Sashe 18
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na yun'kura da sauri zan tashi ya riko hannuna da k'arfi ya janyo ni na rikito kansa kawai sai ya sanya hannuwansa gabad'aya ya tallafe ni.
Ya sanya ha'barsa a dokin wuyana.
Cikin tsananin tashin hankali na fara ko'karin raba kaina dashi amma ban samu nasara ba domin wani irin riko ya yi mini mai tsauri wanda ya sanya lokaci kan'kani ga'bobin jikina suka fara amsawa
Ban san abinda ya gigitashi ba kawai ya dinga bin jikina yana shanshanawa yayin da hannuwansa keta mammatsa mini naman jikina.
Sai na rushe da kuka mai tafe da kururuwa domin har ga Allah gani nake yi kamar Yana ko'karin keta mini mutunci duba da irin yadda lokaci guda babu wata sha'kuwa da ala'ka ta soyayya mai k'arfi a tsakanina dashi amma cikin 'yan sakkoni ya samu jikina yana luguigiutawa har da zura hannunsa cikin rigar mamana.
Na dinga doke hannun ina tunkud'eshi da bugun bayanshi ya'ki sakina ya ma sanya k'afafunsu duk biyun ya kanainaiye ni...Shi kansa hularsa da gilashinsa na gado sun fad'i domin a ki'dime yake baya cikin hayyacinsa.
Da kyar da na samu ya cika ni, na tashi da sauri na d'auko hijabina na zura domin na lura ganin tsaraicina a waje shine ya asassa faruwar hakan tunda ai muna had'uwa wuri d'aya tsayin wattanin da nayi a gidan bai taba kwatanta rike mini hannu ba balle har ya rungume ni.
Kuka nake yi sosai gabad'aya na tattare a jikin bango banda so ya fita daga d'akin ba abinda nake yi.
Ashe k'arfi ne dashi a haka duk da ba wani jikine dashi sosai ba amma yadda ya rike ni kamar ina hannun katon gardi.
Gabana ya cigaba da bugawa sabili da tuna irin mutsukar da ya dinga yi wa tsokokin jikina.
Kusan mintina goma da faruwar al'amarin ya daidaita nutsuwa domin tunda na 'kwace yake kwance lakadan a gado kamar matacce ido a rufe sa'ilin kuwa da naga ya tashi zaune sai na sake tsorota domin gabad'aya ya zama wata kala fatar goshinsa tabi ta tattara kuma babu wani kuzurin kirki a tare dashi.
Ina kallo ya d'auki hula da gilashinsa ya sanya a idonsa ya zo ya tsaya daf da ni, ta cikin gilashin ya tsira mini ido babu yabo babu fallasa ya furta." Yau ce rana ta farko dana fara rungumar wata 'ya mace har na ji wani yanayi mai wahalar fassaruwa a tattare da ni, ban shigo nan da niyyar yi miki wani abu ba domin a raina na ajiye cewa na aminta da duk irin zaman da kike so ayi zan baki goyon baya.
Na shigo ne domin na tambayeki dalilin da ya sanya kika daina zaman break fast tare damu, kuma ina so na tabbatar da shin gaskiya ne maganar da Yusuf ya gaya mini cewa abinci sau daya kike ci a yini wai saboda kada ki yi 'kiba to kuma sai lamarin ya canza domin ganin zahirinki ya tayar mini da sha'awata ta d'a namiji, kuma nan ba da jimawa ba zan yi kokarin ganin na kawar da ita." Ya numfasa kafin ya cigaba da cewa." Ina ganin babu amfanin horar da kai da yunwa domin zama yadda ake so, ke ai daka ganin ki jikinki na ki'ba ne duk abinda za ki yi domin guje mata sai ta riske ki, a shawarce kada ki kara yi wa kanki horo da hakan.
Akwai abubuwan motsa jiki a gidan nan.
Ki ci abinci ki koshi sannan ki dinga motsa jikinki, Ina ganin ko kibar ta riske ki ba zata yi miki muni ba.
Sai kuma abu na gaba shine in sha Allah cikin satin nan zan turo likita za a yi miki gwaje-gwaje domin tabbatar da lafiya.
Ni ma zan nuna miki result dina don hankalinki ya kwanta na yi gwaje gwaje na tun lokacin aurena da Matata Samira Allah Ya gafarta mata.
Ni ba yaro ba ne, haka zalika kema ba yarinya ba ce, kin yi aure a k'alla har sau biyu kin san maza, ba zai yiwu a ce kina zaune a haka babu buk'atar d'a namiji ba.
Ko ba ma son juna sai mu zama abokanan d'ebewa juna kewa ko ba haka ba ne?"
'Kokari na yi na dubi tsabar idonsa kamar yadda yake duban nawa na furta." Ni ba wani namiji da yake gabana a halin yanzu, maganar kuma ba ka taba rungumar wata 'ya mace ba ko al'kur'ani zaka dafa ka rantse mini ba zan yarda ba.
Shin wai ko ka manta ni ce dai matar nan da ta zo ofis dinka ka kawo mata maganar banza.
Idan ka manta ni ban manta ba, ka neman matan banza wannan shine abinda ka nuna mini tun kafin k'addarar aure ta shiga tsakaninmu.
Ai na san ciwon kaina duk da aure-auren da na yi nasan mazan dana aura nutsatstsu ne, cikinsu babu wanda ya ta'ba kawo mini irin maganarka.
Don haka ni ban shirya yin wata mu'amula da kai ba a yanzu."
