← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 276

Sashe 118

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Takuwa ji dad'i sosai da muka je gidan nata, kuma duk yadda Hauwa take d'ari-d'ari da ita sai ba ta nuna mata komai ba a fuska ba, ta sakar mata fuska kamar babu wani abu da ya ta'ba faruwa na saba'ni a tsakaninsu.

Sosai na ji dad'in ganin yadda suka samu daidaito da fahimtar juna.

Muka rabu cikin girma da mutunta juna ta yi mana alheri sosai tunda dama can a sanin da na yi mata itama hannunta a bud'e yake.

Bayan komawarmu da kwanaki uku na kira Hamusu a waya na ce masa ya fitar da kudi ya kuma nemi kwararrun ma'aikatan da za su gyara gidana na kuntau sannan ya sayi set din kayan d'aki da kujeru da gado labuleye masu kyau ya sanya a shirya gidan.

Idan komai ya kammala kawai ya kaiwa Sahura mukkulin na mallaka mata shi gabad'aya tunda dama takardun suna hannunsa sai ya bata.

Shi kansa ya taya ta murna sosai ya kuma bani tabbacin zai kammala komai a cikin sati d'aya.

To mun yanke shawara har da maigidan kan cewa tare za su sake komawa da Hauwa saboda yanayin garin koyaushe cikin ruwa ake yi duk da gidansa ya sha bam-bam da sauran gidajen da suke garin legos amma dai hankalinsa ya fi kwanciya da mu zauna anan abuja zuwa wattani shida lokacin yaran sun yi k'wari sosai..

Na ji dadin hakan sosai kuma na yaba da yadda suke nuna mini kulawa dashi da matarsa.

Sai dai tunda muka yanke wannan shawarar nake cin 'kaniyata a hannunsa duk ranar girkina nakan ji jiki kwarai da gaske baya daga mini 'kafa, idan na yi magana sai ya ce abinda ma ya kusa tafiya.

Haka na yi ta hakuri dai har ya kammala musu shiri suka tafi sannan na samu sa'ida.

Cike da mamaki Sahura ta kira ni a waya tana tambayata wai Hamusu ya kai mata mukulli da takardun gida in ji ni, na ce mata 'kwarai kuwa gidana na kuntau na mallaka mata halak malak.

Sai ta rasa bakin magana ta yi shiru ta kasa cewa komai ba.

Sai da na sake yin magana tukkuna na ji sautin muryarta cikin rawa kamar za ta yi kuka tana yi mini godiya na ce kin wuce haka a wurina Sahura dukiyata taki ce kuma ki shirya zuwa umara in sha Allahu farkon Azimi maigidan ya baku kyautar kujera ke da Anti Yagana da Baba Sule.

Sai ta fashe da kukan da take ta b'oyewa na kashe wayar ina dariya da mamakin kukan da take yi a ganina ai Sahura ta wuce duk wannan abin a wajena yadda nake jinta a raina kamar anti Yagana da muka fito ciki d'aya.

Gudun aure littafine na kudi ki ji tsoron Allah ki biya ni hakkina kafin ki karanta
Ubangijina ya jarabce ni da abubuwa da yawa a lukutan baya wanda har nake ganin kamar ni kadai ce nake cikin masifa da ibtila'in rayuwa.

Na yi kuka kamar ruwan idona zai tsiyaye yadda na ji dad'i na kuma godewa Allah shine ban ta'ba had'a Allah da waninsa ba, shi kadai na k'adaita na kai kukuna wurinsa domin kuwa nasan shine mai iko da kowa.

Allah na gode maka wannan kalmar ba zata ta'ba yankewa daga bakina ba har na koma ga mahallicina.

Yadda Allah Ya kar'bi adduata a yau da Kamalu yake zaune a gabana cikin Kamala da suttura tare da tsantsar nutsuwa da wadataccen ilimin Islama a tattare da shi.

Kamalu ya girma ya zama saurayi mai tattare da tsafta nutsuwa da ladabi.

Ban iya daurewa ba rungumeshi na yi sosai a jikina ina kuka ina tuna mahaifinsu har shi ma ya kasa daurewa ya fara taya ni Baba Tabawa dake goye da Hassana a bayanta ta fito daga kicin da saurin domin sautin kukan namu har can ta tsaya tana ba ni baki wai na daina yin kuka Allah ya kamata na godewa domin duk abinda yake faruwa hukuncinsa ne.

Da kyar na yi shiru shi ma ya rike hannuna gam ya kasa saki.

Cikin wannan halin Yusi da Adam suka shigo domin lokacin da aka kawo mini Kamalun ba sa nan.

Wani tsalle Yusi ya yi ya rungumeshi suka fadi a wajan Adam ya dinga yi musu dariya.

Shi ma Kamalun dariya yake yi wa Yusi ganin yadda duk kwalla ta cika kwarmin idonsa.

Ya dube ni yana tambayata wai wane irin abinci Yusi yake ci ya kumbura irin haka, ko bashi da lafiya ne.

Na ce masa lafiyarsa lau hutu ya samu da jin dadi.

Adam dai yana tsaye yana ta dariya da yake yaro ne mai sakakkiyar fuska kamar ta Mamansa.

Kamalu ya gyara hannun rigarsa ya daga k'wajinsa na hannun dama duk a mur'de ya dubi Yusi yana cewa ka ga ni da nake cikin hatsi ina kuma aikin gona da motsa jikina dubi kwanjina malam haka ake son namiji ya kasance.

