Sashe 250
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru na yi bayan fitarsa na gaza tab'uka komai saboda mamaki yadda ya burkice.
Can k'asan zuciyata na ce mini tabarmar kunya ce fa yake nad'eta da hauka domin ya k'waci kansa duk hargagin banza ne.
Na yi shiru sosai ina sake nazarin maganganun da ya furta.
Tabbas kamar yadda ya fad'i mutum ne mai tsananin kishi.
Tun bayan haduwarmu ta farko a ofis dinsa da ya zo mini da maganar banza bisa wata hujja tasa to tun daga lokacin ban sake ganin wani abu na sakarci da b'acin suna daga wajensa ba.
Yana da ibada daidai gwargwado sadaka kyauta ciyarwa kulawa da marayu wasa da dariya da iya mu'amula.
Da'biarsa mummunan da na sani gaba da k'ullaci kuma cikin ikon Allah da zama ya yi zama a tsakaninmu ya rage.
Ban ta'ba cin karo da wasu alamu da za su nuna shi din manemin mata ba ne gaskiya idan na ce na gani na yi masa sharri tunda a yanayin yadda yake mu'amulantarta a shimfida ma wannan ya isa sheda da tabbatar mini da cewa bashi da lokacin bibiyar wasu matan a waje.
A yanzu dai idan na fahimci abinda ya hasala shi bai wuce don na ce ya ji tsoron Allah ba saboda shima ya haifa wannan maganar itace ta tunzura masa zuciya har ya fita da b'acin rai!
Mai tsanani hakan na tabbatar mini da cewa ya ji ciwon maganar sosai kuma abinda duk ya fad'a gaskiya ne yau kan an kira ni da mara mutunci mara kirki dole na bada ha'kuri Allah Ya sawwa'ke.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*165*
Ban yi zaton fushin zai tsananta da yawa haka ba.
Tunda a daran ranar da lamarin ya faru na bashi ha'kuri tare da nuna masa na yi kuskure sai ya dinga ciccijewa haka muka kwana bai ce mini komai ba da gari ya waye na gaishe shi ya amsa da k'yar.
Still da ya fita ya dawo da yamma nan ma na sake bashi ha'kurin bai huce ba.
Abinci ya'ki ci na dare da jiyan da yau a gidan Hauwa yake zuwa ya ci.
Ganin kamar kwantar da kan da nake yi ina bashi ha'kuri yana Kara masa kuzari da karsashin yi mini wulakanci sai kawai na 'kyale shi Hauwa ta kar'bi girki ya je ya yi kwanaki biyu ya dawo mini babu fuska har yanzu zai amshi gaisuwata amma akan dole ko na hau saman na same shi sai ya tsiri aiki a loptop ko ya kira yara su yi wasa.
Abin ya fara ba ni dariya da mamaki.
Na yarda na yi kuskure kuma ban kyauta ba na nemi afuwa sai a yafe mini ai a cigaba da cud'a rayuwar amma sai ya samu hanyar hura hanci da d'aga kai ganin ina binsa da kwantar da kaina dama dabi'arsa ce haka idan ana ba shi ha'kuri sai ya kara hawa ba zai sauko ba.
Gaisuwar ma sai na daina na zura masa ido ko ni nake da girki ba ni hawa saman abinci kuma tunda ya daina ci na daina kai masa.
Muka cigaba da tafiya haka tsayin sati biyu babu wani sukuni a tattare da shi domin alamu sun nuna ya fara gajiya yana ta kame-kame.
Da daddare na yi shirin kwanciya tsaf ina zaune Ina bawa Hasan nono shi bai yi baccin ba tukkuna ya turo kofar d'akin ya shigo cikin jallabiya k'amshin turaransa ya mamaye d'akin gabad'aya ya had'u da wanda na yi amfani da shi.
Na d'aga kaina na kalle shi muka had'a ido sai na yi 'kasa da kaina dama ni ban zafafa ba ai ya nemi wuri ya zauna a gefena babu yabo babu fallasa na sake kallonsa muka had'a ido a hankali na ce." Sannu."
Bai amsa ba ya d'ora hannunsa saman goshin yaron yana fad'in." Minal ta ce mini ba shi da lafiya?"
Na ce." Lafiyarsu lau fa ta ji yana dan tari d'azu shine take tambayata wai bashi da lafiya na ce mata kalau yake."
Ya kar'be shi daga hannuna yana fad'in." Tari ba ciwo ba ne Amina."
A takaice na ce." Ciwo ne amma ba irin wanda nake tunani ba.
Nono yake sha sai ya d'an 'kware shine bashi da lafiya in ji ta."
Ya d'an yi shiru na wani lokaci kafin ya furta." Jiya Hauwa a asibiti ta kwana bata da lafiya!"
Na dube shi da sauri " Bata da lafiya?"
Ya gyad'a kansa ya ce." Ciwon ciki ta yi sosai daga karshe dai cikin nata ne ya fice! amma alhamdulillahi ta samu sau'ki tana gida."
A d'an sanyaye na ce." Ban sani ba wallahi, kai za ka gaya mini kuma kana jin haushina."
Ya ce." Gashi yanzu na gaya miki ai."
"Allah Ya bata lafiya." Na fad'a cikin jin wani yanayi ta ba ni tausayi wallahi domin ta kallafawa ranta cikin Allah bai yi zai zo duniya ba.
Shiru na tsayin lokaci kafin ya kwantar da yaron kusa da d'an uwansa.
Ya gyara kwanciya a gadon.
