Sashe 261
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aikuwa sai ta zama abar tsokanata bini bini da abin ya fado mini sai nasa dariya ina kallonta har dai ta tsargu ta fara kame-kame tana sake jadadda mini da gaske take yi kuma ba ta fad'i domin na yi mata dariya ba tsabar farinciki ne ya sanya ta kasa rufe bakinta.
Ni kuwa na ce ai dariya kam yanzu na fara tunda har lafiya ta samu to auren zai tabbata da izinin Allah.
Ban sanar da maigidan ba sai da ta gama shan maganin na tsayin sati uku tukkuna lokacin ta kara kasantuwa cikin jazaba irin ta buk'atar ruhi da gangar jiki kuma ba ta jin kunyar gaya mini yanayin da take ciki ba.
Ranar da girki ya dawo hannuna bayan mun nutsu ni da shi na gaya masa halin da ake ciki.
Ya yi murna sosai yana fad'in abu na gaba a tsakaninsu zuwa yin gwaje-gwaje kamar yadda zamani ya zo da shi domin samun nutsuwa da kwanciyar hankali.
Ni ma hankalina zai fi nutsuwa da yin hakan daga kowane bangare a samu daidaito.
Alhamdulillahi kowane irin tes an yi kuma sakamako mai kyau ya fito na genotype ya yi mini dadi sosai Hauwa AS Sukairaju A-A Bangaran blood group ma komai ya daidaita yadda ake so.
Tsakanin shi da ita sai na rasa wanene ya fi farinciki kasancewar yanzu na taka tudu biyu sai girman da yake ba ni ya kara tsananta duk da maigidan ya gaya masa yayata ce amma risina mini yake yi kuma ba shi yarda mu had'a ido.
Ni dai da muka dawo daga asibitin a mota na bar su shi da ita suna zantawa.
Ina shiga ciki na riski Hauwa tare da Mairo a falo suna hira yaran dama sun tafi skull tun safe.
Na zauna kan kujera cikin hijabi don ban iya cire shi ba ganinta a falon a zaune sai nake tambayar zuciyata dalilin zuwanta.
Muka gaisa sosai da sakakkiyar fuska abin har ya so ya ba ni mamaki amma dai na share ban nuna mata na ji dadin zuwanta ba haka zalika kuma ban nuna mata na ji haushin ganinta ba ta ce mini sallama ta shigo ta yi mini farkon wataran maulid wanda saura kwanaki uku kacal mu shiga za ta tafi umara kasa mai tsarki.
Na taya murna sosai da fatan alheri mu kad'an ta'ba hirar yara kad'an kafin ta tashi da zumar tafiya ni ma na mi'ke har bakin kofa na taka mata ta fita tukkuna na dawo falon na ce da Mairo ta shiga kicin ta cewa Baba Tabawa su dafa zogalen nan da Masa'udu ya kawo mana tsaraba daga garinsu domin kafin maigidan ya fita ya ce a yi masa kwadonsa idan ya dawo da yamma zai ci.
Ta tashi da azama kuwa ta nufi kicin goye da Hassan a bayanta.
Usaini kuma ina da tabbacin yana bayan Taburni tunda kusan tare suke rainon su biyu wasu lukutan Hadiza da Baba Tabawa na sanya musu hannu.
Hadiza ta shigo cikin annashuwa sai na fashe da dariya ina kallonta cikin zolaya na ce." Masoya masu kafasiti Hadiza na fahimci Sukairaju ya saye zuciyarki kina sonsa ba."
Ta zauna tana kallona da murmushinta har yanzu ta ce." Sosai kam, kin san lokacin kuruciya sakarci muka dinga yi na zo na za'bi mugun mutumin nan Alhaji Halilu Umma da Baba Sule suka rud'e saboda watsi da kudin da yake mini, lokacin wallahi ban san menene so ba Amina ni ma kudi da jin dad'in kawai nake hange ashe mugu ne azzalimi na ci wahala a hannunsa ba kad'an ba."
Na gyada kaina a tsanake na ce." Kaddara ce ai Allah ya zano shi a matsayin mijin da za ki aura amma shawara anan shine kada ki yarda ki nuna masa tsananin son da kike yi masa maza suna da wani abu a duk lokacin da suka gane mace na mutuwar sonsu to sukan kwatanta rashin adalci a kanta.
Amma ba duka ne suke da wannan halin ba.
Ban ce kada ki nuna masa k'auna ba amma daidai misali."
Ya gyad'a kanta a hankali tana fad'in." In sha Allahu zan lura amma fa ni kaina yanzu ne nake jin ina soyayya Amina."
Na yi shiru ban ce komai ba sai ta cigaba da cewa yanzu muka gaisa da Hauwa a farfajiya ta tare ni da fara'a sosai abin har ya ba ni mamaki."
Na ce." Ta sauko ai tana neman shiri ta zo yi mini sallama ne wai za ta tafi umara cikin satin nan."
Ta ce." Allah Ya kar'bi ibada ya sa ta je lafiya ta kuma dawo lafiya."
Na amsa da Amin ta d'an yi jim kafin ta cigaba da cewa." Wai tambayata take yi yaushe zan je gidanta mu gaisa sai na ce mata zan zo in sha Allahu.
Shine ta wuce tana cewa wai tana saurarena kafin ta tafi umara."
Na ce." Wata gaisuwar kuma za ku yi bayan wadda kuka yi a yau Hadiza?"
