← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 276

Sashe 141

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni marainiya yarana ma marayu Baba Tabawa ga damuwa iri daban-daban wanda nake tare da shi shine mussababbi Baba Tabawa mutumin nan ya tsane ni, wallahi ya hana zuciyata ta huta, bala'in yau daban dana gobe, na gaji! na gaji da auransa ya zame mini karfen kafa a rayuwata."
Ta dinga girgiza kanta tana jimantawa kafin na ji saukar hannunta a kumatuna tana share mini hawaye take ce wa." Ki daina ce wa kin ga ji da ibadar Allah Amina, ba ki sani ba ko wannan itace hanyar shiga aljannarki.

Ni kam sai nake ganin kamar kukan dad'i kuke yi, domin kuwa a kaso dari Ubangiji ya yi ba ku kashi tamanin, idan har an samu wani tasgaro da kalubale a cikin kashi darin nan a shawarce godiyar Allah ce za ta biyo baya.

Kuna rayuwa ne anan a lullube amma Amina duniyar nan a rikice take wallahi talauci da k'akanakayi ya yi wa al'umma yawa.

Matan aure zina zawarawa zina 'yan mata k'ananun yaranmu zina duk domin su ci abinci.

A yanzu duk wata mata da Allah ya rufa mata asiri ta samu miji mai kula da iyali da d'aukar nauyin ci da sha da kula da lafiya, to wallahi tallahi ta yi hakuri ta zauna domin idan ta fito rayuwar da za ta fuskanta bayan auran gagarima ce.

Amina mace yanzu ko tana da kudi tana kasuwanci muddin ba ta da miji abin zargi ce a wurin mutane koda kuwa tsarkakkiya ce, yanzu nan za ki ji wasu daga cikin marasa fahimta marasa hankali suna kiranta da sunan karuwa.

Wannan rayuwar kin yi ta a baya Amina a lokacin duniya ta dan kwance gari bai lalace irin haka ba.

Ki yi hakuri ki jure kalubalen gidan auranki in sha Allahu watarana sai labari......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan.

Normal What'sapp group kuma #700 telegram hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*TALLAH!*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl
Momyn Hajara GHT supplements
Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan kowacce irin matsala in sha Allah
Hadin Amare
Hadin Ango
Hadin jego
Hadin uwar gida
Hadin babbar mace
Hadin maida tsohuwa yarinya
Muna da Maganin sanyi kowanne iri
Muna da maganin ulcer
Muna da maganin Asthma
Muna da maganin ciwon zuciya
Muna da maganin ciwon Hanta
Muna da Maganin hawan jini
Muna da Maganin ciwon Ido
Muna da Maganin rashin haihuwa
Muna da Maganin skeler
Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah
Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki
Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya
07012621175
Register 8000 ne kachal
*97*
Sosai maganganun Baba Tabawa suka sanyayyar mini da jiki.

Duk abinda ta fad'a babu k'arya.

Tabbas na yi gwagwarmayar rayuwa na san komai.

Amma ni a irin fargabar da nake ci a yanzu sai nake ganin gwara mini zaman babu laluran miji hankalina zai fi kwanciya shin mai ake nema a cikin aure ne haihuwa to na samu.

Ina da dukiyar da zan iya ri'ke kaina da yarana marayu.

Allah da kansa ya ce a rabu idan abin ya ci tura, ai gabad'aya lamarin aure da maslaha ya zo domin kuwa abu ne na mutum biyu tare da yarjejeniya kafin tabbatuwarsa.

Fuskata na goge a lokacin na ji idanuwana sun tasa sosai, ba komai ne dalili ba sai irin kukan da na yi wanda na shafe tsayin shekaru rabona da yin irinsa.

Wayata dake saman madubi ta fara kara alamun shigowar kira.

Da kanta da sauri ta tafi ta je ta d'auko mini ta ba ni na kar'ba ina dubawa A kunnena kawai na sa wayar kafin na bud'e baki da kyar cikin alamun cushewar murya da dashewa na ce." Na'am.''
Muryarsa babu amo ya furta." Baban Saude ya sauka tun d'azu yanzu haka muna tare da shi sashena da nake saukar ba ki."
Shiru na yi ban ce masa komai ba.

Na ji yana fad'in." Ko ba kya ji ne?"
A takaice na ce." Ina ji ya za a yi yanzu to?"
"Ke muke jira?"
Ban bashi amsa ba na kashe wayata jin yadda zuciyata take wani irin harbawa, ina ganin sai mutumin nan ya kaini kasa tukkuna hankalinsa zai kwanta.

Baba Tabawa ta kwashe kayan karin kummalon tana fad'in." Sai dai a had'o miki wani don wannan ya yi sanyi.

Cike da sarkewar murya da numfashi na ce." Ki bari na dawo tukkuna na yi ba'ko daga Maiduguri d'an uwan Mamana ne ya zo."
A sanyaye ta furta." Amma lafiya dai ko?"
Ne ce." Baba Tabawa akan maganar 'barin cikin da na yi ne, shine ya kira shi ya gaya masa don yana zargin zubarwa na yi da gangan.

