← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 276

Sashe 101

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali na ajiye wayar na silale na kwanta saman ledar dake tsakar d'akin Ina wani irin kuka mai ciwo lallai mutumin nan ya yi wa rayuwata illa ta kowane 'bangare, kokari yake yi da gaske sai ya shiga tsakanina da 'yar uwata jini daya bayan fin karfin da ya yi mini wurin raba ni da yarona duk kuwa da tsananin shakuwar da take tsakaninmu kamar ya sanya almakashi ya datse yanzu ganin Yusi ya yi mini tsananin wahala balle na ji muryarsa, wannan wace irin masifa ce!

Wajejan sha biyu na dare na tashi na je na d'auro alwala nafila na yi raka biyu cikin sujjadar karshe na fashe da kuka tare da kai wa Allah kukana akan ya za'ba mini abinda ya fi alheri a rayuwata muddin rabuwata da Alhaji Tajon akwai alheri to Ubangiji Ya gaggauta kawo k'arshen lamarin.

Idan kuma zamana dashi bai kare ba ina ro'konsa ya daidaitamu cikin ruwan sanyi ba tare da an kai ruwa rana ba rayuka sun 'baci ta dalilin hakan.

Na kwanta bacci da jin sasaauci a zuciyata domun kuwa ina kammala addu'ar na ji nutsuwa ta shigeni tare da tawakkali da kar'bar duk irin abinda Allah Ya zartar a kaina.

Da safe bayan na yi wanka Sayyada ta kawo mini kayan karin kummalo d'akin da nake ta zauna muna d'an ta'ba hira jefe-jefi kafin ta fita daga d'akin domin ba ni damar karyawa a nutse.

Gama karin kummalona ke da wuya Babansu Fadila ya zo wato mijin anti Yagana lokacin Baban Saude ya fita zuwa babban gida wajan Dada domin su gaisa.

A soro na same shi a tsaye da shirin fita wajan sana'arsa muka gaisa kafin ya fara yi mini maganar da ta kawo shi domin jiya duk wayar da muka yi da anti Yagana a gabansa ne kuma shi ma a jiyan da magriba ya ga gilmawarta a tasharsu sai yake hasashen anya ni din ce domin bai gama tabbatarwa ba sai da ya dawo gida tukkuna ya tabbatar da cewa ni din ya gani bayan saukata a garin.

Nasiha da ban ha'kuri tare da kawo misalai irin na matan magabata ya dinga yi mini har yana cewa ko don yadda 'yar uwata take shiga damuwa matsananciya akan matsalata yana da kyau na jure na yi hakuri na samar mata da nutsuwa domin kuwa jiya raba dare ta yi akan dadduma gaban Allah tana addu'a da hawaye akan lamarin.

Wannan dalilin ya sanya shi ma ya kasa rintsawa har garin Allah ya waye kuma ya kudire a ransa cewa zai zo ya same ni akan abinda yake faruwa.

Hakika sun ba ni tausayi sosai ita dashi kuma sun isa su ce mini na yi ko na bari ba tare da na yi musu jayayya ba.

Amma a wannan karon Ina ganin ba zan iya bin umarinsu ba domin kuwa duk abun nan da ake yi shi wanda ake yi dominsa bai yi wata magana ba, bai zo ba tun bayan kiran da ya yi wa anti Yagana jiya ban sake ji daga gare ta ba.

Hakan na gaya masa na ce ya bari tukkuna ya magantu ai yanzu dama a hannunsa take idan yana da ra'ayin cigaba da zama da ni zai zo ya nemi sulhu idan kuma bashi da ra'ayi to zai aiko mini da shedar da zata nuna mini lallai ya gama zama dani, Ina ganin kamar haka ya dace a yi.

Sai ya nuna ai ba haka ya dace a yi ba tunda ai anti Yagana ta gaya masa har yanzu na'ki na fadi abinda ya yi mini kuma ba shine ya ce da ni na tafi gida ba yaji na yi na bar d'akina don haka kuwa tunda ba shine ya ce na tafi ba ai babu lallai a ce sai ya nemi inda nake domin ya ji dalilina.

Na jima ina nazarin maganar kafin daga bisani na yanke shawarar gaya masa abinda yake faruwa tunda ai shi din ba bare ba ne, sannan kuma maganace da za a zauna a zube ta shi ma makusancina ne tunda yana auran sha'ki'kiyata.

Duk bada'kalar da take faruwa na zayyana masa da irin ni ma abinda na aikata da tuban da na yi sannan kuma na tabbatar masa da cewa na gane kuskurena na kuma nemi afuwa da gafarar Allah da kuma neman sulhu da shi domin mu yafi juna amma hakan bai yi masa ba har sai da ya d'auki hukuncin kaurace mini na tsayin wattanin tare da shigowa garin ba tare da ta nemi inda nake ba .