Na dube shi yana lumshe idonsa yau anan za a kwana kenan.
Bai ji ma da kwanciya ba ni ma na kwanta a gefensa tunda dama na yi shirin kwanciyar.
Ya bude idonsa yana kallona ni ma shi din nake kallo wai akace labarin zuciya a tambayi fuska duk kame-kamen da yake yi na gane.
Ya d'an janyo ni kusa da shi can k'asa na ji maganarsa yana fad'in.'' Kin yi mini abubuwa da yawa na kyautatawa da kuma alheri ba kuma zan mance ba."
Ya nisa kafin ya cigaba da cewa." Wad'annan maganganun da ki ka yi a kaina sun yi mini zafi k'warai da gaske ina so wannan ya zama na farko ya kuma zama na k'arshe kada ki kara dangantani da haramci da abinda Allah ya la'anta.
Ki san irin maganar da za ki dinga gaya mini wadda ta dace da wadda ke kanki kin san kuskurene.
Ba ni da nufin auran Nabila a cikin raina na fad'a muku maganar ba d'aya ba sau biyu ba wallahi ba ta ta'ba ba ni sha'awa ba balle har na yi tunanin yin zina da ita ba zan boye miki ba har yanzu idan na kalleki na tuna abinda ki ka jingina mini raina yana b'aci wallahi."
A hankali na ce." In sha Allahu, Allah Ya ba ka ha'kuri."
Ya sauke ajiyar zuciya tare da d'an matse ni a jikinsa shikkenan daga lokacin kuma sai komai ya sauya..
Wai aka ce fad'an masoya hutu ne.
Da gari ya waye duk da bai sake yi mini maganar Hauwa ba amma ni da ita na kwana a raina domin yadda ya ke fadi ta sha wahala sosai kafin ma cikin ya fita tunda har sai da aka kwanta a asibiti kwana da yini.
Sai da yamma na shirya lokacin yara duk suna makaranta muka tafi da Mairo saboda yaran ita goya Hasan na ri'ke Usaini a kafadata.
Mai aikinta Ladidi tana ta goge -goge ita kadai a falon muka gaisa ta ce mana tana ciki a akwance na ce ta shiga ta gaya mata.
Minti uku ta fito tana sanar da mu cewa gata nan.
Ta nufi kicin da sauri.
Mun kai kusan minti goma sha biyar a zaune kafin ta fito daga cikin bedroom dinta ta d'ashe sosai kamar wata mara jini duk sanda take da ciki haka take irin wannan mugun hasken fau! yanzu abin ya hadu da d'aita domin da alamu cikin nan a k'alla zai yi wata hudu zuwa biyar ta sanya rai.
Ta ba ni tausayi sosai ta zauna kamar mara laka a jiki babu kuzari da karsashin tana fad'in." Ashe kune in banda shiririta irin na Ladidi ai da sai ta gaya mini cewa ke ce."
Na ce." Ba sai ta san ni ba Hauwa."
Ta d'an yi murmushi kafin ta ce." E hakane bata ta'ba ganinki ba sai dai labarinki wurin yara."
Na gyad'a kaina ina sake nazarinta a nutse na ce.
Ya jikin Ubangiji Allah Ya baki lafiya Allah ya mayar da abinda aka rasa."
Ta amsa da "Amin suma Amin na gode sosai."
Mairo ta gaisheta da jiki ta amsa tana kallon Hasan dake goye a bayanta sai kuma ta dube ni tana yar dariya ta ce." Sun k'ara wayo sosai yaran nan Amina."
Na ce." Sosai ni ma na ga girmansu wata uku muke yanzu."
Ta ce." Hakane kam."
Ta yi shiru tana lumshe Idonta na ce." Za mu tafi Hauwa Allah Ya kara afuwa."
Ta bude idonta tana kallona a daidai lokacin dana tashi tsaye ta ce." Na gode sosai."
Muka kama hanyar fita ni da Mairo.
Na ji tausayinta gaskiya abin babu dadi.
Da ya dawo ya ji labarin na shiga dubata ya yi murna sosai yana fad'in da haka kuke yi tun farko ai da na ji dad'i Amina."
Kwana biyu ba sai jikin nata ya kara rikicwa ba ranar girkina ne da daddare wajan sha biyu da wani abu lokacin muna shirin kwanciya ta kira waya cikin mayuwacin hali ciwon kai matsananci jini kuma ya tsinke mata.
Tare da ni da shi muka nufi gidan a ki'dime lokacin ma ta fice daga hayyacinta mai'aikinta na ta ihu jini ya bata jikinta da bedsheet din da take kwance a kai.
Muka gigice ni da shi domin dai kamar babu rai a jikinta.
Jikina na tairairayota ina kiran sunanta ko'ina a sake.
Ya fita da sauri yana kiran waya.
Kuka na fara yi ganin yadda take wata irin jijjiga ina kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! taune lebanta take yi hakan ya tabbatar mini da cewa jijjiga take yi domin duk rik'on da muka yi mata ni da Ladidi sai da ta fi karfinmu.
Ya shigo da kansa ya ciccibeta tunda dama ba wani nauyi ne da ita ba.
Na ce ya bari tukkuna a kintsa mata jiki domin a 'bace take da kaina na gyara mara jikinta cikin wannan yanayin ya fita da ita rai a hannun Allah muka bi bayansa Sukairaju ya kunna mota.
Ya ce da mai'akin ta koma gidan tare muka tafi asibiti a daran emagency da yake sananne ne a take manyan likitoci suka rufu a kanta.