Sashe 238
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Ko ka zama kurma ne Allah Ya ja zamaninka my heart."
Ya dube ni yana lumshe idonsa a kasalance ya ce." Menene?"
Na ce." Kai ne my love dina"
"Humm!" kawai ya iya cewa kafin ya janye idonsa daga kaina ya cigaba da daddana romot.
Nasa hannuna a cikinsa ina fad'in." Yunwa kake ji fa, tun jiya baka ci komai ba ina sane gaskiya rayuwata tana cikin had'ari."
Ya dai yi shiru bai tanka mini ba, sai ma ya fara muzurai yana d'an 'bata fuska.
Na dake sosai ina fad'in." Bari na yi maka abinci ko, wane iri ka ke so na yi maka? umm ka fad'i kalar da kake so zan shirya maka yanzu."
Ya yi gyaran murya bai kalle ni ba ya ce." Tafiya zan yi gobe idan Allah Ya kaimu."
Na ce." Na shirya kenan mu tafi tare ko?"
Ya kalle ni da sauri fuskarsa ta d'an sassauta.
Sai kuma ya d'auke kansa yana cewa." Duk yadda ki ka gani Amina?"
Na ce." Farincinka shine nawa Habibi za mu tafi tare in sha Allahu."
Ya gyada kansa amma bai ce komai ba.
Na ce." Me zan yi maka fannin abinci."
Ya ce." Ki yi duk abinda ranki yake so zan ci."
Na sauke ajiyar zuciya a hankali na ce." To shikkenan in sha Allahu."
Kicin din na tashi na nufa na fara aikin cikin nutsuwa mintinta ashirin a tsakani ya biyo ni lokacin ina yanka albasa ya furta.
"Kawo na taya ki ko."
Kai na girgiza tare da cewa." Ka huta kawai ba ni so ka yanke hannunka ni zan yi komai na samu lada."
Ya tsaya daf da ni a hankali na ji yana cewa." Wane suna ne na ji kin kira ni dashi da zu." Yafad'a yayin da ya d'ora hannunsa saman kirjina.
Na d'an janye kad'an kafin na ce." Suna wane iri Allah Ya taimaki rayuwarka."
Ya girgiza kansa yana cewa." Babyn love da dad'i sunan.
Me yasa tuntuni ba ki kira na da shi."
Na ce." Ka manta dai Ina kiran ka dashi mana a wani yanayi."
Ya yi shiru yana kallona har ina jin saukar ajiyar zuciyarsa.
Ya ce." Na tuna a yanayin nan da ni dake muke ganin tamkar mu kadai Allah ya hallita a duniya ko."
Na gyad'a kaina ina murmushi na ce." E, amma idan kana so a cigaba da kiran ka da sunan sai a cigaba."
Ya ce." A a ki cigaba da kira na dashi a yanayin nan na mussaman ni tsoho ne idan yarana suka ji ana ce mini baby dariya za su yi."
Murmushi na yi ina fad'in." To haka za a yi kuwa."
A haka na gama shirya abincin muna hira da kalaman soyayya.
A daran Usaini ya zo ya kar'bi sa'kon matarsa na wurin Hajja.
Sannan na ce masa zan je gidan Gwaggo ya ce na shirya mu je tare shima zai gaisheta.
Allah sarki Gwaggo ta ji dadin ganinmu bakinta kamar gonar audiga ta samu alheri na kudi a wajensa tana ta yi masa godiya har sai da ya gaji ya hana ta ya ce don Allah ta daina yi masa godiya akan yana rik'on yaran da addini ya bashi damar zame musu uba.
Koyaushe idan magana ta tashi zai ce haifarsu ne kawai bai yi ba amma tunda yana aurena ubansu ne kuma addini ya mallaka masa.
Yadda na samu Sultan cikin walwala da wani irin kuzari da lafiya ya tabbatar da mini da cewa hasashena akan Hauwa gaskiya ne.
Shi kansa uban dana d'auki yaron mussaman na kai masa shi d'akinsa ya d'aga shi sosai yana duba shi fadi yake yi ya k'ara nauyi sosai Amina kin ga dai duka sati daya rabona da shi amma ya yi mini girma a ido ashe Hauwa bata da hankali dama."
Shiru kawai na yi ban ce masa komai ba zuwa yanzu ai ya kamata ace ya gane halin matarsa muguwar ma'karyaciya ce mara son zaman lafiya.
Kwanana biyu da dawowa yara sun yi doki da murna haka zalika ma masu aiki aka kewaye ni ana ta farinciki na dawo na zama kamar ba'kuwa har Baban nasu ya dinga kishi yana jin haushi wai shi ba su damu da shi ba.
Yadda ya hak'ikance yana fad'a abin ya yi ta ba ni da dariya.
Da daddare Salim da Adam suka shigo mun jima tare da su a falo muna hira nan Salim yake gaya mini ai yana da lambar wayar Kamalu har ya kira shi ma ya taya shi murna tafiya karatun da zai yi.
Ikon Allah kenan gabad'aya yaran sun samu wata iriyar nutsuwa mussaman shi Salim din da ya canza ko maganarsa ma cikin nutsuwa kuma duk wadda zai furta mai muhimmanci ce.
Lallai Allah yana kishin bayinsa ya sanya musu nutsuwa da tawakalli babu uwa babu uba, haka zalika babu 'yan uwan uwa nagartattu.
Dangin Babansu ne kawai masu nagarta sai Kuma uban rikonsu a yanzu wanda ya zame musu bango.