Sosai al'amarin ya dake shi ya jima yana nazari kafin daga bisani ya dube ni da alamun tausayi da sasaauci ya ce." Ni ai duk ba ta gaya mini haka ba Amina ta dai ce mini kawai tana zargin ke ce ba ki son auran ki ke so ki kasheshi amma ba ta gaya mini dalili ba
A hankali na furta." Ai ba ta sani ba don ban gaya mata ba har yanzu saboda na san halinta da sanya abu a ranta kuma bai zama lallai ta fahimce ni ba, in banda kai da Baban Saude babu wanda na gayawa sai ko Sahura 'kawar nan tawa.

Ya ce." Lamarin na ku ne da rikitarwa Amina, kina da kuskure shi ma yana da nasa kuskuren ai dama ba za a d'auki lefi a daurawa mutum d'aya ba.

Kuma gaskiya abinda ya fi tsaya mini a raina dangane da lamarin nan yawan zargin da ki ka ce mutumin nan yana yi miki babban abu ne a ganina wannan ba soyayya ba ce domin kuwa zargi yana daya daga cikin manyan dalilan da suke saurin lalata ala'ka ta auratayya.

Ba zai yiwu a ce don ya aureki a matsayin bazawara kuma 'yar kasuwa ya dinga zarginki ba sam ba shi da hujja ko a wurin Allah domin kuwa bai ta'ba kama ki da wani mummunan abu ba.

Sai maganar tsayin wattanin da ya d'auka ba tare da ya neme ki ba, wannan normal ne Amina akwai matan matafiya da suke shekara da biyu uku ba tare da mazajensu ba kuma aurensu bai lalace ba sai dai kin san shi addini kogi ne domin ni kaina na ji wasu malaman suna cewa idan namiji ya k'auracewa mace na tsayin wata uku hud'u biyar har zuwa shekara to aure ya haramta a tare dasu amma fa sai in dai suna kwana tare a gida daya ya aikata hakan.

Idan sun yi nesa da juna kamar dai matafiyi wannan ba lefi ba ne haka daga shekara daya zuwa biyu aure yana nan.

To anan za mu iya cewa auranku yana nan tunda baya garin da a ce kuna gida daya ne kuna kwana a daki daya ya k'aurace miki tabbas akwai alamun a tambayi malamai domin sanin menene gaskiyar lamari.

Wannan shine iyakacin fahimtata.
littafin nan na kudi ne kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Ya nisa kafin ya cigaba da ce wa." Sannan ke ma zan gaya miki gaskiya abinda ki ka yi bai kyautu ba domin kuwa kin shiga hurumin Ubangiji dalili kuwa ai shine mai rayawa da kashewa kuma bai zama lallai don kin haifi d'aya da lalura ba ki ce duka yaran da za ki haifa haka suke ba.

A lokacin da ki ka lura da samuwar cikin sai ki bar shi kawai ki ro'ki Allah ya ba ki masu albarka kuma masu lafiya.

Abu na biyu kuma kin ga mutumin nan bashi da yara shi zai so ko masu lalurar ne wannan kadai ya isa ya sanya shi ya k'ullaceki kuma ya ga duhunki domin kuwa ai zai ga kamar kina yi masa b'akinciki ne saboda wata hujja taki wadda bata da tushe balle makama, sannan da yawan mutane ba zu fahimceki ba domin kuwa za a ga ai ke ko dan kina da yaran ne ya sanya ki ka zubar masa da nasa cikin.

Lefi ne babba ko wurin Allah Amina amma kuma na ji dad'i da ki ka gane gaskiya kuma ki ka nemi gafara a wurin Allah lallai Ubangiji mai afuwa ne kuma mai yafiya ne, sannan kuma shi ma Yallabai din yana da kyau ya yafe miki ya d'auki 'kaddara domin ta riga fata bai kamaci ya d'auki wannan matakin ba domin a ganina da tun farko kun kashe matsalarku a cikin gida hakan zai fi alheri ba tare da kowa ya sani ba domin kuwa irin wannan lamari baya buk'atar a ce a zauna ayi ta nanata shi saboda kowa da irin fahimtarsa wasu suna gyarawa ne wasu kuma na 'batawa."
Tun a 'karshen maganarsa na fahimci gugar zana yake yi mini akan Baban Saude wata'kila kafin zuwansa nan din anti Yagana ta gaya masa halinsa shiyasa yake yin shagu'be shi ma yana nuna rashin dacewar kawo maganar wajan Baban Saude ni kuma gabad'aya duka sun kasa gane dalilina.

Ban kawo 'karar Alhaji Tajo wurin Baban Saude da zummar ya wulakantashi ba, ni kaina nasan wargi ma wuri shi ka samu.

Baban Saude idan yana yi wa wasu ya zauna lafiya ina ganin kwarjini gami da haiba irin na Tajudden ya wuce a ce ya yi masa tijara mai muni.

Ina dai da tabbacin cewa za su yi musayar yawu irin na fahimta domin a samu matsaya akan abinda yake faruwa.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.

Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.
Chapter 101 · 0% Book details