Sashe 208
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mun jima muna magana akan yara tana labari yanzu Sultan na yarda ta d'auke shi yaran kuwa gabad'aya sun daina gudunta.
Cike da jin dad'in hakan na ce dama ai sakarci ne irin na yara cikin ko'karin nuna mata kuskuranta na baya na ce ai shi yaro baya son hantara da kyara duk inda ake dukansa ko aka nuna masa tsana zai guji wajen kuma kwakwalwarsa bata saurin mance abu.
To a daran ranar da za mu tafi sai ga wayar Idiris mijin Sahura muka gaisa da shi sosai ya fara gaya mini dalilin da ya sanya ya kira ni cewa Sahura ta tare a sabon gidanta kuma ya sanya kwa'do ya kulle tsohon wanda na mallaka mata ya yi-ya yi da ita ta bashi aron gidan ya sanya amaryarsa ta ce 'yan haya zata zuba.
Da farko ya kama hayar d'aki daya da rumfa mutum biyu ne a gidan da ya kama hayar to dakunan k'ananu ne gashi iyayen amaryatasa sun yi mata kayan d'aki a matse suke a gidan.
Shine yake neman alfarma a wajena na yi mata magana ta d'an ba shi aron gidan su zauna shi da amaryar tasa na d'an wani lokaci.
Na yi dariya sosai har sai da jikinsa ya yi sanyi ya dinga fad'in.'' Amina dariya ki ke yi mini tsakani da Allah daidai ne abinda Sahura ta yi mini ai mun zama daya ni da ita kuma ban auri yarinyar nan domin na wulakantata ba Allah Ya kaddara ne kawai."
Na ce." To Idiris gida dai na mallakawa Sahura shi tuntuni ka ga ba ni da hurumin da zan ce mata ga yadda za ta yi da shi tunda yanzu mallakinta ne ai daidai ne idan ta zuba 'yan haya ba wata matsala ba ce."
Ya furta." Ai na buk'aci cewar ta ba ni hayar gidan ta ce wai ita na waje za ta bawa domin tana zargi kada shekara ta zagayo na 'ki biyan ta wanda ni babu hakan a cikin raina wallahi zan biya ta kud'inta dalilin da ya sanya kenan na kira ki idan ba za ta sanya ni domin Allah ba to ki rarrasheta ta ba ni haya ta fad'i abinda ta yanke da shedu da komai a tsakani duk shekara na biya ta kud'inta.......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*140*
Na yi 'kokarin danne dariyar da yake ba ni na ce." Idiris a yanzu dai ba ni da wata hujja mai karfi da zan ce da Sahura ta baka gidanta ka sanya amaryarka a ciki.
Akwai gidajen haya da yawa a unguwanni mai zai hana ka sanya dillalai su cigita maka sai ka biya hankali kwance ka sanya matarka a ciki ina ganin kamar hakan zai fi kwanciyar hankali."
Ya yi d'an jim kafin ciki kame-kame ya fara cewa" To shikkenan zan sanya a nemo mini din amma tunda ita ta ce haya zata bayar da gidan mai zai hana ni ta ba ni akan dai ta bawa wani na waje kuma tsakanina da Sahura ai mun zama dayai shekaranmu kusan ashirin da aure yana da kyau a ce ta gane yadda take da matsayi a cikin raina.
Karin auran nan na gaya mata nufin Allah ne amma ta ki kwantar da hankali koyaushe idan na je gidanta da rigima muke rabuwa abubuwan nan da take yi mini bana jin dadi wallahi."
Na furta." Sai a hankali za ka ga komai ya wuce amma ni dai a shawarce kawai ka bar mata gidanta ka nemi wani."
Ya amsa da "To a sanyaye muka yi sallama na kashe wayata na ci dariya na koshi lallai Idiris ba shi da kunya wato shi gani yake yi abinda ya yi wa Sahura 'karamin abu ne da bai kamaci ace ta daga hankalinta ba ana sa tunanin kenan kuma yanzu Allah Ya dube ta ya kawo mata d'auki ya lallabo su ci tare har yana so su samu sakewa da walwala da matar da ya auro a kuma cikin gidanta.
Shi dai kawai ta bashi ya sanya matarsa a ciki amma babu maganar biyan kudin haya fad'e kawai yake yi mahaukaci ne shi ya d'auki kudi ya bata bayan yana ganin gidajen duka samunsu ta yi a sama ba kudinta ne ya saya mata ba.
Ni kaina ba ni goyon bayan hakan domin yadda yake munafikin nan ta sanya shi a gidan watarana sai dai mu ji labari ya sayar mussaman idan ya sake tara yara wahala ta sake yi masa yawa.
Kuma dole ta ha'kura ta kyaleshi dalilin yaran da suka ratsa a tsakaninsu .
Daga na yi juyi sai abin ya fado mini nasa dariya har sai da shigo gidan ya fahimci Ina dariya jefi jefi ya fara tambayata menene na bashi labari yadda muka yi da Idiris din.
Tsaki ya ja yana fad'in shima baya goyon bayan hakan tun daga farkon fara neman auran da rikicin da suka dinga yi ya gama fahimtar shine bashi da gaskiya kuma ai duk matar da za a yi wa kishi miji yakan ru'banya kulawa da ita domin dakushe mata damuwa da takaicin abokiyar zamar da za a kawo mata amma shi bai yi ko daya ba ya kuma nuna abinsa nasa ne shi kadai abinta kuma nasu ne gabad'aya mugunta ce tsantsa irin ta wasu mazan.
