← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 276

Sashe 82

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*55*
Sai zamanta ya rage mini kad'aici mussaman idan Yusura ta tafi islamiyyar dana sanyata anan bakin titi domin ta cigaba da dora haddarta kasancewar dama ta yi saukar al'kur'ani wattanin shida da suka wuce wanda ya yi daidai da lokacin da ta zana jarrabawar fita daga secondary da kaina na yi tunanin sanyata a makarantar saboda zaman a haka bashi da amfani zata sake d'aukar darrusa masu muhimmanci kafin lokacin auranta tunda makarantar ba wai al'kur'ani kawai suke koyarwa ba har da sauran littafain na addini za ta kara sanin tsarki da hukunce-hukuncensu.

Ranar da Sahura ta zo yini muka yi muna magana daya har dai na gaji na yi mata shiru domin kuwa ba zan ta'ba yin abinda take so ba don ban ga abinda na yi ba ai na d'auka sai mutum ya yi lefi tukkuna zai ta bibiyar wanda ya yi wa domin ya yafe masa.

Ita kanta tasan maganata akan daidai take ba zai yiwu ace sun mori juna sun jiyar da kansu dadi ciki ya samu ace ni kuma dake gefe na je na yi musu wahala ba, ai ba yarinya ba ce balle ace kuma ita din menene bata sani ba tunda malamar asibiti ce duk wanda zai zage ni ya dad'e bai yi ba abu ne mai mutukar wahala wata mace ta aminta da hakan.

Ita Sahura wai kada mutane su yi mini wata fassara ko a juya maganar ace ina yi mata b'akinciki don ta samu cikin haihuwa wanda ni kuma wallahi babu wannan a cikin raina komawa ne kawai ba zan yi ba, ni ma a lokacin da na samu nawa haka nayi ta fama dalilin ma da ya sanya kenan nake d'agawa Hadiza kafa saboda wahalar da ta yi mini.

Wai lallai sai na kira shi na bashi ha'kuri na gaya mata ha'kuri kuma na nawa lamarin da ba yau akayi shi ba an kusa wata biyu to me zai sanya na damu kaina.

Ina nan dai da kudirina wata uku na cika idan bai zo ba to kuwa zan san inda dare ya yi mini ai ko addini wannan abin da yayi ba daidai ba ne kuma daf yake da ya lalata auransa.

Duk hujjar da ta kawo mini zan soke ta dole sai ta ha'kura ta kyaleni ta tafi da b'acin rai dalilin da na ki na yi abinda take so.

Babanmu da Baba Sule suka zo ranar wata jumaa bayan an sakko daga massalaci na ji dadin zuwansu sosai na shirya musu abinci mai kyau suka ci suka koshi suna ta yaba gidan da fatan alheri na dinga nazarin Baba Sule gabad'aya duk ya susuce tufafin ma dake jikinsa kamar ba wankakke ba takalmi irin soso shine a kafarsa.

Babanmu ne kawai cikin sutturar arziki tsaf dashi, sai na ji kunyar hakan a cikin zuciyata ko babu komai Baba Sule uba ne duk lalacewsa kuwa, duk ranar da babu ran Babanmu dole shi din zamu k'alla a matsayin Ubanmu kuma idan da kara duk wata taguwa da zan dinkawa Babanmu shima ya kai ace na had'a dashi ganin da na yi masa babu kintsi ya sanya jikina yin sanyi domin yanayinsa ya nuna yana buk'atar agaji ilai kuwa ashe damuwa ce mai yawa a tattare dashi dalili ubangidan nasa Alhaji Muntari ya karye jinya ta cinye masa kudi ga tarin bashin mutane dake kansa komai ya karye masa wasu sun ha'kura wasu kuma sun ce sai an biya su, wannan dalilin ya sanya gidan da yake ciki aka sanya shi a kasuwa domin biyan bashin da yake kansa.

Yadda Baba Sule yake mini bayani lamarin ya bani tsoro mutuka da gaske yanzu uwargidansa anti Maimuna ita kadai ce ke jinyarsa anti Jamila ta gudu garinsu Bichi bayan ta turasashi ya saketa wai ba zata iya zama ta lalata kuruciyarta a banza ba.

Yana gaya mini baban yaronsa namiji wato Turmuzi yana nan yawo cikin tashar Kano line yana bin 'yan kamasho da samarwa da matafiya mota a sallameshi ya lalace da shaye-shaye tunda wasu lukutan a tashar yake kwana sai yayi sati bai je gida ba.

Kuka sosai na dinga yi ina kiran sunan Allah amma anti Jamila ba ta yi wa kanta adalci ba, ni a tsarina duk wahala ba zan iya watsar da yarana akan jin dadin duniya ba, babu ma yadda za a yi na tafi na bar yarana a wurin da nasan ba zasu samu kulawa ba hankalina ma ba zai ta'ba kwanciya ba.

Anti Maimuna ta ba ni tausayi sosai ita kuma tata jarabawar kenan rayuwa kenan.

Ba ni da halin da zan iya biyawa Alhaji Muntari bashi har na kusan miliyan talatin gabad'aya ma abinda nake juyawa bai kai hamsin ba ribar da take fita yau da gobe da ita muke buk'ata ni da Hamusu da kuma biyan yaran shago hakkinsu.

