← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 276

Sashe 135

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni fa wallahi masifar nan ta ishe ni haka
don Allah ki samu nutsuwa gabad'ayanmu fa babu yaro, yanzu ke za ki gyara auranki da zumuncin da yake tsakaninki da shi, na gaya miki idan kina so ki samu nutsuwar zuciya don girman Allah ki fita sha'aninsa da matarsa, da sannu idan muna da hakki za mu gan su a rana."
Shiru ta yi ba ta sake cewa komai ba, ta dai sunkuyar da kanta kasa tana tauna lebanta tabbacin abin da ya yi mata ya yi mata ciwo a zuciyarta.

Sai wajejan tara da wani abu tukkuna muka rabu ta shiga d'akinta da zummar shan maganin ciwon kai ta kwanta dalilin kukan da ta ti'ka, abinci ma ni na bi bayanta da shi kafin na fito falo na zauna na ci nawa muna hira jefi jefi da Baba Tabawa wajan goma da rabi ya shigo Baba Tabawa da saurin gaske ta yi masa barka da shigowa ya amsa babu wata kyakyawar kulawar da yake yi mata domin mutuniyarsa ce sosai a wasu lukutan har barkwanci suke yi ita dashi amma abin mamaki ko yau ni ma ban ji dadin abinda ya yi mata ba.

Ta dube ni tana fad'in." Ni ma kuna nema ku shafa mini kashin kaji Amina, Yallabai kamar fa haushina yake ji duk yadda nake ko'karin ganin na gyara ku abin zai shafe ni.

Yadda ta yi maganar da alhini da damuwa sai ta ba ni tausayi da dariya na d'an yi kad'an kafin na daidaita kaina na ce." To ke ina ruwanki Baba, kawai dai ransa ne a b'ace shiyasa ki ka ga bai amshi gaisuwarki da kulawa ba, kada ki wani damu ai ba ki da lefi."
Ta yi shiru tana jijjiga kai har da tallafe ha'ba.

Na yi dariya sosai ina fad'in " Hajiya Baba Tabawa ta mu ta gargajiya."
Ta dube ni da yanayi na zullumi amma ba ta ce komai ba.

Daga can barandar samansa na ji maganarsa na juya da sauri yana tsaye hannunsa zube a cikin jallabiyar dake jikinsa ya ce." Zo."
Na yun'kura na tashi da tahamidi da kuma addu'ar rinjiye wannan lokacin nake jira, na kuma ji dad'i da ba a ja dogon lokaci ba gwara a yi ta ta 'kare kawai.

Na d'auka idan na shiga d'akin zan gan shi a rikice cikin matsananciyar damuwa, abinda ya ba ni mamaki bai wuce ganinshi a zaune a gefen gado da waya a kunnansa yana magana cikin rarrashi da wata kalar murya wadda tun tsayin zamana da shi ban san shi da ita ba.

Jikina ya d'an shika kad'an amma lokaci d'aya ban bari ya fahimci raunina ba, na zauna gefansa hankali da jina yana kansa domin fahimtar da wa yake waya.

Kasa gane kowacece na yi domin da da farko na d'auka Momi ce sai da na ji yana kiran Maman Hanif tukkuna na yi tsai ina tunanin wacece wannan kuma.

Tunani na ya katse lokacin da na ji sautin maganarta cikin reshin kuka ban dai ji mai take gaya masa ba, amma gabad'aya yanayin yadda take magana shi ya tabbatar mini da cewa cikin tsananin b'acin rai take.

Na dinga nanata sunan a cikin raina Maman Hanif domin na kasa gane wacece can nazarina ya hasaso mini Nabila kanwar Momi ce tabbas ita ce babban yaronta sunansa Hanif hakane yakan zo wurinsu Adam a duk lokacin da aka yi hutun makaranta.

Ajiyar zuciya na sauke na sake kai duba na gare shi ya tak'arkare yana ta rarrashi da ban ha'kuri na gyada kaina ina jimanta matsayin momi da alhalinta a zuciyarsa.

Maganar abinda ya faru tsakaninta da Hauwa suke tattaunawa da 'kyar dai da jibin goshi da irin rausayar da kai da muryar da yake yi ya rarrasheta ta ha'kura tare da kudirin janye 'karar da suke ko'karin shigarwa akan Hauwa.

Na ji dad'i dai da bai gaya mata irin hukuncin da ya yanke ba ba domin a yadda yake a zaburen nan abu ne mai sau'ki ya gaya mata cewa ai ya saki hauwa ba.

Wasu lukutan kuma zurfin cikinsa yakan burge ni ya kuma yi masa amfani.

Tabbas Hauwa bata kyauta ba, kuma ni ban ga laifinsu ba don sun ce za su kai ta 'kara matsalar kawai idan har aka bari hakan ta faru gabad'aya rayukan kowa ne zai b'aci shiyasa Annabi ya yi hani da tayar da masifa domin idan ta tashi kafin ta kwanta sai an d'auki wani lokaci.

