Sashe 237
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta dawo da leda viva mai zurfi tana fad'in wannan ai zata d'auke kayan ko?"
Na kar'ba Ina fad'in." Eh za ta isa."
Ta zauna saman kujera tana cewa." A kar'ba da hakuri ban samu zuwa biki ba amma wannan a bawa amarya Hajara idan na sanya rana Yusi zai kai ni gidan na yini in sha Allahu."
Na sa dariya ina fad'in." Kai Hajja an yi abu ya wuce fa don Allah da kin bar atamfofinki ki dinka abinki."
Ta girgiza kanta tana murmushi ta ce." A a dama na yi niyya Amina sai ki sanya Ayuba direbanki ya kai mata ko kuma angonta ya zo ya kar'ba a ce babu yawa kuma ina yi musu fatan alheri."
Na ce." To shikkenan Hajja Allah Ya saka da alheri ya kara girma Ubangiji Allah Ya sa a fi haka, mun gode sosai."
Ta amsa da kulawa tana kallona kafin ta ce." Ya gaya miki Kamalu zai tafi karatu can Madina ko?"
Eh ya gaya mini." Na fadi haka duk da har yanzu bai ce mini komai ba.
Sai ta gyada kanta tana cewa." Ki kara yi wa yaron nan addu'a akwai alamun haske a cikin al'amarinsa in sha Allahu za a amfana dashi."
Na furta." In sha Allahu rabbi Hajja na gode Allah Ya saka da alheri."
Ta yi murmushi ba ta ce komai a daidai lokacin ne kuma ya shigo yana waya ya tsaya tsakiyar falon duk muna kallonsa har sai da ya kammala tukkuna.
Ya dube ta yana fad'in." Hauwa ce ta kira waya wai Sultan baya jin dad'i."
Hajja ta ce." Ashsha me yake damunsa?''
Ya gyada kansa da Yar damuwa ya ce." Ciwon ciki abinda dai tace kenan ya kwana biyu bai yi bayan gida ba yana ta kuka uwar rainon nasa ce ta je tana gaya mata halin da yaron yake ciki amma ya sha magani a cewarta."
Hajja ta ce." Wata'kila wani abin ya ci ya dam'ke masa ciki sai an kula da abinda za a dinga ba shi ya ci mussaman abinda ya danganci madara da fulawa."
Ya furta." Sauyi ne kawai tunda yaron ya fara cin abinci bai ta'ba irin wannan ba ko ba haka ba ne?"
Ya fad'a yana kallona na ce." Sosai kuwa kuma Baba Tabawa na kula kwarai da gaske da abincin da zai ci, tana kokari a kansa gaskiya.
Ta ce." To shikkenan Allah Ya sawwa'ke ai tunda ya sha magani da sauki cikin zai saki zuwa dare sai ka kira waya ka tambayi jikin nasa."
Ya ce." Hakan za a yi in sha Allahu, ni ma ai ina tunanin jibi zan koma."
Ta gyad'a kanta tana cewa to babu lefi ai tunda an yi uku sai kowa ya koma bakin aikinsa."
Ya dube ni cikin kulawa yana fad'in." Tashi mu tafi."
Na tashi da bismillah tana fad'in." Sannu ai gwara ki zauna nan din Amina ki haihu ni kaina hankali zai fi kwanciya."
Da sauri ya ce." Ai ba sabuwar haihuwa ba ce Hajja."
Ta ce." In ji wa? au! haihuwa dama akwai sabuwa da tsohuwa ina ce idan ta yi nisa ne ma ake jin jiki, ko makaho ne ya dubi yarinyar nan ya san tana cikin ibada."
Ya yi shiru bai ce komai ba amma gabad'aya jikinsa ya yi sanyi a haka muka yi sallama ta rako ni har farfajiyar gidan lokacin shi tuni ya shige mota.
Ade ya bude mini kusa da shi na zauna da ledar atamfofin Hajara da madaidaicin fulas din towona.
Ina zama a gefansa ya kar'bi ledar ya ajiye kasan k'afafunsa saboda kayan sun yi mini yawa a hannu
Ade ya shiga mazauninsa muka d'auki hanya.
Har muka isa gida bai yi magana ba.
Ya rage walwala da nishadi ya yi shiru abinsa tabbacin akwai abinda yake damunsa.
Na daure na fara tambayarsa ko ba ya jin dadi ne ya ce dani 'kalau yake gajiya ce kawai.
Ko da na yi masa tayin towon ma kafin mu kwanta ya ce a a shayi kadai zai sha shima cikinsa ya b'aci.
Na kyale shi kawai na zauna na ci towona na koshi na sauka da kayan na dawo na same shi yana waya da Hauwa jikin yaron yake tambayarta ga yanayin fuskarsa amsar da ta ba shi ba mai dadi ba ce.
Raina ya ba ci sosai wai shin ya ma aka yi Hauwa ta san yaron ba shi da lafiya ne abinda ba tare suke ba, ba fa da gaske ba ne karya take yi ta mayar da shi shashasha tana daga masa hankali saboda ta gane lagonsa akan yara yake yau tace wannan gobe tace wancen kwanaki ta bugo waya tace bata da lafiya yau kuma ta kirkiri ciwo ta d'orawa yaro wane irin jahilci ne wannan.
Ta gama gane damuwarsa akan yara shiyasa take amfani da wannan dama.