Ta ta'be bakinta tana fad'in." To ni ma haka na gani sabon salon makirci ne ai babu inda zan je kuma ni ban yarda da wannan faram-faram din na ta ba, hausawa suka ce ruwan da ya dake ka shine ruwa.
Ban ce komai sai murmushi na saman lebe Hauwa kenan neman mutane take yi yanzu ga shi kuma ba ta iya mu'amula ba.
Nusaiba ta sha gaya mini wai tana kiranta a waya ita har tana mamakin a ina ta samun lambarta yarinyar da ta yi wa zagin tsamar nama da cin zarafi shine yanzu take janta a jiki saboda tana kishin yadda yaran ke dabdala a gidana domin ko zuwan Salim hutu nan wurina yake d'aukar abinci kamar yadda d'an uwansa ke zuwa ya d'auki na rana da daddare Adam kwana ne kawai ba ma yi a tare a gidan.
A can gidansu yake kwana tun bayan abinda ya faru da Nabila to yanzu kuma sun juya Legos din shi da Salim din domin cigaba da gudanar da abinda zai kawo musu cigaba a rayuwarsu.
Lamarin yana yi mata zafi ba tun yau ba na lura da cewa ta tsani duk wanda zai ra'be ni shima sai ta dasa masa k'iyayya.
To yanzu kuma taga hakan bai yi ba ta fito da wani salon.
Lambar waya ai ba za ta yi mata wahala ba ko a wurin mijinta za ta iya samu.
Kafin ya shigo gidan ya kira ni a waya yana fad'in zogalan nan da Masa'udu ya kawo dama buhu guda ne d'anye sai uwar doya da albasa ya ce a dibarwa Hauwa na ce to ina mamaki shin shine ya gaya mata ko kuwa a takaice dai na ce." Zogalan kad'ai ka gaya mata an kawo ko da sauran abubuwan?''
Na ji shi yana fad'in.'" Shi tace tana buk'ata idan ma aka ajiye shi zai bushe ko ya lalace ku d'ibar mata tunda tace tana buk'ata."
Na ce." Ba wani lalacewa da zai yi ai kana son miyar zogale sai mu busar da shi."
Ya ce." A d'ibar mata dai na ce." Sai na tare shi da sauri ina fad'in." Ai shine na ce iya zogalan kawai ka gaya mata an kawo ko da sauran tsarabar."
Ya ce." A a ni ban gaya mata ba Giwa mun yi waya ne yanzu take gaya mini ta shigo yi miki sallama bayan ta fita suka gaisa da Masa'udu tasan ya yi tafiya zuwa garinsu shine ya gaya mata abinda ya kawo muku."
Na ce." To tunda hakkinta za ta fitar mata ai kamata ya yi ta buk'aci sauran kuma saboda neman magana ni me yasa ba zata gaya mini ba."
Cikin k'osawa ya furta." Ba ni son 'karamar magana ta zama babba Amina kwana biyu abubuwa sun yi sanyi dalili na fahimci kowacce a tsakaninku kada ki girmama lamarin don ta sanar da ni ba wani abu ba ne, ni kuma ai gashi na gaya miki."
Na ce." Munafurci ne kawai idan da yarda babu wani nufi a zuciyarta ai ni ya kamata ta gayawa tana buk'ata tunda tana da lambar wayata."
Ya datse kiran ba tare da ya ba ni amsa ba.
Kicin din na shiga na ce su raba tsarabar nan kashi biyu daidai a bawa Hauwa.
Hadiza dake gyara alayyahu ta ce." A a ai nan kuke da yawa Amina na yi zaman gidan iyali na gani kin san dai Alhaji Halilu matansa biyu ni ce ta uku ko, to duk abinda ya kawo nawa ne kad'an tunda ba ni da yara.
Me zai sanya za a yi haka kuma?"
Ina dariya na ce." To Masa'udu garin kaud'insa ya gaya mata ya kawo tsarabar zogale da albasa tare da doya shine tana zuwa gida ta kira maigidan wai tana son zogale.
Taburni ta ce ." Ban da abin Hajiya Hauwa ai ke da ita duk daya ne sai ta gaya miki tana buk'ata ta shigo ta dibi yadda ranta yake so."
Murmushi kawai na yi ban sake tankawa ba Ina jin su suna ta magana.
Hadiza na fad'in." Idan an raba an bata biyu ba a yi miki adalci ba."
Anan ne na ce to wannan tsaraba dai ta Masa'udu na neman ta janyo cecekuce ayi dai yadda na ce din idan ma kyautar da su za ta yi shikkenan a bata zogale ne dama yake yi mana wahala don ta doya da albasa wannan ai ba matsalarmu ba ce ko ku raba daidai a had'a mata cikin buhu sai ta aiko ta d'auka."
Na juya na fita daga kicin ina jin maganganunsa akan lamarin.
Yana kuwa shigowa da abinda ya fara kenan na ce an raba kashi biyu ta aiko ta d'auka ko kai ka d'auka ka kai mata.
Yadda na fadi maganar a harzuke shine abinda ya sanya shi tsirawa fuskata ido yadda ya nuna kamar abin ba na tashin hankali ba ne gashi ina ko'karin girmama shi.
Ni abinda ya ba ni haushi yadda ta kasa tambayata sai shi zata tambayata tunda ai Masa'udu direbansa kuma shi ya kawo kayan babu buk'atar ta tambayeni wanda yake zaune dominsa shi za ta tambayata ni ban isa ba.
Yanayin yadda ya damu da lallai sai an bata tamkar wadda ta bawa umarni.