Sashe 32
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ban ce masa komai ba na kad'a kaina na kama hanyar fita daga d'akin ina goge hawayen da yake zuba amma ya'ki tsayuwa idan na tuna abinda ya gayawa Hauwa akaina sai zuciyata ta d'auki zafi mai tsananin gaske.
Ashe soyayyar karya yake yi mini domin ya amfana da jikina ne, babu irin kalamin soyayyar da baya yi mini idan muna kwance a bargo guda.
Wai ashe akwai ranar da zata zo ya ci mini fuska a wurin matar da yake shirin aurowa.
Cikin damuwa mai yawa na sauka kasa, kuma duk yadda na so da ganin na daidaita kaina abin ya gagara domin zuciyata ta gama karyewa da mutumin nan munafiki ne na karshen, gashi ya riga ya gama da ni tunda ya d'irka mini ciki ya san dole wasu kudirorin nawa na janye su.
Hajja hankalinta ya tashi ganin yadda na sakko a hargitse ta kama ni ta zaunar kusa da ita.
Lokacin zuciyata ta sake tsinkewa hawayen ya tsananta zuba a kumatuna.
Cikin damuwa ta fara tambayata abinda ya faru, gabad'aya yanayinta ya canza, sai na ji tsoron tashin ciwonta domin jikinta sai karkarwa yake yi.
Ta dinga fad'a tana fad'in na gaya mata abinda ya yi mini.
Na yi kokarin tsayar da kukan da nake yi a raunane na ce.
" Hajja ni ba zan hana shi aure ba, amma don Allah ki yi masa magana ya daina kwance mini zani a wurin wadda zai aura da kunnena na ji yana gaya mata cewa ina zaune a gidansa ne a matsayin alfarma, amma bana daga cikin irin kalar matan da yake da burin aura.
Hajja kin fi karfin komai a wurina a yanzu dai ko kara ki ka ajiye ki ka ce kada na tsallaka zan kiyaye saboda irin kulawa da soyayyar da kike mini, amma kalamansa suna nufin haddasa husuma tsakanina da Hauwa idan Allah ya kaddara shigowarta gidan nan, kin ga dama ya gaya mata ga yadda akayi ya aureni ai ba zata mutuntani ba tunda alfarma ya yi mini.
Sannan tunda maganar auran nan ta b'ullo yake gaya mini duk maganar da yaga dama harda zagin iyaye Hajja ba zan iya jurewa ba domin iyaye sun wuce raini."
Ta dinga girgiza kanta tana fad'in." Alfarma ai ke ce ki ka yi masa Amina, kuma dole ace da mijin iya baba.
Duk inda za a je kece Amina dai da ki ka aure shi a lokacin da kowacce mace ke gudun rab'ar inda yake ba don komai ba sai dan saboda matsalar da take tattare dashi.
Ke alheri ce a wurinsa shine bai sani ba da har yake fad'in wad'annan maganganun kuma wallahi muddin ya ce zai biyo ta irin wannan sigar zan rusa maganar auran gabad'aya."
Tana rufe bakinta ya sauko cikin jallabiya da wayoyinsa hannu.
Ya zauna yana kallonmu wani irin yanayi a tare da shi.
Aikuwa ta rufe shi da fad'a ta inda take shiga ba ta nan take fita.
" Wallahi Tajo ka kiyayi 'batawa matarka rai, kai baka da tausayi ne, baka duban abinda take d'auke shi kullum cikin daga mata hankali kake kana sanyata koke-koke. wai har kana cewa zaman alfarma take yi a gidanka.
To idan har Amina zaman alfarma take yi, ni ma alfarma kake yi mini, yanzu ba ka ji kunyar yi wa yarinyar nan haka ba, kada fa ka manta tilasta mata na yi rana daya ban ta'ba ganintaba, itama bata taba ganina ba, amma saboda mai biyayya ce ta amince har ta aureka bayan duk ta san abinda yake faruwa da rayuwarka.
Me yasa a lokacin da muka nemi Hauwan ta maye gurbin 'yar'uwarta taki amincewa saboda tana tsoron mutuwa, amma ita Amina ta sadaukar da rayuwarta ko ta mutu ko ta yi rai bayan tana da tarin k'udurori a rayuwarta.
Tajo ba kai ka yi wa Amina alfarma ba, itace tayi maka alfarma ka ajiye hakan a cikin ranka, kuma muddin kana son mu zauna lafiya da kai ka kiyayi 'bata mata rai."
Sai da ya bari ta gama fad'an tukkuna ya sassauta murya a nutse ya ce." Hajja ku yi hakuri don Allah, amma yana da kyau ki saurari uzurina a wannan ga'bar ina da abubuwan da suke damuna game da yarinyar nan.
Dalilin da ya sanya ban zo na gaya miki ba saboda naga ita din mafi soyuwa ce a wurinki, amma ai ni ma tana kwarata kwarai da gaske gashi bata da kunya wallahi, bata ganin girma da shekaruna kamar sa'anta haka take sa'insa da ni.
Sannan bata ba ni kulawa ta kowane bangare, ta hana ni hakkina tsayin satika, kuma ina cikin sha'awa, duk lokacin da ki ka ga ta hau sama wajena wallahi masifa ta je nema ba kwanciyar hankali ba, ni duk yadda na so mu zauna lafiya ta'ki, yau ta ce wannan gobe ta ce wannan, ta'ki ta bari mu fahimci juna."