Sai ta shiga girgiza kanta gabad'aya yanayinta ya nuna alamun damuwa da fargaba ta ce." Haka kawai kuma sai ki zubar da ciki Amina, ai kuna da ilimin addini daidai gwargwado wad'anda ma suke yin sakarcinsu a waje su samu ciki ba su zubar ba sai na sunnah, amma ban ji dadin wannan zargin ba.

Ban ce mata komai ba domin duk bayanin da zan yi mata akan mutumin nan ba zata gane ba.

Idan na ce mata shekarun baya na ta'ba yun'kurin zubarwa za ta fara wasu tunanuka marasa kyau akaina kuma bai zama lallai ta fahimci nufina ba tunda ita ai mutuniyar da ce.

Akwai tauhidi tare da k'adaita Allah.

Shi kam ai ko zan kwana ina rantsuwa ce wa zubewa ya yi babu wata hujja da rantsuwar da zan yi masa ya yarda kan cewa ba hada ba ki muka yi da Hauwa ba.

Hijab na zura a jikina mai fuska har kasa muka fito tare da ita tana ta jadadda maganar har zuwa lokacin Hauwa ba ta fito ba..

Kai tsaye hanyar fita na nufa ita kuma ta nufi kicin babu karsashi da kuzari a tare da ita.

Wuri ne k'ebantace ya ware a gidan domin ganawa da manyan bakinsa na mussaman.

Gabad'aya wajen ya fi ko'ina kyau da tsaruwa a gidan.

Masu hidima da aikin wajan su kansu na daban ne.

Yadda ya sau'ki Baban Saude a sashen ya tabbatar mini da ce wa bai ajiye shi a nesa ba, suna tare domin tun bayan sulhunmu na farko na fara fahimtar abota mai karfi ta shiga tsakaninsu.

Ina dosa kofar da zan shiga falon escort dinshi Sukajiru da Emanuel 'Dahuru sune dai amintattun nasa da basa rabo dashi mussaman ma Sukairaju da duk inda zai tafi tare suke tafiya, bayan wasu jami'ai guda uku da naga ba sa rabo da shi.
ina isa suka fara gaisheni na amsa sama-sama kafin da sauri Sukairaju ya bud'e mini k'ofar na shiga a nutse.

Suna zaune a kujera d'aya hira suke yi cikin faraa da barkwanci tsakiyarsu Loptop ce ta maigidan da alama akwai abinda yake nuna masa a ciki.

Center tablet din da yake tsakiyarsu kuwa sha'ke yake da manyan kuloli akwai tazara sosai tsakanina da inda suke tunda girman falon ya shahara sosai.

Kafin na k
rasa gabad'aya gwiwata ta sage saboda ban san irin tozarcin da Baban Saude zai yi mini a gaban mutumin nan ba
Cikin nutsuwa na isa wajan da suke zaune na d'an rangwafa kusa dashi kafin na bude baki a nutse na ce." Baban Saude sannu da hanya, fatan duk mutan gidan suna nan lafiya ya su Dada da sauran 'yan uwa."
Ya fuskanceni sosai yana dubana da wani irin yanayin da na kasa tantance shi.

Ya ce." Kowa lafiya lau Amina, Dada tana gaisheki ai dana gaya mata cewa zan zo nan wurinki har ta sanya mini rigima wai sai ta biyo ni da k'yar na zame na gudo ba ta sani ba.

Murmushi na yi wanda babu nisha'di ko na miskala zarratin cikin dusheshiyar muryarta da ta ga ji da kuka na ce." Dada kenan ai ba ta ta'ba zuwa ta ga inda nake zaune ba."
Ya sake fuskantata sosai yana fad'in." Tabbas hakane amma ai tana samun labarai a kanki masu dad'i da akasin haka."
Shiru na yi tare da yin kasa da kaina gefe guda Ina ta nazarin manyan mazuban abinci masu daukawar hankali dake jere a saman center tablet din da yake daf da su.

Cikin zuciya na dinga tunanin akan haka.

Akwai masu yi masa hidima nau'i daban-daban domin sai na ce duk tsayin zama da shi wasu daga cikin yaransa ma ban san su sosai ba.

Amma dai zuciyata ta fi aminta da cewa wannan aikin ba na kowa ba ne face na matarsa da ya rataya fulawar so da k'auna irin ta indiyawa.

Momi ce ta yi masa wannan hidimar domin fitar da shi kunya.

Ko kad'an hakan bai burge ni ba duk da cewa ta yi ne bisa bin umarinsa amma sai nake zargin babu abinda bai gaya mata ba na abinda ya shafi tsakaninmu da shi.

Na sake jin wani irin nauyi da kunci a cikin raina, gabad'aya sabgar mutumin nan ta fice mini daga rai domin kuwa kansa kadai ya sani bai da adalci ko kad'an.

"Ina ita abokiyar zaman naki ai tare nake so na zauna da ku domin tattauna masla'ar da ta kawo gidanki Amina."
Wannan maganar ita ta datse tunanin da na lula na daga kaina cikin kasala da zullumi amma abin da ya ba ni mamaki bai wuce ganin idanuwan maigidan a kaina ba gabad'aya ma hankalinshi na kan 'kafafuna.

Har cikin raina kallon ya ta'ba ni domin irin na mutukar 'kurrula ne, nan da nan na fahimci abinda ya assasa hakan bai wuce lallen da ya fito ya zanu radau a kafafuna ba.
Chapter 141 · 0% Book details