← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 276

Sashe 81

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dukda hakan dai inna uwani ba ta ji dad'i ba ta so a ce mun zauna mun yi sati guda kamar yadda ta buk'ata.

Jin shawarar da suka yanke ya sanya na fara tunanin nemawa kaina mafita dole gobe ma mu shiga cikin mutane kuma ba zai yiwu na sake komawa da kayan jikina ba ba don komai ba sai don na siyawa kaina mutunci.

Na gayawa hajiya Saratu abinda yake da akwai da buk'atar son ta yi mini jagora mu fita a daran tunda da sauran lokaci dare bai yi ba.

Hajja ta kama fad'a sosai irin wanda bata taba yi mini ba gabad'aya taki kar'bar uzurina tana fad'in ai nasan ba yadda za a yi mu yi tafiya irin wannan mu je mu dawo a ranar na ce mata mantawa na yi sai da muka fito daga gidan tukkuna Allah ya tunasar da ni.

Ina jin inna Uwani da tunda muke maganar ba ta ce komai sai da ta ji hajjan tana yi mini fada tukkuna ta sanyo bakinta wai ko dai ba na son zuwa aka tursasani.

Takaici da b'acin rai bai barni na sake wata magana ba, na yi shiru kawai da bakina Ina mamakin yadda yanzu gabad'aya Hajja ta daina fahimtata ta kuma daina tausaya mini.

Haka dai muka fita ni da Hajiya Saratu ran mu duka a b'ace domin ita kad'ai ce ta dubi uzurina ta kuma fahimce ni ita Hauwa ma bata iya cewa komai ba har aka yi maganar aka gama kuma tana kwance a wajan amma uffan ba ta ce ba.

Direban da muka zo dashi ne ya fita da mu.

Garin ba bak'on Hajiya Saratu ba ne ta san wurare da yawa don haka ma ba mu yi nisa da hawa titi ba muka ci karo da wani shop a d'aya hannun na cewa magaji direba ya shiga damu ciki.

Dogwayen riguna na sayo mana ni da Yusura na had'o da hijabai biyu da takalmi flat ko rabin awa ba mu yi ba muka koma gidan Hajiya Saratu tana kara ta tausata don gaskiya yanayinta gabad'aya ya nuna takaicin abinda aka yi mini tana gaya mini ita kanta ta rasa abinda yake damun Hajja a tsukin nan don ta fahimci kamar tana shakkar Inna Uwani dalilin ma da ya sanya ta fara dora zarginta akanta
Na nuna mata babu komai kawai amma can kasan zuciyata abin yayi mini ciwo kawai da gaske, zan yi kokarin ganin na taushi zuciyata har mu tafi wani abu bai faru ta b'angarena ba.

Mussaman aka kunna genareto saboda mu.

Gidansu Hauwa sai na ce da kadan ya dara namu gidan kwaryar sama ce take dukan ta kasa.

Gidan kuma na had'aka ne mutum uku ne amma kowa da nasa bangaran wanda ya rasu ne kawai gidansa a waje.

Mahaifinsu ya rasu kuma shine babbansu sai dai gabad'ayansu 'yan boko ne babu wani dan kasuwa a ciki suna ci da biro da takarda rufin asiri na abinci ne kawai kuma a cikin sa'aninta dai Ina ganin ita kad'ai ce take auran mawadaci sauran duk sai a hankali suna kula da kansu ne dalilin aikin gwamnati da suke yi sai dai yadda na lura suna da hadin kai da k'aunar junansu ba kamar na mu gidan ba.

Wajan goma da rabi har mun kwanta ni da Hajiya Saratu da Yusura muna d'aki daya ita Hajja da 'yar uwarta suna tare Hauwa kuwa ba na ce ga inda take ba tunda ko lokacin da muka dawo ban ganta a falon ba.

Muna d'an ta'ba hira kad'an kad'an Hauwa ta shigo da wayarta a hannunta tana fad'in." Har kun kwanta ne?"
A tsanake na dubeta na ce." E wallahi."
Sai ta miko mini waya tana cewa." Maigidanki ne yake so ya yi magana."
Na yi sakare Ina kallonta yana so ya yi magana da ni bashi da lambata ne?" Abinda zuciyata take tambayata kenan.

Ta sake maimaita maganarta tana cewa'' Wata'kila ya kira layinki bata shiga ba kin san matsalar network, ni dai yanzu ya kira ni ya ce na hada shi dake."
Ban ce komai ba na amshi wayar sai ta juya ta fita ni da Hajiya Saratu muka bi ta da kallo.

Ita dai girgiza kanta ta yi a hankali ta koma ta kwanta ni kuwa na tashi zaune da wayar a hannuna ina tsammanin kiran nasa.

Minti biyar da fitarta ya kira.