Alhaji Tajo shi yake da iko koda miliyan dari ne don ya fitar ya bayar ba na tsammanin dukiyarsa zata girgiza amma da nauyi sosai a ce na tunkare shi da wannan maganar har cikin raina nake jin wani iri dangane da ibtila'in rayuwar da ya faru da Alhaji Muntari domin ko banza ya taimaka mini ni ma a can baya a wannan ga'bar ya kamata ace na tagaza wani abu kafin akai ga kar'bar kudin gidan da yake ciki wannan duniyar ta zama abar tsoro.

Haka na kwana na yini da tunanin hanyar da zan bi wurin ganin na nemi taimako daga wajan wannan wannan d'an tahalikin ba tare da ya fassara ni ba.

Na kira anti Yagana na gaya mata domin ta ba ni shawara itama dai abinda Sahura ta ce shi ta fad'a na sauke abinda nake ji kawai na neme shi domin yin hakan babban taimako ne da zai sanya ni dashi mu tsinta a ranar lahira.

Na yi na'am da shawararsu domin a raina na ji zan iya jure cin kashi da bakaken maganganunsa muddin zai taimaka ai me nema baya fushi ni ko bashin ne ma ya biya masa su dai zauna a gidan ni kuma zan yi kokarin ganin na d'auki nauyin kaishi babban asibiti domin a duba lafiyarsa sosai.

Na samu lokaci ranar lahadi da la'asar domin a irin wannan lokacin ne yake free sosai na kira shi a waya daf da zata katse ya daga yana sallama.

Na amsa a nutse kafin na gaishe ya amsa can kasa kamar wanda yake cikin mayen bacci.

A sanyaye na ce." Dama na kira ka ne kawai na gaisheka na ji ya kuke ina Yusi."
Ya ce." Ina nan lafiya muna nan Abuja tare dashi gidan babban abokina Alhaji Amadu na taba baki labarinsa ko?"
Na ce." Eh kun dai ta'ba yin waya sau daya a gabana ina yawan jin sunansa a bakinka."
A dan sanyaye ya furta." Yana nan rai a hannun Allah Amina yana jin jiki muna kan shirye shiryen tafiya asibitin jiddah nan da kwana uku"
Jikina a mace na ce."inna lillahi me yake damunsa haka?"
"Kin san yana da ciwon zuciya dama to wannan karon da ciwon ya motsa masa abin ba kyau ni har na fara fitar da raina a kansa Amina."
A sanyaye na ce." In sha Allahu zai tashi zai samu lafiya."
Ya ce." To Allah Ya sa, ina fatan dai lafiya kuke na yi mamakin kiran da ki ka yi mini a wannan lokacin da ban yi tsammani ba, ni da kika kullace ni kina gaba da mijinki ko Amina baki damuwa da halin da nake ciki ba, ai ina kallon yadda ake soyayya a wurin Hajiya Maryam mai d'akin abokina Alhaji Amadu amma ni da nake da mata biyu kun yi watsi da ni ko, ita waccan din idan an yi mata uzuri ke fa? son ranki kike bi, ba ki damu da abinda zai same mu ni da Yusuf ko ba haka ba ne?"
Jiki babu kuzari na ce." Ban kyauta ba ka yi hakuri amma me yasa ka gaza fahimtata ya kamata ku yi mini adalci a wannan lamari sai ka tsiri gaba da ni, ban kullaceka ba kaine ma kake jin haushina dalilin da ya sanya ma kenan na ga rashin dacewar haka na kira ka yanzu domin mu sasanta gabar ta isheni haka.

"To tunda kin nemi sulhu zuwa za ki yi inda nake ai ki lallaba ni domin ni ma ba ni da wata lafiya rashin lafiyar abokina ta dame ni a kwanakin nan Ina buk'atar mai kula da ni ta ba ni magani ta kuma kwantar mini da hankali da kalamai masu dad'i zuciyata ta daina yi mini tunanin kamar ban yi sa'ar iyali ba."
Cike da mamaki na furta." Yallabai duk me ya kawo wannan maganganun don Allah."
Ya nisa kafin ya sake cewa." Kulawar da abokina yake samun wurin iyalinsa shine ya sanya nake jina kamar maraya gashi dai babu abinda Allah ya rage ni na jin dadin duniya amma matata ta na yi mini wulakanci."
Dariya maganarsa ta ba ni wai wulakanci wato shi baya duba abinda yake yi mini a matsayin wulakanci saboda namiji ne duk abinda ya yi daidai ne."
Na yi dariya 'yar kad'an kafin na ce." To shi ba ka ganin bashi da lafiya ai dole a ninka bashi kulawa ko ka manta lokacin da ka yi mura a gidana yadda na dinga lalla'baka ina rarrashinka kamar jariri."
Ya ce." Ni dai na gaya miki zan sanya a kawo miki ticket da za ki same ni anan abuja gobe kafin mu wuce saudiya ki ba ni magani kada na tafi da lalura.

A dukunkune yake maganar amma na gama fahimtar inda ya dosa wannan ya nuna mini cewa a mutukar bukace yake dauriya ce kawai da son dole sai an nuna iko ba zai neme ni ba muddin ba ni na neme shi ba yanzu kuwa dana tsaga billena na kira shi kai tsaye yake neman abu a wurina.
Chapter 82 · 0% Book details