"Ayyo, shiyasa kenan kake sanar da Hauwa ta shigo a shirye itace matar so ko? gata 'yar uwarka, ga shi kuma kana sonta saboda tana kama da Samira, sannan siririya ce ita Amina kuma 'yar lukutan, sannan ni ce nace ka aureta, ni da ita muna cikin alfarma."
Murmushi ya d'anyi ya saci kallona.
Ina ta goge hawaye don na ji dadin titsiyar da Hajjan ta yi masa, na cigaba da jan majina Ina shassheka da sake nuna raunina don kada ta yarda da abinda ya gaya mata a kaina.
Ya ce." Ni wallahi ina sonta Hajja ban ma san irin kalar son da nake mata ba, itama damar da ta samu kenan take yi mini iyashege yadda ranta yake so, ki daina fad'in tana cin alfarmar nan Hajja.".
Ta ce."To ai ba zata yi maka karya ba tunda dai da kunanta ta ji kana gayawa kishiyarta baka sonta ni na aura maka ita.
Da sauri ya ce." 'Karya take yi wallahi ni yaushe rabona ma da na yi waya da Hauwa, ni fa auranta bai wani kwanta mini a rai ba Hajja saboda k'arfafa zumuncinku da inna Uwani ya sanya har nake bibiyar maganar."
Da sauri na dube shi jin yadda yake rantsuwa da wallahi bai yi magana da Hauwa ba.
Hajjan ta ce." Oho toni dai na gaya maka ka kiyayi b'atawa matarka rai, ba wai dan za ka yi aure ka k'untata mata ba." Yadda take yi masa fad'a sai ka d'auka karamin yaro ne, shiyasa aka ce namiji duk shekarunsa a gaban iyayensa yaro suke kallonsa.
Abin har ya d'an so ya ba ni kunya.
Duk abinda ta ce masa a kaina sai ya ce to, babu musu da jayayya.
Sai da ta kammala tsaf tukkuna ya nisa kafin ya ce." An gama Hajja, za a kiyaye in sha Allahu amma itama wane irin jan hankali za ki yi mata a game da irin abinda take yi mini."
Ta dube ni cike da tausayi.
Ni kuwa na sake karyar da kaina ina d'an sake jan majina.
Ta juya tana kallonsa kafin ta ce." Kai Tajo mace mai wannan lalurar ai abar tausayi ce wallahi kuma cikin nan wahala yake bata da gasken gaske, ai dan kai namiji ne baka san ya abin yake ba."
Ya kalleni babu yabo ba fallasa ya furta." Ni kaina abinda nake dubawa kenan Hajja shiyasa nake tausaya mata, amma itafa ba yarinya ba ce, duk dabarun da za ta yi mini na samu na nutsu ta sani, me yasa ba zata yi mini ba."
Hajja ta kawar da kanta ba tace masa komai ba, dan yadda ta nuna ma sam bata san maganar.
Ya sake rauntar da muryarsa yana cewa." Tana da taurin kai da tsayayayya Hajja, kuma bata tausaya mini irin na miji da mata ."
Ta dube shi hankalinta a kwance .
" Baka ji tausayinta ba yaushe zataji naka, ai kai baka iya rarrashi ba, mace tsohon ciki ai abar lallabawa ce."
Ganin duk hanyar da ya bullo dan ta duba kokensa taki sai kawai ya fito mata a mutum ya cire kunya yana cewa." Ko yanzu abinda ya had'a ni da ita kenan, na nemata taki yarda, kuma wallahi tallahi a bukace nake Hajja, yarinyar nan ce halalina."
Kunya mai 'karfi ta rufe ni, da sauri na sunkuyar da kaina, ban kara kallon inda hajjan take zaune ba, dan ji nake yi maka kamar na tashi daga wajan.
Itama cikin jin nauyi ta yun'kura domin ta bar wajan tana cewa." Ni dai na gaya maka kada yarinyar nan ta sake kukan takaicinka, ai namiji kake duk hanyar da zaka bi wurin tausar zuciyata ta yi maka dabaru ka sani, kaine ka tunzurata har hakan ta faru a tsakaninku sai ka rarrasheta."
Tana gama maganarta ta bar wajan.
Ni ma na fara ko'karin tashi ya cimma ni, ya zauna kusa da ni har jikinmu yana haduwa.
Sosai ya tausasa murya yana ce wa." Hajja ta dawo da soyayyar da take mini kanki Amina, kiri kiri sai ki yi mini laifi amma a nuna ni ne mara gaskiya."
Uffan ban ce masa ba.
Ya kama hannuna ya rike a hankali ya furta." Kin san wani abu." Na yi shiru ban tanka masa ba
Ya ja numfashi tare da rintse hannuwana acikin nasa." Na yi kuskure akan abinda na yi, ki yi hakuri ki ajiye hakan a matsayin ajizanci irin na dan Adam zan kiyaye."
Gudun aure na kudi ne kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Kallonsa na yi Ina sake tuna lokacin da yake waya da Hauwa.
Na ce." Wallahi ba zan yarda ba ai ba a cizan mumini a rami d'aya.
Akwai manufar da ta sanya kake zaune da ni kamar yadda ka fad'a."
Ya jim yana kallon kasan kafet kafin ya ce." Ni dan Adam ne fa, dole a cikin ayyukana akan samu kuskure smma wallahi ban gayawa Hauwa hakan dan na tozarta ki ba, ina sonki kwarai da gaske."
Ta'be bakina na yi ban ce masa komai ba domin gabad'aya na dawo daga rakiyarsa, mayaudaran kalamansa sun daina kayatar da ni.