Sashe 108
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wato ana zaton wuta a ma'kera ashe Baban Saude mutumin kirki ne na gaske ban sani ba, lallai anti Yagana da mutanan da suke masa wani irin kallo sun d'auki alhakinsa domin kuwa mutum ne nagartacce mai mayar da d'an wani nasa, irin wad'annan mutanan masu tsage gaskiya da gudun abin duniya sun yi 'karanci a wannan duniyar.
Ina komawa d'aki anti Yagana ta kira ni a waya na daga tare da jin d'an faduwar gaba domin kuwa ban san dame take tafe ba.
Sama sama ta amshi gaisuwa kafin ta fara gaya mini dalilin da ya sanya ta kira ni a waya.
Na ce mata ai yanzu ma Baban Saude yake sanar da ni komai.
Sai ta ja tsaki da alama har yanzu ciki take da ni don dai na yi mata nisa ne babu yadda za a yi ta zo inda nake ta huce fushinta saboda sanin halin maigidan , shiyasa haushina da take ji ya sake ninkuwa.
Shiru na yi Ina sauraran duk maganganun da take yi uffan ban ce mata ba domin Ina iya yin magana ta ce na yi mata rashin kunya domin mu rabu lafiya duk abinda ta ce mini sai na ce to, ta kashe wayarta bayan ta gama gaggaya mini maganganun da ranta yake so da sunan jan kunne da gargadi akan zuwan da zai yi har tana cewa tasan ba ni da mutunci za a iya had'a baki da ni a wulakantashi da tozarci saboda yin hakan a wurin Baban Saude abu ne mai sau'ki dalilin da ya sanya ta kira ni kenan ta gaya mini sun yi waya dashi tun jiya kuma ya tabbatar mata da cewa da zummar sulhu zai zo.
Ajiyewar wayar na yi raina fes cikin zuciyata na ce da ke dashi dukkaninku ba kwa son gaskiya, ko yanzu ai na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, na d'auka ai girman kai ba zai bar shi ya tako kafarsa ya zo ba, ai na ji dad'i mutuka da gaske da yadda Baban Saude yake da kafiya da dagiya akan ra'ayinsa.
Duk da kwarjini da haibar da yake da ita ina da tabbacin hakan ba zai firgita Baban Saude ba dalili shi ma mutum ne mai ra'ayin rik'au kuma mai tattare da wadatar zucci.
Washe gari da safe bayan mun karya kummalo na koma na kwanta bacci mai nauyi ya d'aukeni ko kadan ba na tare da wata fargaba ko zullumin abinda zai faru idan ya zo garin shiyasa kwata-kwata ma ban sanya abin a raina ba don ni har so nake ma ya zo din naga yadda za ta kaya wannan shi zai nuna mini cewa yana sona da gaske ko kuwa duka karya ce da yaudara.
Sai wajan daya na rana na tashi rana gatse-gatse ina fitowa tsakar gidan da zummar wanke bakina da burushi na sami matan gidan suna ta aiki na yau na daban ne domin Sayyada na hanga a can cikin kicin ta dasa kujera tana ta suyar kaji.
Mama tana gyara alayyahu ita kuma anti amarya tana tace zo'bon da yake kan wuta.......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.
Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.
'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.
A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*71*
Abinci muka ci a tare hankalinsa duk rabi yana kaina don ma ni ce karfin cin abinci.
Da ga karshe sai ma ya ajiye cokalin hannunsa yana fad'in shi dan gargajiya ne bai saba da wannan ciye ciyen ba.
A nutse na ce ba sai ka sanya a kawo maka abinda ka ke so ba?"
Ya yi shiru bai ce komai ba can kuma sai ya ce." Amma na ji dadin towon nan da aka sauke ni da shi a gidan kawunki Baban Saude mutumin kirki ne Amina.
Murmushi na yi kad'an amma ban ce masa komai ba.
Shiru ya dan ratsa d'akin a kafin a hankali na ji ya kira sunana.
Na daga kaina na dube shi a tsanake ya furta.
Da gaske fa nake da na ce miki mu d'aura alkawari."
Ina tauna abincin da ya rage a bakina na ce." Ai ban fahimci alkawarin da ka ke nufi ba.
Zamansa ya gyara babu alamun wasa a fuskarsa ya ce." Tsakanina dake babu cuta babu cutarwa duk rintsi duk wahala kada ki zauna da ni da wata zuciya ki amince da cewa ni mai 'kaunarki ne ba kuma zan cutar dake ba, wallahi tallahi Amina da wata ce ta aikata mini abinda ki ka yi mini ba na tsammanin zan sake had'a numfashina da ita.
Domin ke idan ba kya ganin abinda ki ka yi a matsayin ta'addanci da yankan k'auna ni ina gani, domin kuwa abin ya jima yana yi mini ciwo a zuciya." Ya yi shiru yana kallona jin ban ce komai ba sai ya nisa ya cigaba da ce wa ."
Babu ruwana da terere da surutun mutane, ina k'ara gaya miki da wata ce bake ba sai duniya ta ji mu da ita, duk yadda na kai ga boye sirrina da rashin son yamadidi akan lamarina wannan ba zai hana ni yin hukunci ba bayan irin wanda na yi miki, to sai
Allah Ya ragewa aya za'kinta ke ce Amina wadda zuciyata take yi wa mahaukacin so.
