← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 276

Sashe 84

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan Isha'i ya d'auke ni a mota da kansa ya yi direving din motar muka nufi asibiti a can muka samu Yusi tare da matasan yaran suna zaune kusa da gadon da mahaifin nasu yake kwance ko'ina na jikinsa sa'kale da na'ura yana ta kokawa da numfashi
Gaskiya dan adam ba abakin komai yake ba idan ma kana d'aukar kanka kai wata tsiyane wallahi gwara ka yi karatun ta nutsu domin Allah ne mai sarrafa al'amura gashi dai da kudin wanda da yawa muke ganin kamar sune karshen jin dadi bayan ba haka ba ne mai lafiya shine d'an gata domin kuwa duk wanda Allah ya wadata da lafiya shi ya yi wa arziki..

Ita da yaranta sun ba ni tausayi kwarai da aniya kuma yanzu na sake gazgata maganar da ya yi mini jiya a waya cewa suna mugun tsananin son junansu shiyasa gabad'aya ta susuce!

Ta kasance kullum cikin zubar da hawaye...Da kyar ta iya amsa gaisuwata hankalina gabad'aya na kan maigidan nata da ko yatsansa baya motsi shi kansa na lura da kid'imewarsa da likita ya shigo suna magana yake tambayarsa ya ga an sake sanya masa oxygen bayan jiya aka cire ta kuma numfashinsa ya daidaita likitan ya ce masa ciwon ne ya sake tashi d'azu da yamma amma kuma numfashin ya fara daidaita ba kamar d'azu ba.

Ya sake duba shi ya fita shi ma da yake likita jikinsa a mace balle ga mu da muke zaune.

Sai wajan goma da wani abin muka bar asibitin cikin damuwa da zullumi domin kukan da Hajiya maryam din take yi ya ta ba mu gabad'aya har dashi gabad'aya yanayinsa ya canza shi bai yi na hawaye ba yana na zucci irin mai mugun cin ran nan.

Na d'auka damuwar da yake cike ba zata bari ya nemi wata buk'ata ba.

A daran bai iya bacci ba sai da ya kwanta da ni irin kwanciyar da na ji jiki a hannunsa har abin ya fara ba ni tsoro ganin yadda ya 'kirkiro wani style wanda ba mu ta'ba yin irinsa ba.

Ban fahimci komai ba sai wahala saboda bai jima yana yi mini wassanin soyayya ba ya fara gudanar da abinda ya kud'irce a cikin ransa wanda tun ina yi masa kawaici har dai na gaza ha'kuri na gaya masa fa bana gane komai sai zafi da ciwon cinya.

Ya ce shi kuwa atafau ta haka yake so ya yi don ya fi jin dadi.

Haka nan na ha'kura na kyaleshi ya dingi yi tamkar wani sabon angon da ya jima yana shan sassa'ke.

Wallahi kasa juriya na yi don duk fitinata wannan lamarin ya sha kaina kamar da zalinci a ciki.

Ashe lumbu lumbu ya yi mini na zo hannu ya yi mini 'keta kuka kariris na dinga domin ya rabu da ni yana fad'in bai gama ba tukkuna.

Da ya gama kuwa sai da na yi ruwan d'umi sannan na ji sasaauci na nemi waje can nesa dashi na kwanta cinyoyina suna ta ciwo.

Na jima kafin bacci ya kwashe ni ina ta kallonsa yana baccinsa hankalinsa a kwance.

Can gefin asubahi kiran da ya shigo wayarsa ya tashe mu gabad'aya a zabure ya lalubi wayar yana dubawa da sauri yasa a kunnansa yana fad'in." Alhaji Jamil....."Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! wannan kalmar ce ta fito daga bakinsa bayan ya gama sauraran maganar mai kiran wayar wanda na ji ya kira shi da Alhaji Jamil.

Dama a wasu lukutan mutuwa takan nuna kama kafin wa'adin ya cika.

Ni dai dama ganin da na yi wa Alhaji Amadu a wannan dare na sare domin gwiwata a sanyaye muka fito daga asibitin lokaci kawai yake jira amma alamun sallama da duniya ya gama bayyana a tattare dashi.

Alhaji Jamil k'anine ga Alhaji Amadu tare suke ta tiriri dashi shi k'aninsa ne uwa daya uba daya shi kuma abokinsa ne tun na 'kuruciya abokin da akayi gwagwarmayar rayuwa.

Mutuwar Alhaji Amadu ta dake shi mutuka gaya domin ni sai na ce tunda na tashi daga kuruciya da girma ban ta'ba ganin kukan babban mutum kariris irin haka ba.

Na fahimci ya yi kokari sosai wurin ganin ya danne kukan amma hakan bai samu ba kuka ya dinga yi sosai amma ba mai gunji ba yana nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! lamarin ya tsoratani sosai wanda hakan ya sanya ni ni ma fashewa da kukan domin na rasa yadda zanyi na rarrashe shi.......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.

Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*57*
Shine akan gaba wajan shirya Alhaji Amadu har aka kaishi gidansa na gaskiya, haka ya dinga kai kawo har ya ba ni tausayin da na ji kwalla ta cika kwarmin idona.

