← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 192 OF 276

Sashe 192

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri na ce." Wanene lafiya?"
"Itace yau ta tashi da jiri shine Hajiya Saratu ta zo ta d'auketa suka je asibitin Malam Aminu likitanta ya dubata amma dai alhamdulillahi tunda yadda ta fita da kafarta haka ta dawo da k'afafunta ta kuma ta ci abinci tasha magani shine bacci ya kwasheta."
littafin nan na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba
Ajiyar zuciya na sauke da damuwa na ce." To Allah ya sawakke kada ka tasheta yanzu da safe dai kace mata na kira ta.''
Ya ce." To Mama amma ya jikin Baba?''
Na ce." Jiki alhamdulillahi Kamalu yanzu ma kiran da na yi mata kenan domin na gaya mata cewa ya tashi har ya ci abinci ana hira dashi."
Ya dinga fad'in." Alhamdulillahi Ubangiji Allah mun gode maka."
Na ce." Da safe zan kira in sha Allahu" Daga haka sai na datse kiran na nemi Hajiya Saratu bugun farko ta shiga ta daga na ji muryarta cikin tashin hankali tana fad'in." Amina Allah dai yasa lafiya."
A tsanake na ce." Lafiya lau Mamana na kira ne domin na yi miki albashiri."
Ina jin lokacin da ta saki ajiyar zuciya a kagauce ta furta." Ya tashi ne?"
Na ce." E, wallahi cikin nutsuwa kuma yadda mai dawainiya dashi yake fadi har ya yi wanka ya ci abinci ya kuma buk'aci wayoyinsa."
Ta dinga godiya ga Allah ina jinta muryarta har tana rawa take fad'in." Amina wallahi da na ga kiranki da farko sai da gabana ya yanke ya fadi haka kawai sai zuciyata take raya mini za ki ce mini Tajo ya rasu.

Yau tun safe na kai Hajja asibiti saboda ta kasa nutsuwa bata bacci ba ta cin abinci hakan ya haddasa mata jiri da ciwon kai kuma kin san tana da hawan jini fadi take yi wai ta san ya rasu b'oye mata ake yi."
Na ce." Na kira Kamalu yanzu ai yake yi mini bayani na ce to bari na sanar dake tunda yace bacci take yi."
Ta furta." Ai yanzu zan sake komawa gidan in sha Allahu.

Amina mun gode sosai lallai mata suna suka tare a gidan Tajo ina yi masa murna ya yi dace da mace tagari mai tausayi da kuma soyayya ta domin Allah.

Abinda Maryam ta yi mana kuma mun barta da hasken rana fad'uwarta Ubangiji shi zai yi mana sakayya."
Na ce." Amin Mamana, ai babu godiya a tsakaninmu mijina ne kuma shi ma ya yi mini tarin alheran da ba zan iya lissafasu ba ni ya kamata ace na tsaya kan gaba wurin bashi kulawa."
Ta dinga fad'in." Hakane wannan Amina hakane."
Na dan yi shiru ina jinta da kuma nazarin maganganun da na furta wata zuciyar tana gaya mini kamar na yi mata rashin kunya akan dan uwanta ina cewa ni ya kamata a kan gaba wurin kula dashi bayan suna raye da ita da mahaifiyarsu can kasan zuciyata kuma na gaya mini cewa babu rashin kunya sai tsage gaskiya domin duk cikinsu ke kin fi amfanarsa kuma abokanan rayuwa ne wanda idan babu daya a tsakani dole kowanne ya shiga yanayi na tashin hankali."
To a daran duk wanda ya cancanta sai da na kira shi na sanar da shi har Babanmu sai da na gayawa ya ce da ni gobe zai zo ya duba shi tunda nan nan ne bunkure.

Aikuwa sammako su Hajja suka buga a gidan Malam ni dai ina bacci na ji maganganunsu na tashi zaune wanda ya yi daidai da shigowar Hajiya Saratu na saki fuska sosai ta shigo tana fad'in." Bacci ki ke yi Amina."
Na ce." Wallahi kwashe ni yayi ban yi tsammani ba Mamana ina kwana ya hanya."
Ta amsa da kulawa sosai tana dan kallona da murmushi a fuskarta.

Hijabina na zura a jikina muka fito tare Hajja ana ta hira da matan malam har da dariya abinda ban taba gani ba duk zuwan da suke yi.

Muka gaisa sosai da ita ina ta mamakin ganin yadda ta watstsake har take ta magana haka.