Ina sonki wannan kowanene zai shaida haka, kuma ina da burin gama rayuwata dake, ina da burin tara zuria dake koda duka za su kasance miskinai marasa mamora masu dauke da lalurar da kike kyama.
Ni ina sonsu.
Ya sake yin shiru na wani lokaci kafin ya cigaba da cewa." Kamar yadda Kawunki ya fad'a na sani a zaman aure dole akwai kuskure dole kuma a samu sa'bani amma ina so ki sani sonki da kaunarki ne ya sanya mini wani ciwo mai wahalar magani a zuciyata.
Wannan zafin kishin da zargin da nake nunawa a kanki ba yin kaina ba ne Amina zuciyatace, na sha gaya miki ni mutum ne mai kishi da tsantsami a duk lokacin da na tuna cewa ba ni ne namiji na farko da na fara saninki a matsayin 'ya mace ba zuciyata tana yi mini wani irin ciwo wannan shine dalilin da ya sanya nake kasa sarrafa kaina, amma in bacin haka ai nasan wacece ke tun kafin aure ya ratsa tsakaninmu had'uwarmu ta farko na bijiro miki da wani lamari wanda hakan ba dabi'ata ba ce, na yi da manufar samun dace da macen aure mai tsoron Allah da gudun abin duniya.
Kin fi kowa sanin ibtila'in rayuwar dana fuskanta dangane da matayen dana aura wanda da yawa mutane suka fara dora ayar tambaya a kaina.
Auranki shi ya korar da wannan rud'anin ki ka yi hakuri ki karbe ni a haka da wasiwasin za ki mutu ko kuma za ki rayu.
Wannan sai ya bawa sauran mata damar kawo mini hari da sunan soyayya tunda ai kin rayu tsayin shekara ba ki mutu ba.
Amina in bacin Hauwa 'yar uwata ce, kuma ina gudun 'bacin zumunci da babu dalilin da zai sanya ni na aureta tunda a can baya ai guduna ta yi saboda kada ta rasa rayuwarta kamar yadda 'yar uwarta Samira ta rasa tata rayuwar.
Aurena da Hajiya Maryam kuwa wannan cikasa wasiyyar abokina na yi domin a cikin abinda yake rubuce cikin wasiyyar da ya rubuta da hannunsa kafin rasuwarsa har da neman alfarmar na auri matarsa domin cigaba da kula da ita da yaransa.
Alhaji Amadu ya wuce komai a wurina domin duk yadda zan fad'a miki kirkinsa sai na rage mutum ne na k'warai mai kaunata da son cigabana.
Ko ni ne na riga shi tafiya ba abin mamaki ba ne don na bashi wasiyyar ya auri iyalina saboda rufin asirinmu bakid'aya.
Mu zauna lafiya don Allah, ki yi hakuri da ni, zan yi hakuri dake.
A yanzu ke ce uwargina da ni da sauran iyalina muna hannunki.
Muddin ki ka bud'e wata kofa ta samun sa'bani a gare mu to kin kashe kanki.
Sai maganata dake ta karshe kada ki sake kaini 'kara wurin kowa domin kuwa ni ba yaro ba ne, ke ba ki ji kunyar kai mutum kamata 'kara ba Amina ke ce fa ki ka yi mini lefi kuma na yi shiru ban gayawa kowa ba amma saboda k'in gaskiya sai ki tafi ki kai ni 'kara na ji ciwon hakan sosai, kuma kin ci sa'a, ina sonki da ba zan je ba wallahi zan ta barinki da igiyoyin aurena a kanki duk ranar da ki ka gaji kya dawo dakinki."
Cikin kuka na ce." Ai kai kaso hakan, mai yasa ka'ki ha'kura, ai na gaya maka gaskiya ban 'boye maka ka dalilina ba, kuma da na fahimci na yi kuskure ba 'a yi wa Allah wayo na yi nadama na ro'ki gafararsa, kaima na ce ka yafe mini, sai ka k'ullece ni, ka dinga gaba da ni, ka rufe duk wata hanyar da kasan zan hadu da kai, ta ya ya ba zan nemawa kaina mafita ba, ai Allah ma muna yi masa lefi ya yafe mana, a lokacin ya kamata ka kar'bi tubana mu sasanta junamu ta inda babu wanda ya ji ya kuma ga ni, hakan bai yi maka ba sai kawai katin d'aurin aurenka na gani, ni ma shine dalilin da ya sanya kenan na nemi iyayena domin su kira ka su ji menene matsayin aurena."
"To mai yasa ba ki sanar da mahaifinki ba har sai kin yi tafiyayyiya kin je kin gayawa wani mutum, a ganina ai mahaifinki shi ya kamata ki sanarwa da halin da ki ke ciki Amina ba wai ki d'auko maganar ki kawota har nan garin maiduguri ba."
"Shi ma ai Baban Saude ba bare ba ne, kamar yadda ya yi maka bayani uba yake a wurina.