Gashi muna cikin farinciki da soyayya da kulawa lallai sai ta rusa hakan ta kira shi ya dawo wajenta shine hankalina zai kwanta.
Na bude baki ina fad'in." Idan ba ka farga da wuri ba wallahi Hauwa daf take da ta mayar da kai sakarai ko ma nace ta mayar da kai tuntuni shashasha take kallonka."
Ya dube ni da b'acin rai yana cewa." Wace irin magana ce wannan Amina ana 'karyar ciwo ne?"
Na ce." Tunda ba ta da hankali ita don ta yi hakan ai ba abin mamaki ba ne, watarana za ta iya kiran ka ta ce wane ya mutu tunda jahila ce."
Ya yi sakato yana kallona ni ma ina kallonsa na ce." So take yi ka koma gare ta domin ku cigaba da cin amarci a sabon gida, na gaya maka Hauwa ba za ta ta'ba canzawa ba kuma ba zata zauna da ni tsakani da Allah ba sai ta yi mini bita da 'kulli a rayuwata me na tsare mata."
Ya yi shiru kawai yana kallona na cigaba da cewa."Ka yarda ko kada ka yarda Hauwa 'karya take yi Sultan lafiyarsa lau."
Ya ce." Na ji, ke yanzu abinda ki ka yanke a ganinki daidai ne na gaji da wannan abin da ki ke yi mini ni nake auranki ko ke ki ke aurana?"
Da mamaki a tare da ni na ce." Me kuma na yi maka yanzu, gaskiya na gaya maka na ce ka farka ka kuma yi aiki da tunani akan abinda matarka take yi."
Ya ce." Ni ba wannan ne damuwata ba so ki ke na kwanta ki taka ni shine karshen so da kulawa da tarairaya me zan yi miki kuma abinda ya rage kenan."
Sai kawai ya kwanta ruf da ciki ya mike sosai yana fad'in." Ta shi ki hau ki bi ta kaina kawai Amina, hakan zai kara tabbatar miki da cewa kin gama da ni, sai abinda ki ka gindaya mini."
Dariya ta kama ni amma na danne ban yi ba sai na kasa gane dalilin wannan rikicin da ya bijiro da shi a yanzu ban sani ba ko maganar da mahaifiyarsa ta yi a d'azu ce ta 'kara fusata shi shine ya sar'kafe maganar ya had'ota da wata a ganinsa kenan na mallake shi juya shi nake yi."
Na sassauta sosai tare da cewa." Ni dai don Allah ka tashi kada ka sanya mala'iku su tsine mini me ya yi zafi zaka kwanta kace sai na taka ka."
Ya ce." Kin san Allah ba zan tashi ba Amina sai kin bi ta kaina kin wuce hakan zai kara tabbatar miki da cewa kin gama da ni, haba don Allah na gaji wallahi rayuwarki kawai ki ka sani ni ko oho, ki tashi kawai ki yi yadda na umarce ki."
Na yi kasa'ke ina kallonsa har yanzu yana kwance ruf da ciki.
Na ce." To ai kamata ya yi ka gaya mini abinda na yi maka sai na baka ha'kuri ba wai ka kwanta ka ce na taka ba, akan wane dalili."
Yana daga kwancen ya ce." Sai na gaya miki ga abinda ki ka yi ke din yarinya ce, ai duk abubuwan da ki ka jima kina aikata mini kin sani, tunda ba k'ank'anuwa ba ce."
Na yi shiru kawai ina kallonsa saboda bakina ya mutu ma gabad'aya ya juyo da fuskarsa yana kallona har yanzu babu wasa a tare da shi ya ce." Ba za ki tashi ki taka ni ba."
Na girgiza kaina a tsanake na ce."Babu halin hakan me yasa zan taka ka Allah kada ya nuna mini wannan rana."
Na kudi ne wannan littafin kada ki karanta ba tare d
kin biya ni hakkina ba.
Ya gyad'a kansa tare da tashi zaune yana fitar da numfashi sama-sama ya jima a haka kafin ya tashi ya shiga bandaki na bi shi da kallo ina girgiza kaina ya fito d'aure da alwala ya hau dadduma.
Haka muka kwana ko hannuna bai ri'ke ba.
Da safe na gaishe ya amsa a dakile ya koma ya kwanta bacci ya yi sosai sai wajan sha biyu ya sakko kasa.
Lokacin na gama had'a kayan sanyawata dana ware domin aikawa da Fati na fito da akwatin kayan domin kiran Ayuba na same shi zaune shi kad'ai ya kunna tibi abinda ba dabi'arsa ba.
Ya dube ni muka kalli juna kafin ya ce." Wannan akwatin ta mecece Amina?"
Na ce." Ayuba zan aika gidan 'kanwata Fati."
Ya yi shiru bai ce komai ba yana kallona na ajiye akwatin na bud'e kofa na fita domin kiransa.
Sai da na shigo tukkuna ya biyo bayana na ce masa ya d'auki akwatin ya kai mata sannan na ya gaya mata zan kira ta a waya zuwa dare.
Bayan fitarsa na je na zauna kusa da ni bai kalle ni ba da romot a hannunsa yana duba tashar da zai k'alla.
Na matsa kusa da shi a hankali na ri'ke hannunsa ya dube ni babu yabo babu fallasa ya mayar da hankalinsa kan tibin.
Bakina nasa a kunnensa cikin k'aramin sauti na ce." Babyn love." Ya yi shiru bai ce komai ba.
Na zura yatsa a kunnansa ina fad'in.