Ya kashe wayar ya dube ni fuskarsa kadaran kadahan.

Kafin ya yi gyaran murya ya ce." Ina alkawarin da muka yi ni dake ranar da baban Saude ya yi mana sulhu....

Kafin na ce wani abu kira ya shigo wayata dake saman cinyata.

Hajja ce sai na d'auka a tsanake muka gaisa da kulawa kamar koyaushe ta ce." Ai ya zo mun jima da shi kuma ya gaya mini dukkanin abinda yake faruwa dalilin da ya sanya na ce ba zan bari har sai gari ya waye ban yi magana dake ba.

Da farko dai ina mai kara baki ha'kuri ina kuma kara yaba miki bisa ko'karin ganin kin yi hakuri da duk umarnin dana ba ki.

Babu shakka kin nuna mini cewa ke din 'yar halak ce na gode sosai Allah Ya yi miki albarka Amina sai dai a wannan lokacin ba zan tauye miki hakki a matsayinki na uwa mahaifiya ba.

Ko daya ban ga lefinki ba domin tsira da mutunci ai yafi tsira da kudi babu wani dalilin da zai sanya yara su zauna a wurin da babu daraja kuma babu mutunci.

Hajiya Maryam tun kafin Tajo ya aureta shedar da muka yi mata mutuniyar kirki ce kuma har yanzu akan hakan muke kallonta.

Amma tabbas tarbiyar yaranta akwai nakasu ba wai na za'bi Kamalu na fifita shi akan Salim ba.

Kafin na kira ki a yanzu na zauna da Kamalu cikin hikima na tambaye shi ya kuma yi mini bayani tsakaninsa da Allah wanda nake da tabbacin haka siddin ba zai kirkiri karya domin ya 'bata Salim ba." Ta d'an yi shiru tana sauke numfashi kafin ta cigaba da cewa." Sannan mijinku na nuna masa kuskuransa sosai duk da ya kawo mini hujjarsa amma ni bata gamshe ni ba saboda banga dalilin da zai sanya ya ce a rufe miki abinda ya shafe ki ba.

Kenan babu adalci a ciki koda ya yi hakan ne domin yin nazari akan lamarin kafin ya yanke hukunci ta 'bangaranki ba za ki ta'ba gamsuwa da cewa bai hofintar da naki ba, ma'ana ya karkarta a bangare daya da tabbacin nan ne da gaskiya.

Abu ya faru wanda ya sosa ran kowa ina kuma sake baki ha'kuri domin a ko'ina ina irin wannan matsaltsalun suna faruwa.

Kin yi daidai da ki ka turo yara nan ni kin burge ni kwarai kuma kin yi hankali da ba ki tunkari Maryam da tashin hankali ba.

Ina so ki gaya mini abinda yake ranki don Allah kada ki ji kunyanta da kuma nauyi yaran nan kin amince da zamansu a hannuna kamar yadda mijinku ya ba ni su amana ko kuma na sanya Magaji direba gobe ya mayar da su gidan Gwaggwon gobe, idan har hankalinki zai fi kwanciya da hakan don Allah ki gaya mini gaskiyar abinda yake cikin ranki."
Sosai jikina ya yi la'asar na gaza cewa komai saboda tsabar nauyi da nazarin ya zan yi na ce mata ba ni son zamansu a hannunta wanda nasan ba wurin da za su cutu ba ne.

Maganarta ta dawo da ni hankalina.

Na ce." Hajja ni dama zamansu ne kawai ba na so anan din tunda har suna nan wurinki babu komai wallahi ai dake da Gwaggon duk daya kuke a wurina na amince su zauna Hajja Allah Ya taya ki riko."
Cike da farinciki ta furta." Aikuwa na gode sosai da wannan alfarma dana samu, ni ma zan samu ladan rik'on maraya ashe na gode Amina, in sha Allahu kuma yaranki ba za su yi kukan maraici ba, Allah Ya yi miki albarka kin jima kina yi mini alfarma ni kuwa da me zan saka miki "
Tak'arasa maganar da rawar murya.

Sai hankalina ya tashi jin tana shirin fashewa da kuka na ce." Haba Hajja ni din taki ce fa balle kuma yara don Allah ki daina yi mini godiya babu ita a tsakaninmu, addu'ar da ki ke yi mini da ita kika saka mini ita kadai ma ta ishe ni wallahi."
Can k'asa-k'asa na ji tana fad'in." To na gode sosai sai da safe." Sai ta kashe wayar.

A sanyaye na ajiye tawa a saman cinyata jikina duk ya mutu Hajja kuka take yi da gaske dalilin da ya sanya ma kenan ta katse wayar da sauri.

Sai kawai ni ma na ji ruwan hawaye ya ciko idanuwana wani kutittiran abu ya tsaya mini a wuya.

Lallai matar nan ta wuce ta nemi alfarma a wurina na tsaya yin jayayya da gaddama ba zata cutar mini da yara ba.

Wannan maganar zuciyata ke ta nanata mini. ........
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.
Chapter 135 · 0% Book details