← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 187 OF 276

Sashe 187

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu.

Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
*Gudun aure paid book complete 2k akan telegram.

Wshap Gruop 1k via 0542382124....Binta Umar gtbank.*
*07084653262*
*126*
Kwanciya muka yi a tare a gadon ya d'auki kaina ya d'ora saman kirjinsa sannan ya d'ora hannunsa a jikina a hankali ya ja bargo ya rufe mu gabad'aya.

Rufe idona kawai na yi ba da niyyar bacci ba domin kuwa babu shi a idona wanda nake da tabbacin shi din bai sake komawa ba har aka kira sallah.

A tunaninsa bacci nake yi ina ji ya sauke kaina a hankali ya mike ya nufi toilet na tashi zaune ina kallonsa har ya gama abinda yake yi ya fito.

Ya d'an tsaya yana kallona na d'an wani lokaci sai kuma ya girgiza kansa kafin ya kama hanyar fita ba tare da ya yi magana.

Sauka k'asa na yi a d'akina na yi wanka na yi sallah a gurguje na kimtsa jikina don babu yadda za a yi ayi wannan tafiyar babu ni.

Na sake komawa saman na shi sai na same shi har ya yi wanka ya shirya yana zaune gefan gado cikin kaftani gilas da hularsa a gefe yana waya dai da Rabi'un da suka yi magana jiya yana sanar da shi gasu nan zuwa.

Sai da ya gama tukkuna ya dube ni na zauna gefansa tare da gaishe ya amsa cikin kulawa ya dago fuskata muka kurawa juna ido.

Kallon da yake yi mini ya kara karya mini zuciya hawaye suka zubo.

Ya fara fadin." Kash! menene haka kuma? ki dubi idanunki sun kumbura Amina ni kam na tsanani wannan kukan wallahi." Ya fad'a cike da yanayi na damuwa da tashin hankali."
Sosai na fashe da kukan da karfin gaske ina fad'in." Ni fa wallahi tare za mu tafi."
Ya ce." Akan wane dalili, ai nima ba kwana zan yi ba kuma in sha Allahu da k'afafuna zan dawo gidana, kada ki yarda da abinda zuciyarki take raya miki Amina tunda har na riga na tsallake na baya to wannan ma zan tsallake in sha Allahu."
Na girgiza kaina ina fad'in." Ban yarda ba kawai dai mu je tare na raka ka hankalina zai fi kwanciya."
Ya ce." To yaran fa?''
Ya fad'a yana goge mini kumatu.

Na ce." Su zauna wurin su Mairo ai da mutane a gidan ba za su ci karo da wata matsala ba in sha Allahu tunda dama babu wani sabo mai yawa a tsakaninmu."
Ya girgiza kansa yana cewa." To ai so nake ku saba yanzu ki zauna cikinsu sosai ki kula mini da su hankalina zai fi kwanciya ki zauna a gida na je na dawo Amina irin wannan rigimar taki ce fa ta sanya ban sanar dake na farko ba."
Na ce." Sai ka jefa zuciyata cikin damuwa ba, menene abin boyewa."
"To in banda abinki ai abin alheri shi ake shela, sharri kuwa ba abin fad'i ba ne."
Ya ri'ke hannuna yana duba zoben azurfan da ya sanya mini a yatsana."
A d'an sanyaye ya ce." Kin amince na je na dawo ko matata?"
Girgiza kaina na yi tare da fad'in." Wallahi ban amince ba tare za mu je gashi ma na shirya."
Ya yi jim na dan wani lokaci kafin ya furta." Tunda dai har kin rantse ba zan karya miki ita ba."
Na sauke ajiyar zuciya Ina fad'in." Na kawo maka abinda za ka ci ko?"
Ya ce." Ke 'din kin ci?"
girgiza kaina na yi.

Ya furta." To je ki kawo sai mu yi breakfast din tare."
Na tashi da azama na sauka k'asa ina jin dad'in yadda ya amince tafiyar da ni.

To ba mu isa 'kauyen Bunkure ba sai gefin la'asar tafiyar mota ce K
kuma ta samu k'wararran direba Ade wannan karon tare aka tafi da shi su uku da Amintattun yaransa Sukairaju da D'ahuru.

Ko da nake cikin a garin kano kafata bata ta'ba taka garin ba sai a wannan karon.

Yadda dama muka shirya shine idan har abin ya zo da sauki mun kammala abinda ya kawo mu gidan malamin sai mu wuce can gidana na sharad'a mu kwana idan ya so idan mun gaisa da Hajja zuwa jibi sai mu tafi.

Mun samu tar'ba ta mussaman a gidan Malam D'aha.

Na ga kara da karamaci irin na mutanan kauye domin kuwa ina idan da sallar magriba aka cika gabana da kwanukan abinci har daga ma'kota.

Mafiakasari towo ne na masara dana dawa sai wata langa da aka kawo mini ita daga baya cike da dambu na tsaki wanda ya ji zogale da gyad'a yana ta k'amshin mangyad'a zuryan da yajin barkono a gefe.

Ya ba ni sha'awa sosai na kuma yi masa cin yaushe gamo na toshe cikina da shi duk tarin yunwar dana nad'a a tsukin nan sai da na rasa yadda zan yi da cikina.

A daddafe na yi sallar Isha'i.

