← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 276

Sashe 35

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne.

To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji.

Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba.

Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu.

In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi.

Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama.

Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.

Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki.

Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki.

Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu.

Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay
*20*
Mutuwar sai ta zama kamar ta wani babban mutum domin kuwa abokanansa da tun daga haihuwar ya sanar musu sune suka dinga turereniyar zuwar masa gaisuwa da jajantawa cikinsu kuwa harda manyan mutanan da sukayi masa angonci ranar d'aurin auranmu a saudiya.

Ni da Hajja gayyar da muka yi sai ta zama ta zaman makoki don gidan cika ya yi da jama'a na kusa dana nesa.

Dangin Mamanmu zugarsu guda daga maiduguri suka zo bisa jagorancin Anti Yagana washe garin ranar da suka tafi 'yan gidanmu suka zo kaf dinsu har da Babanmu da Baba Sule da wasu daga cikin yaransa.

Da yake akwai sassa daban daban a gidan a can mazan suka taru, matan kuma muna tare tunda akwai d'akuna kusan shida a falon...

Maigidan ya bada kwangilar yi musu abinci mai kyau daga restaurant.

Domin ba mu da mai aiki mace dama falalu ne yake yi mana a wasu lukutan kuma ni ma na kan dan shiga kicin sai da cikina ya tsufa tukkuna na tafi hutu.

Amma dai har yanzun Falalun shine yake yi ma harda Hajja.

Inna Uwani ba ta zo ba amma ta kira suka kan hanya ta d'an yi jiyya ne amma ta warware a yadda take gayawa 'yar uwatata.

Satinsu daya suka shirya tafiya duk yawansu maigidan ya sanya direba yin jigalarsu a irin manyan bos din da yake da yake ajiye dasu saboda faruwar irin haka.

To gaskiya 'yan uwa sun nuna mini kara da alhini dangane da abinda ya sameni.

Kowa da irin nasihar da yake yi da kawo mini misalai kan cewa duk wanda ya yi rashin dansa yana karamin yaro ana sa ran zai samu cetonsa a ranar alkiyama, Kuma na godewa Allah tunda ina da wasu ba ita kadai ba ce.

Koda anti Yagana da Falmata suke yi mini wannan tsokacin a lokacin kasa tsayar da hawaye na yi domin ba kaina nake tausayawa ba maigidan ne abin tausayi domin daga randa akayi mutuwar zuwa yau ya kasa nutsuwa yakan 'boye kansa ya yi kuka abin ya yi ta ba ni mamaki, sai nake ganin a matsayin shekarunsa ya ci a ce ya ha'kura ya barwa Allah domin ita mutuwa rigar kowace, shi mai yi wa wani fad'ane amma shi yake yi, ya dora hotonta a fuskar wayarsa, na ce masa ya cire ya'ki cire hakan kuma da ya yi ba shi zai kawo masa nutsuwa da kwanciyar hankali ba.

Ni kam duk da abin yana sasakata hakan nan na barwa Allah na yi ciwon nono kamar me ya gaji da tsiyaya da kumburinsa ya sace.

Daga zarar ta fado mini zan ta nanata Innalillahi wa'ina ilaihi! har na samu rangwami.

Sai ya zamana shi da Yusi ne suke neman daga mana hankali a gidan.

Shi ma Yusi ha'kuri kullum cikin zancenta da yake akwai sauran hankali har tambayar Hajja yake yi a can lahira wacece zata zama mamanta.

Hajja ta bashi amsa da cewa." Uwar muminai itace Maman duk wani jinjiri mace ko namiji da ya mutu Nana Aisha matar manzon Allah RT.

Duk wannan misalin da take kawo masa hakan bai sanya ya barwa Allah ba.

Kamar yadda Baban nasa yake k'unshe kansa ya yi kuka Shima haka yake b'uya a koridon gidan ko cikin d'aki ya yi ta kuka.

Na same shi watarana yana yi na dinga yi masa fad'a domin hankalina tashi yake yi nima, ni na haifi abata amma na danne na ha'kura na barwa Allah ikonsa a ganina kowama sai ya ha'kura.

Fad'an da nake yi masa ya janyo hankalin Hajja da Hadiza da suke falo.

Yaron ya fita ya barni ni kad'an a d'akin yana kuka.

Na bishi falon ina cigaba da nuna masa illar hakan.

Yau kusan sati uku ya ci ace a ha'kura hakan.

Hajjan ta ce." To sai a hankali ai Amina kowa zai manta kuma kin san zuciya kowa da irin tasa, Wani yana dauriya da juriya, wani kuma bashi da ita, bayan haka ma yarinyar dai ta shiga zukatan kowa kafin a manta sai an yara."
Na ce." Hakane Hajja amma ni idan naga suna haka sake dawo mini da lamarin baya suke yi.