A wannan ga'bar shi kansa maigidan na sara masa domin ya yi namijin kokari kwarai da gaske duk abinda uwarsu ta yi masa na illatarwa ya ture ya rungumi yaran abokinsa domin cikashe wasiyyar da ya bar masa.
Hakika ya zama uban marayu ni ce sheda tunda ni ma ga nawa nan ya runguma har yana b'acin rai idan an yi masa godiya bisa abinda yake yi musu.
Sati daya da dawowata komai ya daidaita a gidan mun samu nutsuwa da kwanciyar hankali tun daga kan maigayya da aiki yaran dai kaf muna tare da masu aiki muna cikin nutsuwa da walwala ba ni da damuwar komai tunda ba ni ganin gilmawarta balle ta takale ni ko ta gaya mini banzar maganarta.
Ya je ya yi mata kwana biyu ya zo ya yi mini kwana biyuna haka muke yi babu canji kuma shima yana ta ko'karin ganin ya yi adalci domin dai ya nemi zaman lafiya kuma ya samu ta sashena domin ba ni da niyyar d'aga masa hankali akan komai tunda ba ni nake auranta ba abinda yake gabana a yanzu rabuwa da abinda yake cikina lafiya.
Ranar wata lahadi girkinta ne tunda gari ya waye bai shigo ba.
Hakan sai ya d'an dame ni tunda bai saba da yin hakan ba yana shigo mana ya jima tare da mu a yi hira haka zalika ma ranar girkina yana zuwa gidanta ya d'auki wani lokaci kafin ya shigo mana.
Na fara nemansa a waya gashi dai tana shiga amma sai a katse na kira ya fi sau shida idan ta shiga sai a katse.
Ga yara tun safe sun tafi tahafiz sai yamma balle na tura Khalil gidan.
Bai kira waya ba kuma bai shigo ba abin dai da mamaki.
Wayarsa kuma na kira ana kashe mini.
Ban zarge shi kai tsaye ba sai dai zuciyata ta shiga wasi-wasi akan hakan.
Gefin magriba ya kira ni na daga da sauri na ji muryarsa a dashe don da 'kyar ma yake magana yana yi tari na sar'kafe shi yake gaya mini baya jin dadin ya tashi da mura da zazza'bi har da tari.
Har da ba ni ha'kuri bai shigo ba kuma bai kira ni ba."
Gabad'aya jikina ya mutu na dinga yi masa sannu.
Tabbas bai iya mura ba tunda ta ta'ba kama shi a gidana farko-farkon auranmu na yi jinyarsa.
Na ce masa idan an jima za mu shigo tare da yaran gabad'aya mu duba ka Allah Ya sawwa'ke." Ya amsa da Amin muka yi sallama.
Na zauna cikin damuwa da mamaki.
Hauwa ce kenan ta dinga kashe mini waya a maimakon ta d'aga mu yi magana take ganin k'yashin yin hakan.
Humm! shine yake ganin za mu zauna lafiya da ita har yanzu bai san wacece matarsa ba Gabad'aya lamarinta ni yanzu tsoro yake ba ni wallahi da jefa ni cikin fargaba.
Ba ni da nufin zalintarta ko cutar da ita shiyasa ma muddin nasan ranar girkinta ne ko ya shigo wajena ba ni sakin jikina da shi balle tsautsayi ya sanya mu shiga hakkinta.......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....
BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*159*
Bayan isha'i na fito cikin hijabina har k'asa kai tsaye d'akinsu Baba Tabawa na nufa, ita da Taburni suna zaune cikin fahimtar juna suna hira Sultan na tsakiyarsu da abin wasansa yana ta wasa gefe guda kuma flat ne da abinci a ciki da alama nasa ne za ta bashi wasa ya d'auke masa hankali
Gaisawa muka sake yi kafin na ce." Sultan za a ba ni aro za mu je gabad'aya domin duba Babansu ne ba shi da lafiya yana ta fama da mura da zazza'bi."
Baba Tabawa ta ce." Subahanallahi ashe ba shi da lafiya dama?"
Na ce." Yau dai ya tashi da ciwon shiyasa ai bai shigo mun gaisa ba." Taburni cikin mutuwar jiki ta furta." Tabbas kuwa, don Allah a yi masa sannu da jiki Hajiya Allah Ya sawwa'ke."
Na amsa da Amin zan gaya masa in sha Allahu."
Muka fito daga d'akin tare da Baba tana ri'ke da yaron tana fad'in." Hajiya Amina ko dai mu je tare ne ya yi miki nauyi ga yanayin jikin naki kema Allah dai ya budi ido lafiya."
Na ce." Bari Khalil ya fito ya d'auke shi ai na ce miki tare duk za mu je da yaran."
Ta ce." To hakan ya yi.
Muna tsaye yaran suka fito tare da Mairo dama kafin na shiga sallah na sanar da su.
Kowacce da hijabi a wuyanta.
Khalil ya fito shima na ce ya d'auki yaron.
Suka yi gaba gabad'aya na bi bayansu.
Muna fita farfajiyar gidan masu hidima da gidan suka fara rige-rigen gaishe ni, ina ta amsawa da kulawa, tunda babu lefi tsakaninmu da su akwai mutunta juna sosai.
Masa'udu da yake akwai sabo a tsakanin da yaran dalili shine yake jigalar kai su makaranta
yana ta tsokanar Usaina itace mai tsotsar hannu tana hararsa tana fad'in." Na daina kai ne kake yi ai kai ka koya mini.