To alhamdulillahi cikin hukuncin Allah muka isa abuja muka samu gida da jama'ar dake cikinsa cikin farinciki da murnar dawowarmu tun daga kan Hauwa zuwa yaran da masu aiki kowa bakinsa har kunne .
Sosai na ga can ji mai kyau tsakaninta da su Taburni da akwai girmamawa da kuma mutunta juna.
Na ji dadin hakan na yi addu'a a cikin zuciyata Allah ya sanya hakan ya d'ore.
Kwana biyu ita take dawainiya dashi ya d'an sake da ita babu kallon kyama ballantana hantara kuma bai nemi da na zo na yi masa wani abin ba har sai da ta yi kwana biyunta tukkuna sannan na kar'bi hidimar tasa.
Ranar da muka cika sati daya da dawowa Sahura ta kira ni a waya muka gaisa jin muryarta a cunshe ya sanya ni saurin tambayarta nan take gaya mini Idiris ya sanya an 'balle k'wadon da ta kulle gidanta sun tare da matarsa a ciki itama d'aya daga cikin yaran shagona ne yake gaya mata shine take gaya mini zata d'auko masa 'yan hizba.'
K'warai na yi mamakin da jin haka wane irin karfin hali ne da Idiris ne shin ina kudin da ya samu to ai ba zai ce duka miliyan takwas din ce ta kare gabad'aya wajen neman auran matarsa ba.
Lallai bai so zaman lafiya ba domin duk da take matarsa tana da 'yancin da za ta nemi hakkinta wace irin gadara ce wannan da son rai."
Ta fashe da kuka tana fad'in." Amina wallahi saboda yara nake zaune da Idiris ba na so na kunyata Yallabai dan ganin irin tagomashin da ya yi mini amma wallahi na gaji da guma mini takaicin da yake yi hizba zan kai shi kwanaki fa haka ya kira baban yayanmu Alhaji Rufa'i yana gaya masa wai gaba nake yi dashi saboda ya k'ara aure na daina bashi hakkinsa na auratayya sannan ina fita ba tare da izininsa ba idan na yi abinci bana zuba masa idan ya zo gidan wallahi kuma sharri ya yi mini.
Abi
ci wataran ba shi yake yin cefane ba ni nake yin abina aiki kuma dole na fita tunda dama tuntuni shine yake ri'ke da ni da yara a gidan da bana fita aiki da ba mu kai labari ba.
Maganar kwanciyar aure kuwa tuntuni na ajiye a gefe bana kaunarsa wallahi shiyasa ko sha'awar ya zo kusa da ni bana yi."
Na ce." Lallai Idiris ashe bai d'auki shawarar da na bashi ba kenan.
Kwanaki fa ya kira ni yake gaya mini kin hana shi gida kin sa kwa'do kin rufe wai na yi miki magana ki bashi hayarsa domin kayan d'akin da aka yi wa amaryarsa suna da yawa can inda ya kama mata haya ya yi matsatsi ya ce ki yanke kudin da zai biya wai na zama sheda duk shekara zai dinga biyanki."
Ta ce." 'Karya yake yi wallahi ta 'karfi da ya ji yake so na bashi gidan akan ban bashi ba ya ce sai dai na ajiye aiki ni kuma na ki ajiyewa shine fa ya gaya yayanmu wai ina fita yawon ma'kota da zuwa kasuwa cefane bada yawunsa ba.
Sannan ya bi dare da rana ya buge kwadon da na sanya ya shiga gidan da matarsa suna zaune yau kwana hud'u kenan."
Dariya kamar cikina zai ciwo bakina ya mace na kasa ce mata komai saboda dariyar da nake yi ta hana ni maganar har sai da na ji maganarta a fusace tana auno mini zagi!
Na danne dariyar sosai ina fad'in." Sahura Idiris takadirin mutum ne wallahi malam bahaushe tsantsa to ki kai shi hizba ki kai wa Sahura an zama daya fa ba zan baki shawarar kai shi hukuma ba don Allah ki rabu dashi wallahi muddin yana zalintarki Allah zai saka miki."
Ta ja hanci tana fad'in." Sai fa hukuma ta shiga cikin lamarin nan Amina na rantse da Allah ba zan lamumci wannan rashin mutuncin ba."
Na ce." Idan kin kai shi hizba suka tura ku kotu ai kin ga duniya ta ji kuma akwai manema labarai ko babu komai mu kyale shi ya ci darajar su Yusra mana Sahura.
Kuma a jikina nake jin idan kin kai shi hukuma zai kara fusata ya ce dole ki ajiye aiki kin ga an biyu babu ko?"
Ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya irin ta b'akinciki da takaici can kuma na ji kittt ta kashe wayar na shiga duba wayata da mamakin abinda ta yi wato bata ji shawarar da na bata ba kenan.
To Allah Ya rufa asiri.
Wata uku a tsakanin dawowarmu daga Legos cikin da yake jikina ya d'an tasa zuwa yanzu wad'anda muke tare da su a cikin gidan sun fahimci ina d'auke da juna biyu tunda har ya huda zani ya yi kurcici wata biyar kenan ba wasu kwanaki.