Adam ya ce abinda ake gaya masa kenan amma kullum sai ya ci nama ya zuba suga da madara da vombita da yawa ya tea Momi na bashi goyan baya.

Yana dariya yake cewa ku raka ni na je na gaishe da Momi ni ma." Ya mike tsaye ya shiga tsakiyarsu suka kama hanyar fita.

Ni da Baba Tabawa muka bi su da kallo cike da wani irin farinciki a zukatanmu bakid'aya.

Abin mamaki da d'aure kai.

Tun ina tsammanin dawowar Kamalu har na cire rai domin kuwa sha daya na dare har ta gota.

Zuciyata ta shiga yi mini nazari ko kallo suka yi ne, ko kuma dai yaran sun d'auke masa hankali sam ban kawo cewa matar gidan ce ta hana shi dawowa ba sai da na kira ta a waya na tambayeta tukkuna kai tsaye ta ce mini zai kwana cikin 'yan uwansa ne.

Mamaki mai yawa ya lullube ni amma ban iya cewa da ita komai ba muka yi sallama har tana cewa a shafa mata kan twins.

Da zullumin lamarin na kwana a cikin raina.

Don haka gari yana wayewa ban yi kasa a gwiwa ba na kira maigidan a waya da muka gaisa na gaya masa fa makaranta sun sallamo Kamalu yanzu haka muna tare da shi anan abuja jiya Ayuba ya kawo mini shi.

Sai ya ce ai Hamusu ya kira shi a waya ta gaya masa.

Daga can makarantar ma sun sanar da shi.

Na ce zai yi sati sati daya anan domin mun gama yanke magana da Hamusu zai zauna a can wurinsa domin dora shi akan harkokin da muke yi.

Bud'ar bakinsa sai ya ce bai amince ba dama ai tuntuni ya gaya mini idan yaron ya dawo zai had'ashi da d'an uwansa su tashi tare .

Idan kuma ina ganin hukuncin da ya yanke bai yi mini ba sai na yanke nawa tunda duka 'ya'yana ne.

Na dinga kokarin nusar da shi hakkin da dangin ubansu suke da shi akan yaran, idan fa magana za a yi ta gaskiya yana da kyau a ce suma an basu damar yin abinda suke so da yaran.

Ya fahimci dalilina amma sai ya mayar da abin rigima .

Ganin haka ya sanya na kashe wayar raina a b'ace.

Ni wannan 'karfa-'karfa da ake yi mini akan yarana ya fara isata wallahi duk na gane take-takensa shi da matarsa wata'kila ya yi mata kyautar yaron tuntuni ban sani ba, tunda haka ya bata Yusi ba tare da neman izinina ba.

Wannan lamari ya janyo mana sa'insa sosai a tsakaninmu, wanda har sai da na gaza ha'kuri ina kuka na kira Hajja na gaya mata ta yi masa magana ta ba ni ha'kuri sosai ta ce za ta sanya a kira mata shi a waya.

Ranar kuwa da suka yi waya Baban Saude ya kira ni tare da rufe ni da fad'a irin wanda ban ta'ba tsammani ba.

Shiru kawai na yi Ina sauraransa wato tunda na kira mahaifiyarsa to shi ma bari ya had'a ni da nawa iyayen.

Baban Saude ya gama nasa fadan.

Anti Yagana ma ta kira ni tana yin nata tana ce wa ba ni da wato har yanzu kuma har yanzu na kasa gane irin k'aunar da mijina yake yi.

Idan duk zai d'auki yaran da zan haifa ya bawa matarsa ai ta cancanta ne tunda kowa ya shaida ita din uwar marayu ce.

Har da Allah Ya isa ta yi mini idan na kuma tashin maganar da kanta zataje ta yi wa Gwaggo bayani tana da tabbacin samun goyon baya da amincewa daga wurinta.

Kuka na ci na 'koshi na ha'kura na kyalesu kullum dai da safe suna shigowa mu gaisa.

Shi ma kuma kamalun ya fi sakewa a can saboda yaran don ma shi Salim yana can saudiya yana 'dora karatunsa sai 'yan yaran Nusaiba Sahib da Yasmin da ake kawo su duk ranakun weakened.

Kiran Hamusun na yi a waya na yi mass bayani duk yadda al'amirin ya juye.

Sai ya dinga dariya cike da nuna rashin damuwarsa yake ce mini wannan ai ba wani abu ba ne hakan ma da aka yi daidai ne da kuma hujja mai k'arfi.

Dole na ha'kura na zubawa sauratar Allah Ido, amma kuma ban ta'ba nunawa matar wani abu a fuska ba, dalili ta wuce na ya'keta akan komai ba, wanda ya riga ya ce yana son naka ai kai yake k'auna.....

Tofa wata sabuwa
Shin wai mai Hajiya Maryam take nufi ne, alheri ne ko kuma sharri Allah ne kadai yasan abinda yake cikin zu'kantan bayinsa.....

Muje dai zuwa.
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.

Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*79*
'Kwarai na danne hakan a cikin raina domin duk 'kwa'kwata na kasa gane abinda yake cikin zuciyarta dalili koyaushe alherinta a gare ni ru'banya yake yi.
Chapter 118 · 0% Book details