Babu damuwa a tare dashi ya ce." Ba zan rantse miki don ki yarda da ni ba.
Ban ta'ba sanin wata mace ba har yanzu idan kin yarda shikkenan idan kuma ba ki yarda ba mu tafi a haka." Ya nisa kafin ya cigaba da cewa." Lokacin dana bijiro miki da buk'atata a can baya na jarrabaki ne,domin ina neman matar aure na kasa samu dalili duk wata mace da zata tunkaro ni da manufarta.
Shigowarki ofis dina kawai na ji a raina bari na gwadaki sai aka ci sa a kika cinye.
Lokacin na ji kin kwanta mini a raina Ina jin zan iya auranki duk da ba kya daya daga cikin jerin matan da nake burin na aura.
Ashe Allah ya kaddara hakan dalilin da ya sanya kenan da Hajja ta nuna mini ke ban musanta ba, sai dai Ina ta jinjina mazan da ki ka aura shine kad'ai damuwata yadda nake saurayi nan ni ma ina so na auri budurwa domin na ji yadda ake ji."
Cike da takaici na ce." To ai hanya a bud'e take Malam sai ka auro budurwar bai dami Amina ba, yadda babu tsarin auran mace Irina a tare dakai ni ma babu tsarin auran namiji irinka domin har yanzu ban ji zuciyata tana sonka ba."
Na gaya masa hakan domin shi ma ya ji zafin da nake ji a cikin zuciyata.
Bai nuna komai ba ya kara kusanto ni yana fad'in." Shiyasa ai nace mu dinga d'ebewa juna kewa kina da sha'awa ni ma ina da ita, ko babu k'auna a zukatanmu ai akwai muradin wani lamari da Allah ya sallad'a a gangar jiki da ruhi.
Don gaskiya babu ra'ayin yin wani auran a yanzu, kuma ni ba zan iya zuba miki Ido ba bayan na san ke halalina ce, sannan Hajja na can a zaune tana jiran shekara mai zuwa ta d'auki jika, kin ga dole na yi kokarin cika mata burinta."
A sakarce na ce." Ai ni maza biyun sun ta'ba ni har na haihu, to me zaka samu a wurina, ai gwara budurwar tunda kai saurayi ne sai kuje ku gwada budurci da samartaka."
Murmushi ya yi kawai ya dubi agogon da yake daure a tsintsiyar hannunsa na hagu yana cewa." Ni dai na gaya miki cikin ko wane lokaci zan iya takarki don gaskiya ba zan iya jurewa ba.
Domin ina ji a jikina akwai wani abu da ki ke amfani dashi don fizgar hankalina zuwa gare ki, amma in banda haka ni sam mata basa gaba."
Yamutsa fuska na yi tare da kawar da kaina gefe.
A raina sai nake ta jin haushin yawan ambaton Samira da yake yi.
Ko nauyina baya ji. kuma na gano yana sonta sosai tunda ya fad'a itace first love d'insa.
Ya juya ya kama hanyar fita daga d'akin yana furta." Ni na fita ki kula da kanki."
Na ja jiki a sabule na nemi gefan gado na zauna Ina nazarin maganganun da ya yi kafin ya fita.
Ban ga alamun wasa a cikin maganarsa ba idan na yi la'akari da yadda lokaci kan'kani ya nuna kwadayinsa a kaina kamar yadda ya fad'a cikin kowane yanayi zai iya zuwar mini da bukatarsa.
Gabad'aya kaina ya kulle a yinin ranar na rasa abinda yake yi mini dadi sai sanda Yusi ya dawo daga makaranta tukkun na dan sake.
Tare muka ci abinci muna dan ta'ba Hira hana cewa duk lokacin da aka shirya zuwa duba d'an'uwansa Kamalu zai nemi izini a makaranta koda zata kasance ranar da karatu.
Shi dai koyaushe maganar Kamalu idan kana so kaga dariyarsa to yi masa zancen d'an'uwansa.
Sai na ce ai ya sha kuruminsa weekend za mu je ranar da makaranta.
To har karfe tara da wani abu maigidan bai shigo ba, abinda bai taba kasancewa ba kenan.
Duk rintsi idan ya fita magariba a gida take yi masa sai dai a wasu lukutan yakan sake fita idan ta kama.
Yusi ya damu da maganarsa karshe dai kawai sai gani na yi ya kira wayarsa da yake shi da kansa ya siya masa waya sabuwa a cewarsa zata dinga taimaka masa wurin karatunsa kuma zata d'ebe masa kewa.
Har suka gama wayar idona yana kan yaron shi ma ya dube ni Yana cewa." Gashin nan akan hanya wai ya sallami wasu baki ne da suka zo masa.
A ta'kaice na ce." To Allah Ya kawo shi lafiya.
Minti goma Sha biyar tsakani ya shigo escort d'insa a baya daya da wayoyinsa a hannu dayan kuma da 'yar jakarsa.
Kusa da Yusi ya zauna shi kuma da sauri ya k'ar'bi wayoyin dake hannun escort din nasa suka fita.
Falalu babban yaronsa da yake yi masa hidima a dakinsa ya shigo da sauri kai tsaye sama ya wuce ruwan wanka zai had'a masa.
Sau daya na dube shi na fahimci sauyawarsa domin ba haka ya fita ba.
Cikin nazarin da nake na ji Yusi yana cewa." Baba hannunka da d'umi sosai fa ko baka da lafiya ne?"
Na dubi yaron sai naga hannuwansu a sarke a wuri d'aya.