← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 228 OF 276

Sashe 228

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wajan uku saura na kintsa jikina sosai kwalliya na yi irin wadda na jima ban yi irinta ba na zuba lece brown a jikina wanda ya ji stones ta ko'ina ga kyau ga kudi na yi amfani da set din gold dina da ban jima da saye ba.

Tare muka ci abinci da yarinyar kamar koyaushe tana yi mini hirar 'yan uwanta da alama ta yi kewarsu nasan duk yadda aka yi sun iso yanzu suna gidan Hajja.

Ina idar da sallar la'asar ya kira ni dama dakon kiran nasa nake yi domin na ji a ina a akwana.

Ya ce mini an d'aura amma Malam D'aha ya ce angon ya je yana nemansa.

Yadda yake magana kamar wanda aka yi wa dole ni ma na amsa da kalar sigar da yayi mini
Ya nisa kafin ya sake magana." Ga ni nan a kan hanyar dawowa gida."
A takaice na ce." Sai ka dawo."
Na riga shi kashe wayar ban jira ya sake wata maganar ba.

Kai tsaye Babanmu na kira dama da safe na sanar da shi halin da ake ciki ya ce tunda mijina ne zai kar'bi auran to a bashi dama zuwansu ba shi da amfani dalili ga yadda lamarin ya kasance amma bayan d'aurin auran za su je wajan malamin domin godiya.

Na sanar da shi an daura sannan na tabbatar masa da cewa zan shigo gidan gobe domin mu tattauna da mahaifiyarsa akan yadda za a shirya hidimar biki."
Ya yi ta yi mini godiya da sanya mini albarka Ina kara jin k'warin gwiwa a cikin zuciyata tare da addu'ar Allah Ya taimake ni na cigaba da tallafar 'yan uwana.

Muna gama waya na kira angon na gaya masa cewa an daura ya kuma zo da daddare ina son ganinsa domin mu yi magana akan abinda ya rage na aikin gidansa da yake ginawa.

Mun jima muna waya da anti Yagana tana fad'in idan mun tsayar da magana na kira ta na sanar da ita halin da ake ciki.

Na sauke ajiyar zuciya tare da kashe wayar bayan mun gama da ita.

Kiran sa ya sake shigowa a karo na biyu na daga amma ban ce komai ba.

Na ji yana fad'in." Kashe mini waya ki ka yi saboda me?" Na yi shiru kawai sai ya cigaba da cewa."
abubuwan da ki ke yi mini sun ishe ni wallahil-azimin zan d'auki mataki mai tsanani a kanki Amina."
Shiru na yi ban iya ce maaa komai ba ganin yana neman fitina a irin wannan lokacin da ya kamata a ce ya kasance cikin walwala a yadda yake nuna 'kunci da damuwa a baya amma kacokan yana neman ya huce takaici a kaina shin wai ko dai yana son yarinyar nan dole ta sanya shi ha'kura saboda rashin daidaituwar jini wannan abubuwan da yake yi sun fara sanya mini zargi da shakku a kansa tunda ai zuciyarsa a kirjinsa take ba a bayyane take ba balle mu ga abinda yake 'boyewa kamar kishi yake yi.

Ya karaci maganarsa ban ce komai ba haka ya ha'kura domin duk yadda ya kai ga so na gaya masa da wanda nake waya har na katse tasa ban gaya masa ba na kyale shi dai ya shigo gidan sai mu yi wacce za mu yi ai waya ta yi kad'an.

Har bayan isha'i bai shigo ba na fi zargin yana gidan Hajja dalili Hauwa da yaran kuma tare za su kwana tunda nan ta zo ta same shi.

Usaini ya zo kamar yadda na umarce shi yaro sai annashuwa yake yi ya nuna mini kara da hallaci kwarai ya kar'bi abinda bai ta'ba ganinsa da ido ba cikin girma da mutunci wannan dalilin ya sanya mini sake d'aukar al'amarin da muhimmanci kwarai da aniya.

Ya nuna mini gidan nasa a waya ya yi nisa sosai don an yi rufi an sanya k'ofofi a wasu d'akunan da yake filin babban ne part biyu ya yi yana gaya mini d'aya bangaran zai sanya Babarsu ne idan ya gyara mata sai na ce masa mu fara gyara na amarya tukkuna duk abinda ya kamata na ado da k'awata a gida a yi lissafi da ma'aikata daga nan zuwa ranar wata juma'ar a yi kokarin kammalawa domin ba ni son yarinyar ta yi dogon zama a gidansu.

Muka yanke magana a kan haka.

Hamusu na kira a lokacin na ce ya had'a masa lefe akwati shida a sanya manyan kaya daga kan atamfofi zuwa leces abinda ba mu da shi a shago a sayo a had'a a kawo mini na gani.

Ya ce mini za a yi kokarin hadawa kamar yadda na buk'ata.

Muna tare da Minal a falo wajan tara da minti goma na dare ina dokon shigowarsa yaran sune a kan gaba kafin su shigo shi da ita.