Na daga a nutse na ji yana cewa." Kin kai mata wayar?"
"Eh ta kawo mini barka da dare?"
Na fad'a tare da ko'karin danne damuwata."
Ya d'an diririce ban san dalili ba can kuma na ji ya amsa yana cewa." Dazu na kira Hauwa a waya ta ce mini kun fita ke da Hajiya Saratu ina kuka je?"
Babu mamaki a tare da ni saboda nasan zai iya yin abinda yafi haka na furta." Ta yi mini rakiya ne na sayo abu a shop saboda ban yi guzurin kaya ba don ban yi zaton zamu kwana ba."
Ajiyar zuciyarsa na ji kafin ya ce." Kada ki kara shiga wani shago da zummar sayan kaya Amina hakan yana nufin abubuwa da yawa, kin san dai ba zai yiwu ace ku je bauchi ko dawo a ranar daya ba, me yasa ba ki bawa maganata muhimmanci ba a lokacin dana kira ki na gaya miki ki shirya ki bi su."
Na hasala da jin yadda yake ko'karin d'ora mini lefi shekkenan ni ba zan yi kuskure ba, kuma ai da ya gaya mini bai ce mini na hada kayana kwana za mu yi ba."
Na ce." Shine me? ai lefin ba na kowa ba ne naka ne ko ka gaya mini na hada kaya zamu kwana? da ka kira ni ka sanar da ni na bijire maka ne, na ce to shikkenan ban yi maka jayayya ba saboda kuskure karami sai kuma a gaza fahimtata."
"Ban kira ki don ki gaya mini magana ba Amina, na ce kada ki sake shiga shago ki ce za ki sayi abu ina da dalilina."
Shiru na yi ban ce masa komai ba sakamakon yadda na ga Hajiya Saratu ta tashi zaune tana kallona da yanayi na damuwa.

Sai kawai na datse kiran ban tsaya na saurari sauran maganarsa ba, wane irin dalili ne dashi wanda ya wuce na tozarci shikkenan don ina a matsayin na matarsa ba zan shiga shago na sayi abu ba ni din wacece.

Itama Hauwa ta so faruwar hakan hakan ne amma menene na gaya masa ga inda muka tafi bai kira ni a waya don ya nuna ya ji dadin karar da na yi musu ba ya kira ni yana tuhumata akan wane dalili.

Ban iya daure kukan da yake ta yun'kuro mini ba na fara share hawayen da yake gudana a kumatuna Yusura ta yi lamo akan katifa tana kallona kamar ta taya ni kuka.

Wannan littafin na kudi ne kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Hajiya Saratu ta dafa kafadata tana rarrashina a yanzu ita kadai ce take nuna damuwarta a kaina Hajja kam sai a hankali 'yar uwarta ta samu galaba akanta.

Hauwa ta shigo domin ta kar'bi wayarta ta same ni Ina kuka muna tattauna abinda yake faruwa da Hajiya Saratu sai ta yi kasa'ke tana kallonmu a lokacin Hajiya Saratu ta rufe ta da fad'a tana cewa." Ki ji tsoron Allah Hauwa yadda ki ke ko'karin gyara auranki to na hore ki ki gyara na 'yar uwarki wadda ki ka zo ki ka sameta da mijinta, bayan abinda ku ke yi na karkashin kasa har sai kin yi mata bita da kulli kin san fa duk abinda ya faru me zai sanya don ya kira ki a waya sai ki gaya masa shikkenan mutum baya kuskure..

Babu wata damuwa a tare da ita ta ce." Sai na yi karya kenan ko anti Saratu na ce masa gata nan a kusa da ni ko me?

Ya tambayeni ina take na ce masa kun fita tare zata sayo kaya ko ba haka na ji kuna maganar ba.

A lokacin da na yi masa karya ya ce na bashi ita kuma na yi yaya kenan, kuma na ji kina cewa muna yin abu ta k'arkashin kasa, ita din da kike shedarta kina da tabbacin ba ta yi ne? ai alhaki koikoyone wata'kila abinda ta yi ne ya waiwaiyo mata, ni wannan ai sai dai na kalleta kawai 'kiri-'kiri tana nuna mini 'kyama ta kuma fito da hassada da kishinta muraran a kaina ciki dai da izinin Allah sai na haifehe ko ana so ko ba a so gwara ma mutum ya ha'kura ya barwa Allah ikonsa
Maganganun Hauwa sun yi mini nuni da cewa tabbas ta ji ciwon abinda na yi wanda har hakan ya sanya suka hade mini kai ita da mijinta.

Amma kuma sun yi tsauri ga hajiya Saratu wata'kila ko ta manta da cewa ita din yayar mijinta ce fa ba kanwarsa ba, a tunanina ko kanwarsa girma da shekarunta bai kai ace ta tsaya a kanta da fitsara.

Ni idan ta yi mini kishiyarta ce ba abin damuwa ba ne tunda da kishi a tsakaninmu amma ni da ban had'a jini dasu ba ba zan ta'ba yi wa mai shekaru irin na Hajiya Saratu rashin kunya ba.

Abinda ya haddasa musu rikici kenan a tsakaninsu sai ya zamana ni na shiga tsakiya kuma a ta dalilina komai ya faru Hajiya Saratu fadi take yi "Ba za ta je ta zauna miki ba din, ko ita ce ta yi miki cikin, ai ni Amina ta yi mini daidai duk abinda za ku ce akanta kun dade baku fad'a shegiya mara kunya ki dubi tsabar idona ki dinga nema ki zage ni saboda kin samu kanki ko, idan kin manta bari na tuna miki ni Yaya nake ga Tajo ba k'anwa ba balle ki ce za ki gaya mini magana son ranki Ubanki zan ci domin ba na ciki da iskancinki shashasha mara wayo kawai, ai iliminki bai amfana miki komai ba sai rashin dubara......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.
Chapter 81 · 0% Book details