummar annabi ba."
Ya ce.'' Tun sanda ka ba ni labarin abinda yake tsakaninka da Maryam mai rasuwa na gaza samun nutsuwa da kwanciyar hankali, a takaice nake sanar da kai har ciwo na kwanta saboda tsananin tashin hankali da damuwa.
Malam Isiyaku shin za ka gaya mini irin bak'aken ayyukan da aka yi wa Maryam domin zalinci.
Kada ka kuskura ka 'boye mini komai nasan ni ma da nake zaune nan a gabanka ka yi aikina ai asiri da tsafi gaskiya ne tunda ya ci annabinmu fad'in gaskiya shine abinda zai k'waceka bayan haka kuma ina so muje da ni da kai a gabana duk inda kayi binne a kaina ko akan wani na ka tone shi da hannunka."
Ya ki'dime sosai da sosai ya kasa zama Yana fad'in." Yallabai Wani aikin kaikayi ne wallahi idan na karya shi zai dawo kaina, zan iya kwanciya ciwo ko abin ya shafi iyalina don girman Allah ka gafarce ni."
Ya dube shi cike da tsantsar mamaki ya ce." Abin zalinci ne kenan, me yasa gabad'ayanku baku da imani ne, kai kanka kana gudun kada abinda ka yi ya shafi iyalinka to me yasa ka yi.
Okey shikkenan tunda duk ina da bayanai a kan ka zan had'a ka da hukuma su za su yi maka tonan asiri duniya ta sheda wannan rawanin daka nad'a a kanka na zalinci ne furfurar dake gemunka kuma ta banza ce, daga nan 'yayanka da kake gudun su damu lahani su yi tur da kai da nadamar fitowa daga tsatsonka."
Ya ce." Duk ba za mu kai ga haka ba ranka ya dad'e za mu je duk inda na yi haka da binne a kanka zan tone da hannuna in sha Allahu ko da hakan zai zama barazana ga rayuwata."
Ya gyad'a kansa yana kallonsa cikin nazari kafin ya ce." Maryam ta yi aiki a kaina da iyalina kenan.''
Ya rusanar da kansa yana fad'in." K'warai kuwa na yi mata aiki akanka da kuma tsohon mijinta Alhaji Amadu akwai wanda na yi binne a kasan bishiyar kuka akwai wanda na yi a bishiyar tsamiya da kuma d'aurin baki da aka yi maka shima yana can za mu je ka gani domin laya ce aka 'dora mata gungumen dutse a can cikin wani daji.......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *Gudun aure paid book 2k complete on telegram what'sapp Gruop 1k via 0542382124......
Binta Umar gtbank*
*07084653262*
*123*
Wato a duk lokacin da Ubangiji ya so bawansa da rahama ya kan wanke shi ya daidaita tunani da tafarkinsa zuwa hanyar tsira ya kuma yafe dukkunanin kuraransa.
Allah," Ya ce kada ku hada ni da wani bawa na wurin neman biyan buk'ata ni ne da Ubangijin talikai mai jin kai, mai kuma bayarwa da hanawa.
Ni ne d'aya wanda ba ni da farko da kuma k'arshe.
Ku ro'ke ni da kowane irin yare ina jinku zan kuma amsa muku.
Had'a Ubangiji da waninsa babban zunubi ne da yake tabbatar da cewa babu afuwa da yafiya daga wajensa.
Domin Allah yakan iya yafe kowane irin zunubi ne mutukar bawa ya yi tabbaccen tuba.
'Kwarai da gaske ya girgiza ya kuma shiga razani da nadamar rayuwa a lokacin da suka dinga haurawa kan dutse tare da Malam Isiyaku da yaransa biyu Sukairaju da D'ahuru.
Duk gwagwarmayar rayuwar da ya yi ta duniya k'afarsa bata zuwa ire iren wannan wurin ba.
Karamin gari ne a cikin jos din kuma mafi akasarinsu maguzawane.
A wannan 'kauyen da mahukunta suka manta dashi nan Malam Isiyaku ke zuwa ya gudanar da ayyukansa.
Tunda a bayan gari yake kuma gari ne da ba su san menene addini ba.
Suka dinga tsallake koguna da dutsina suna wuce manyan bishiyun kuka masu tsananin firgitarwa da bada tsoro.
Wata narkekiyar bishiyar kuka suka nufi mai manyan koguna kuma babu ganye a jikinta.
Suka tsaye gabad'aya wurin tsit sai kukan tsinye-tsinye ne ke tashi.
Da alama bishiyar ta zama sansani wurin ajiye kayan asiri domin ga layu nan birjiki wasu a cikin kwalabe wasu kuma an nad'e su da jan zare da kwalaban tururukan da iska ke so.
Ya tsuguna ya fara wasu zantuka kimanin minti goma ya gama can daga gefe ya fara hak'a da zurfi sosai ya d'auko wata doguwar kwalba da ta fara rinewa cikinta cike da allurai da bakin yadi mai kama da likkafani a ciki.