Ina idarwa wata matashiyar budurwa ta shigo doguwa mai duhun fara ba ta da jiki sosai akwai yarinta a tare da ita ta sake gaishe ni na amsa ina fad'in ta kwashe kwanukan abincin da ta dinga kawo mini gasu nan shida a jere.

Ta tsuguna tana bubbud'awa ta dube ni tana fad'in." Ai d'aya kawai ki ka ci Hajiya."
Na ce.'' Ina zan kai wannan abincin yar uwa wannan ma na gode sosai kuma wallahi ya yi mini dadi 'kwarai da gaske."
Ta yi murmushi ba tace komai ba ta fara had'a kan kwanukan tana fita da su.

Na d'auki wayata dake gefena na duba na ga network dina ya d'auke gabad'aya wata'kila yana da ala'ka da yanayin d'akin da nake ciki tunda na 'kasa ne kuma a k'asa yake sosai.

Gabad'aya hankalina yana can b'angaran malamin tun zuwanmu da muka shiga tare na gaishe shi na fito ban sake jin wani motsi ba sai ta hayaniyar iyalin gidan da shige da fice da ake ta yi na d'aukar abinci daga almajiran malamin.

Gajiya na yi da zaman d'akin na fito tsakar gidan na samu jama'a a cike da yake mai yalwa ne kwarai matan gidan su hud'u suna can daga gefe suna cin abinci a tare wasu daga cikin yaran kuma sun ci sun gama wasu na cin na su.

Kwanuka gasunan birjik a bakin manyan tukwanansu.

'Yar budurwar nan da har yanzu ban san sunanta ba na ji tana fad'in." Bandaki za ki shiga.''
Kafin na ce komai daya daga cikin matan gidan ta ce." Hajara zuba mata ruwa maza a buta Hajiya alwala za ki yi ne?"
Na ce." A ai na yi sallah na fito na sha iska ne." Yarinyar da aka kira sunanta da Hajara ta d'auko tabarma da sauri ta shimfida mini can gefe na je na zauna ina yi mata godiya cikin ikon Allah zamana ke da wuya network din duka layukana ya dawo.

Na fara neman number Sahura muka gaisa sosai ta sake yi mini gaisuwa nan nake sanar da ita cewar na shigo garin zan kira ta zo gida ta same ni zuwa gobe.

Muna sallama na nemi number Hajja da ta shiga sai ta katse na kira ya kai sau biyar nan na gane network din yake hawa da sauka wai ina so na gaya mata cewar za mu shigo gobe.

Na dauki kimanin minti talatin da zama a tsakargidan wanda ya yi daidai da lokacin tara na dare da minti biyar.

Daga can b'angaran malamin na ji maganarsa alamun zai fito na sauke ajiyar zuciya a hankali idona a kan hanyar suka fito tare da wannan Rabi'u da yake yawan kiransa a waya wanda shine ya kan gaba wurin tararmu lokacin da muka sauka a garin.
littafin gudun aure na kudi kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Suka fito tare da kuzarinsa ya tsaya cikin kulawa yana yi wa matan gidan sallama na tashi ina gyara mayafina na d'auki jakata can inda suke zaune na nufa ina fad'in." Za mu tafi, na gode sosai da karamaci Allah Ya saka da alheri, na dubi Hajara dake zaune cikin 'yan uwanta na ce." 'Yar uwa sai Wani lokacin ko na gode da kulawa."
Ta washe bakinta tana fad'in." Ku gaida gida Allah Ya tsare hanya."
Na ce." Amin Ya Allah tare da yin gaba ganin ya riga ni fita ina jin matan da yaransu suna ta yi mini fatan alheri.

Ina fita daga can wajen motar da mu ka zo Sukairaju nake hange da D'ahuru sai Rabi'un suna taga-taga kafin na hangi Baban ya yi wata irin fad'uwa irin ta ruf da ciki da kirji.

Ade ya fito daga mota a ki'dime! yayin da gabad'aya suka rufu a kansa duk da yake dare ne amma ai irin na karkara ne da suke da wadatar kwanciyar hankali ba irin cikin gari ba hakan ya sanya mutane fara tsayuwa a wajen.

Ban san inda nake jefa k'afafuna ba kawai dai na tsinci kaina a tsakiyarsu lokacin da suke ko'karin ciccib'arsa.

Rabi'u yana fad'in da k'afafunsa ya fito kuna dai kallo magana ma muke yi da shi ya yanke jiki ya fadi."
Jikina ya dinga kyarma na tsuguna ina d'ago kansa yana karyewa ganin haka ya sanya ni ihu! ina Kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!

Baba Baba, na dubi Sukairaju a gigice ina fad'in." Ku d'auke shi mu tafi asibiti."
Rabi'u ya ce." Cikin gidan za mu mayar da shi Hajiya ."
Daga haka suka fara kici-kicin ciccib'arsa Sukairaju ya cire gilashin idonsa da wayoyinsa tare da wallet dinsa ya sanya cikin aljihunsa su biyu shi da D'ahuru suka kama saman shi ta wajen kansa.

Rabi'u da Ade suka rirrike k'afafunsa a haka ina kallo suka taitayeshi suka koma dashi cikin gidan suna ta Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un.

Na bi bayansu k'afata na karkarwa shikkenan kuma tunda har kansa ya karye ya mutu.
Chapter 187 · 0% Book details