Shima fa Baba da yake wasu lukutan da haka nake kiransa na sha kama shi a dakinsa yana kuka kamar karamin yaro na yi masa magana ya'ki ya daina.

Ta yi murmushi tana cewa." Rabu da wannan Amina Inaga sai an had'a masa da rubutu, domin ni ma sai dare ya tsala ina bacci sai shigo mini idan na tambayeshi sai ya ce wai ya kasa bacci da ya rufe ido zai ga Nana ko da Samira ta rasu haka ya dinga yi mini wallahi sai a hankali kuma ya manta.

Shiru na yi ban ce komai ba na zauna saman kujera wanda ya yi daidai da lokacin da ya sauko daga samansa hannunsa ri'ke da manyan hotona irin na bango uku.

Na yi mamaki sosai tunda a dan zaman da na yi dashi na fahimci bai fiye son bidia ba, domin kuwa yan alhalussuna basu yarda da kafe hoto a d'aki ba.

Na farko ya ajiye frem din da yake d'auke da hoton tsohuwar matarsa Samira sai kuma ga hotonan baby Nana ya sanya a buda masa su lallai koda yana da wannan akidar ba ta yi tsanani ba tukkuna
Na bishi da kallo a lokacin da yake ko'karin isowa wajan da muke rungume da allon hoton nan dana tabbatar da cewa na Baby Nana ne, domin kuwa da kunnena na ji lokacin da yake waya yana bada umarnin yadda za a yi masa bayan ya turawa mai aikin hoton nata wanda ya d'auketa tun tana raye a wayarsa.

Kusurwa uku duk ya bi ya sa'kale allon hoton yarinyar ta fito sosai kuma ta yi kyau.

Na tsirawa fuskarta ido Ina sake tabbatar da kamaninta da ubanta wanda a lokacin da take raye ban ga hakan ba duk kuwa da fadar da jama'a suke yi ban tabbatar ba sai yanzu da bata raye a duniyar.

Hajja ta dube shi tana fad'in." An ya Tajo ka so ka zauna lafiya kuwa, ka dubeka duk ka zabge lokaci guda, idan irin haka ta faru ha'kuri akeyi a barwa Allah ikonsa cikin kudirarsa sai kaga wata shekarar an samu madadi.

Wannan yarinyar Allah Ya rubuta ba mai nisan kwana ba ce."
A ajiyar zuciya ya dan sauke a hankali ya furta." Hajja na yi hakuri tuntuni ai na barwa Allah wataran muma duk na hakane, amma har yanzu ina jin wani yanayi a tare da ni wallahi tunda aka haifi yarinyar nan Ubangiji Allah Ya dora mini tsananin sonta shiyasa nake jin rashinta kamar na babban mutum."
"To ai dama hakane duk dan da ba zai yi nisan kwana ba sai Allah Ya jarrabi iyaye da tsananin sonsa.

Ka godewa Allah bisa ni'imomin da ya yi maka sai kaga ya sake yi maka wani tagomashin domin shi Ubangiji yakan jarrabi bawansa da abubuwa da yawa idan ya ga ya yi hakuri sai ya kawo masa d'auki."
Ya girgiza kansa a nutse ya furta." Allah Ya ba mu dangana.

Ya dubi inda nake zaune a hankali ya ce." Zan koma sama ki biyo ni da abinci."
A hankali na ce." To me zaka ci sai na shiga kicin na yi maka da kaina yanzu."
Ya juyo yana kallona kafin ya furta." Falalu bai yi ba ne."
''Ya yi."
Na fad'a ina dubansa sai ya ce." To ki kawo mini kawai ke ki huta."
Haka yake tun dama can bashi da matsawa akan lallai sai na yi masa abinci.

Idan na yi masa zai ci da godiya da yabawa idan ma ban yi masa ba zai ce don me ba, zai ci na wanda ya saba wato Falalu.

Wad'annan halayensa na saukakawa suna taka muhimmiyar rawa wurin ganin na bi shi ko da kuwa ya 'bata mini rai a wasu lukutan.

Na sameshi zaune saman sofa da laptop a gabansa amma hankalinsa baya kanta Yana duba wayarsa ne.

Na ajiye kayan abincin saman daddumar da yake zama idan zai ci abinci.

Ya kalleni yana fad'in." Zo ina so na yi magana dake."
Gabana ya dan buga kad'an saboda ina jin tsoron kada ya ce zai kwanta da ni jikina da d'aita ban dawo daidai ba, duk da jinin ya d'auke amma har yanzu ban ji ni yadda nake ada ba, kuma ban yi wani gyara ba, ba ni da nutsuwar yin hakan saboda rashin nutsuwa da rashin sukuni dake tartare da ni da mutanan gidan.
Chapter 35 · 0% Book details