Tabbas Alhaji Amadu ya wuce aboki a wurinsa sai da d'an uwa, domin tun a daran kafin gari ya waye ya dinga gaya mini irin gwagwarmayar da suka sha duk domin tsayuwa da kafafuwansu.

Marigayin ya riga shi auran fari kusan shine ma ya yi masa rakiya ta angonci kuma tare suka dinga jigilar zuwa jos neman auran Maryam din har dai Allah Ya tabbatar da auran.

Shekaru kusan goma sha biyu da auransu ne shi kuma ya yi auran fari Samira kenan Allah kuma ya dinga wanzar da ikonsa.

Ni kam da babu sha'kuwa a tsakanina da Hajiya Maryam ban nuna bak'untata ba mijina abokin mijinta ne sannan yarona yana tare da nata yaran ta ri'ke gabad'aya dalilin da ya sanya kenan na shiga cikin 'yan uwanta na zauna tare dasu har dare muna kar'bar gaisuwa a tare.

Na sake yin karatun duniya sosai domin mutuwa wa'azi ce ga duk wani mumini na kuma tausaya mata kwarai da aniya ganin yadda ta zabge ta ki'dime a lokaci d'aya babu shakka mutuwar miji wani babban rashi ne da har abada ba za a ta'ba maye gurbinsa ba.

Sai wajan tara da arba'in tukkuna na shiga gida tunda muna kusa da juna amma ban tafi ba tukkuna sai da na tabbatar da cewa ta ci abinci domin yini guda babu abinda yake cikinta babu irin rarrashin da ban bakin da ba a yi mata ba tace ba zata iya cin komai ba.

Itace babba a cikin 'yan uwanta shiyasa da suka gaji da rarrashinta suka ha'kura dalili duk ta girmesu iyayensu kuma basa raye itace ke ri'ke da ragamarsu gabad'aya ni ma na tabbata don tana jin kunyata ya sanya ta kar'bi abincin da na hada mata da hannuna ta dinga ci kamar magani tana goge hawayen da suka ki daina fita daga idonta.

Bai shigo ba sai wajan sha biyu saura shi Yusi yana can dama lokacin da ya shigo din har na yi shirin kwanciya amma ban kwanta ba din tukkuna ina dakkon shigowarsa.

Littafin gudun aure na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Wanka ya fara yi tukkuna ya same ni a zaune a gefan gado ya zauna kusa da ni.

A nutse nake dubansa gabad'aya bashi da kuzari na ce." Sannu baba ya karin ha'kuri?"
Ya amsa da "Alhamdulillahi yana dan duba wayarsa ya ce." Gobe su Hajja suna tafe tare da Hajiya Saratu da sauran 'yan uwan mahaifina."
Na ce." Ubangiji Allah ya kawo su lafiya amma ka ci abinci kuwa?"
A nutse ya ce" Na ci amma ba mai yawa ba."
"Ko kana buk'atar wani abu yanzu wanda sai sanya cikinka ya dan yi nauyi."
"Wannan towon naki nake sha'awar ci irin wanda ki ka yi mini a gidanki amma dare ya yi yanzu za mu bari da safe sai ki yi mini ko?"
Cike da kulawa na ce." Muddin da akwai duk abun bu'kata yanzu ma sai na yi maka har da d'umame ai ba wani abu ba ne."
Ya girgiza kansa yana yi mini wani irin kallo ya furta." Ba ni da imani sai na sanya ki aiki da wannan dare duba lokaci fa sha biyu har ta gota."
A nutse na ce." To ai aikin lada ne?"
Ya d'an jima yana kallona kafin ya girgiza kansa da cewa." Ki huta kawai na gode."
Jikina ya d'an mutu da yawan kallon da yake yi mini wanda na kasa tantance na menene na soyayya ne ko na wani abin ne.

Wayarsa yake latsawa kafin yasa a kunnansa ban tsammaci da Hauwa yake waya ba sai da na ji yana fad'in." Kin fi kowa sanin matsalar hakan tunda ma'aikaciyar lafiya ce ke to me zai sanya kuma ki aikata, idan kika zubar da cikin ai mun huta gabad'aya tunda ke ba za ki yi aiki da abinda ki ka sani ba."
Ban ji abinda take ce masa ba.

Ya ce." Ina cikin jama'a ne sosai muna kar'bar gaisuwa abokin nan nawa Alhaji Amadu ne ya rasu nasan zuwa yanzu kin samu labari ko ta kafafan sadarwa ne dalilin da ya sanya kenan ban samu damar amsa kiranki ba gashi yanzu da na nutsu na kira ki da kaina."
Shiru ya yi yana sauraranta har ta gama yi masa magana cikin kuka wanda nake jin sautinsa kad'an kad'an.

Ya ce." To shikkenan a d'aure mahaifar idan hakan shine solution ai kin fi kowa sanin hakan tunda ajikinki take gobe ki je asibiti da wuri ayi miki aikin Allah Ya sawwa'ke."
Ya kashe wayar da damuwa a tare dashi.

Ni ma sai na ji hankalina ya tashi wato dai muddin kana raye a duniyar nan ba zaka huta ba.

Bai gaya mini ba amma na fahimci kadan daga cikin abinda suka tattauna cikinta ne yake barazanar zubewa.
Chapter 84 · 0% Book details