Rabi'u ya zo suka gaisa kafin ya ce Malam yana magana."
A wannan karon ma tare muka shiga d'akin malamin yana ta k'amshin turaran wuta na tsinke kamar dai koyaushe tsaf ko'ina babu kazanta balle abubuwan da zai nuna malamin matsubbaci ne.

Al'kur'anai ne gasu nan a jikin bango a rataye a cikin jaka gefan buzunsa kuwa tarin littafan addini ne masu yawa da irin carbin nan zabgege mai dubu.

Yana zaune cikin tsafta da shiga ta Kamala yayin da majinyacin nasa yake can gefe zaune a kan shimfidar da aka yi masa amma sun dan sanya fillo sun tokare bayansa.

Yana sanye da wata babbar riga ta shadda wadda take nuna alama ta malamin ce ita kadai ce a jikinsa sai dogon wando don daga cikin rigar ma ana gano fatar jikinsa sai dai fa gilashin nan nasa na bala'i yana idonsa wato komai d'an lafiya ne.

Shi ma al'kur'anin ne a hannunsa lokacin da muka shiga har da shi wajan amsa sallamar mu gabad'aya hankalinmu na wajan da yake haka zalika shima idonsa na kanmu na yi kokarin daidaita nutsuwata sosai domin yadda zuciyata take ingizani zuwa wurinsa sai nake ganin hakan ba daidai ba ne kada za'kewata ta yi yawa.

Amma zahiri Ubangiji ne kad'an yasan yadda nake jin wani mugun dad'i da k'aruwar sonsa a cikin zuciyata.

Tunda muka had'a ido sau daya na yi k'asa da kaina smma na saki fuskata sosai a haka muka gaisa da Malamin na zauna gefan Hajja yayin da nake saurarar maganar da suke yi cikin jin dadin yadda Ubangiji ya sassauta lamarin ya kuma kawo sau'ki cikin dan kankanin lokaci har yana fad'in zuwa gobe ma za mu iya tafiya gida tunda jiki ya yi kyau domin ya cigaba da gudanar al'amuransa."
Hajiya Saratu ta nufi wajansa ina jin suna magana ban dai ji komai ba smma yanayinsu gabad'aya ya ba ni tausayi kwarai da gaske kaina a kasa na ga Hajja ta tashi itama ta tafi wajensa.

Na kasa tashi har sai da malamin ya ce mini malama Aminatu je ki duba maigidanki."
Na yun'kura na tashi da tahamidi domin duk motsin da zan yi a yanzu godiyar Allah ce.

Na d'an tsuguna gefan kafafunsa ina fad'in." Baba ya jikin Ubangiji Allah sanya kaffara ce, Allah Ya warware ya kara maka lafiya."
Yana kallona ya ce." Amin Amin Ya hayyu ya 'kayyumu." Hira suke yi a tsakaninsu kaina a k'asa ba zato na ga ya kamo hannu na sai na dube shi da sauri muka had'a Ido sai ya saki hannun da sauri yana duban su Hajja to mantawa ya yi da suna wajan oho kuma sun ga ni da ri'ke hannun da sakin da ya yi kamar wanda ya kama wuta.

A zuciyata na ajiye hakan da kewa da kuma yadda yake jina a ransa.

Da yake kusa da k'afafunsa na zauna sai ya d'an dinga sanya k'afarsa daya yana ta'bo ni idan na kalleshi sai ya yi mini murmushi na d'an janye kad'an ina mamakin abinda yake yi gashi magana suke yi a junansu amma hankalinsa na kaina gabad'aya har sai da suka fahimta ganin hakan ya sanya ni saurin tashi ina fad'in." Hajja sai kun fito."
Ta ce." To Amina ai yanzu za mu fito mu tafi gabad'aya domin Uwani tana kan hanya ba ni so ta zo ba ta same ni ba d'azu da wurwuri kafin mu fito ta kira waya tana gaya mini.

Na ce." To Allah Ya kawo su lafiya."
Kafin na fita sai da na d'an risina gaban malamin tukkuna sannan na fice zuciyata cike da tunanin abinda ya yi wato shi dai mai hali baya fasawa amma in ba haka ba a gaban mahaifiyarka ma ba za ka saurara ba kuma kai da kwana daya kacal da tashinka......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[5/3, 2:50 PM] +234 803 054 1544: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.

Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.

To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.

Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu.

Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya.

Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne.

To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji.

Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba.

Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu.

In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi.

Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama.

Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.

Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki.

Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki.

Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu.

Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
*Gudun aure paid book 2k complete on telegram.
Chapter 192 · 0% Book details