Minal ta buga tsalle a guje ta nufi bakin kofa suka rukunkume juna Hassana da Husaina suna cikin wasu 'yan kanti sabbi masu kyau sosai da wani karamin hijab a wuyansa daga inda nake zaune nake k'are musu kallo na ga sun sake yi mini tsayi ko dai don na kwana biyu ban gan su ba ne oho sun dai yi mini kyau k'warai Khalil na cikin shadda riga da wando da aiki a gaban rigar har da hula a kansa.

Ita kuma tana cikin abaya baka mai jajayen dutsuna ta yafe mayafinta a wuyanta har da gilas baki a idonta da jar jaka da taka
lmi.

Na juyar da kaina cikin nutsuwa na amsa sallamar da ta yi suka 'karaso falon ita da yaran gabad'aya shi kuma ya haura sama ba tare da ya ce komai ba.

Ta zauna kan kujerar da take fuskantata fuskarta a sake kamar ba itace Hauwa mai k'uncin rai ba.

Ta zare gilashin idonta tana duba na sosai ta ce."Amina ina yini mun same ku lafiya."
Na amsa a tak'aice ina nazartarta.

Sukairaju ya shigo ya tsaya daga bakin kofa akwati biyu ya ajiye madaidaita don basu da girma kayansu ne a ciki daga nan ya juya ya fita da sauri.

Hankalina ya d'auke wajan amsa gaisuwar da yaran suke jero mini Usai ta zo ta dafa cinyata tana ta kallona sai kuma ta dora kanta a saman cinyata.

Na dora hannuna a kanta ina le'ken fuskarta.

Hassana cikin narai-narai da ido ta ce."Mama ki ka ce za ki dawo gobe."
Ta fadi maganar muryarta tana rawa kamar za ta yi kuka lokacin na tuna da alkawarin bogi da na yi musu a lokacin ma tun ina maiduguri.

Na ri'ke hannunta amma ban ce mata komai na kira Khalil da hannu Ina fad'in ."Zo mu sake gaisawa."
Ya kuwa taho da sauri yana dariya yake fad'in.

Mama mun yi kewarki fa sosai kullum muna labarinki shiyasa da muka zo muka ce mu dai nan a wajenki za mu kwana."
Na ce." Ni ma na yi kewar yarana sosai Khalil ina su Mairo baba Tabawa da Sultan."
Ya ce." Duk suna nan lafiya sun ce a gaisheku Sultan ba shi da lafiya yana zazzabin hak'ori Baba ya ce a bar shi a gida kada a zo da shi."
Na gyada kaina ina dubanta lokacin da take yin magana cikin yar dariya ." Aikam yara sun yi kewarki a gida Amina shi kansa ma gidan kewarki yake yi."
Murmushi na yi ina duban Minal da wayata a hannunta tana latsawa ko kusa da uwar ba ta je ba gefe guda kuma ina nazarin abinda yake so ya faru domin ga dukkanin alamu ba yaran ne kadai suka zo mini kwana ba har da ita tunda ga akwatin kayansu nan."
Na danne tare da furta." Kun ci abi
ci a gidan Hajja ko kuwa na kawo muku."
littafin nan na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba
Ita ta ba ni amsa duk da ba ita na tambaya ba na ji tana cewa." A alhmdullhi ai sai da muka ci abinci muka fito mun gode sosai."
Na yi shiru ban tanka mata ba ina ta sauraran labarin Mairo a bakin yaran da sa'kon gaisuwar da suka ce a gaya mini.

Wajan goma daidai na tashi na hau saman domin tunda ya hau bai sauko ba ga yara suna so su kwanta.

Yadda tsarin gidan yake dama can babban falo ne da dakuna manya biyu a cikinsa toilet da kicin wanda yake d'auke da store wadatattu.

Saman kuwa dama can d'akuna biyu ne amma daya ne a gyare wanda yake mu'amula a cikinsa tun farkon tarewarta a gidan zaman mace daya ne babu takurawa yanzu kuma Khalil ya zama d'an saurayi ya d'an fara girma babu buk'atar a had'a shi da mata a d'aki daya tunda tun can abujan aka raba musu d'aki.

Yana zaune da jallabiya a jikinsa ya yi wanka yana waya shigowata bata hana shi cigaba da wayarsa ba amma kafatanin hankalinsa yana kaina har na zauna daga dan nesa da shi waya yake yi da Alhaji Sulaiman yana yi masa bayanin yadda al'amarin ya juya har aka d'aura auran da waninsa ya yi masa fatan alheri a yayin da yake ta amsawa da Amin Amin can kuma sai ya yi shiru yana sauraransa na ji yana fad'in." Anya kuwa Alhaji ba dai yanzu ba tukkuna wad'annan ma fama nake da su amma za mu cigaba da neman zabin Allah."
Daga haka suka yi sallama ya juyo yana kallona 'kuri!

Na sake tamke fuskata tare da tariyo maganganun da ya gaya mini dazu amma bari mu ajiye wannan mas'alar a gefe kafin nan ina so na ji dalilin da ya sa ya kawo mini matarsa cikin gidana bayan da bakinsa na ji yana gaya mata babu waje a ina zai sauke ta.
Chapter 228 · 0% Book details