Daga 'kasan wurin da ya yi hak'an ya cire yadin likkafani shima ya dan rine da kasar wajan Amma hakan bai hana ganin sa'kandamin da yake zane ba.
Ya taso da kayan a hannunsa yana fad'in." Na ha'ko nan."
Ya tambaye shi nasa ne ko na Alhaji Amadu.
Cike da nadama da tsoron abinda zai biyo baya ya ce." Na ka ne Yallabai."
Ya ce ya warware a wurin.
Sukairaju da ba shi da tsoro ya kar'bi likkafanin da sa'kandamin yake hannunsa suka fara dubuwa.
Zanen hotonsa ne tsaf kowace ga'ba da kusurwa ta jikinsa rubuce da sunan Allah da kuma wani irin jagwalgwalon rubutu mai
ri'ke ta kwakwalwa.
Abin mamaki yadin likkafin yana ta 'kamshin wani irin turare mai masifar karfi.
Ya dube shi yana fad'in." Menene makarin aikin."
Ya ce." An karya ai tunda an ha'ko."
Suka yi gaba bishiyar tsamiya ce itama turgijejeya kana kallon wannan bishiyasa zaka tan ta tara 'kwan'kwamai masu illa gashinan ma da kanta take kamawa da wuta tsabar sansanin bak'aken aljanune.
Itama dai kamar daya bishiyar kukan aikin mutane ne birjik a k'asanta da sassan reshenta tunda akwai ragowar ganye a jikinta ga layu nan murtuka murtuka suna ta reto wasu daban wasu a cikin kwalabe."
Ya shiga mamaki sosai da ya ga ya d'ane bishiyasar can k'ololuwa ya kamo wani reshe ya d'auko wata doguwar kwalba da aka d'aureta sosai a jikin reshen an nannad'eta da jan yadi ya daddafo ya sauko da ita a hannunsa.
Sukairaju ya mika masa babbar rigarsa yasa yana fad'in." Wannan shine na alhaj Amadu mai rasuwa."
Ya buda kwalbar a wurin ta fashe.
Layu k'ananu ne soke da allurai suka fito da wani irin warin turare mai gigitarwa..
A wurin ya sanya shi ya warware layun gabad'aya sunan Allah ne gashinan muraran Maliki yaumiddin mimun din da sunan Alhaji Amadu da Hajiya Ayya babarsa da kuma mahaifinsa.
Duk ya warware guda ukun.
Ya bawa Sukairaju umarnin tattarawa ya zuba a leda domin babu damar barin su a wurin da sunan Ubangiji.
Suka yi gaba sosai suka riski wani shuri zungurere ya tsaya a sanyaye yana fad'in" Sati uku da suka wuce na zo na yi aikin wata mata a nan itama akan abokiyar zamanta ne farra'ku zan cire." Ya fad'a a sanyaye da alamar nadama a tare da shi.
Suka tsaya kuwa ya tsuguna ga rana ta kwalle a wurin tururuwai masu yawa sun fito har suna bin kafafunsu.
Ko alama bai sare ba, kuma bai tsorota duk da akwai razanarwa saboda ya san jahadi ya yi shiyasa ya fi yarda su je ya gani da idonsa domin tabbatar da duk ya warware kullin da ya yi."
Ya haka gefen shurin inda ya san ya yi ajiyar ya d'auko wata yar tukunya ta 'kasa nan nad'e da likkafani ya kwance layu ne uku masu kauri ya warware cikinsu gashi ne da barkono tsidigu a hade da kuma d'anyan nama wanda kwance layun ke da wuya wari ya game hancinsu.
Daga kansa ya yi musu bayani cewar naman na ja'ba ne sai gashin matar da aka yi wa asirin tsidigun (barkono) kuma shi zai dinga zafafawa ma'auratan zuciyoyinsu su ji sun tsani kansu da zama da juna.
Suka gama da wannan suka sake nausawa sosai wannan karon tafiyar da suka yi tafi ta baya can suka riski murgujejen dutsan.
Suka tsaya cikin ransa yana raya da wannan aka danne masa baki kenan.
Gudun aure paid book ne kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba
Daga can gefe Malam Isiyakun ya tsaya ya takarkare yana ture dutsen D'ahuru ya taimaka masa.
Aikuwa sai ga wata laya mai fad'i a kwance tsabar nauyin dutsin ya sanya ta tamushe duk tudunta da nannad'ar da aka yi mata.
Suka d'auko tare da fara kiciniyar kwanceta yana tsaye yana kallonsu jikinsa duk ya yi sanyi wato nan aka kawo bakinsa aka daure to akan me wai?
Annabi ya yi gaskiya da yake cewa mata za su kasance da yawa a wuta, shi kam bai ga abinda ya yi wa Maryam ba da za ta yi masa haka.
Aka warware laya itama mai cike da sa'kandamai guda uku daga kowane sashe sunan da labaraci ya fito radau Tajudden!.