← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 276

Sashe 123

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar mai koyon tafiya haka na dinga jan k'afa ina kuka na isa gefan gado na zauna kamar an kwad'e mini gwiwata da tabarya lallai Allah Ya jarrabeni da shu'umin mutum.

Ya biyo ni shima kamar wanda aka kuzawa ruwan sanyi jikinsa duk a sanyaye.

Yana zama a gefena na yi kukan kura cikin wani yanayi na bazata na sake kai masa naushi a kirjinsa ya kuwa yi kwanciyar da bai shirya ba na zabura da sauri na d'auki fillo na raba k'afafuna akan ruwan cikinsa na danna masa fillon a hancinsa ina ihun nake fad'in." Sai na kashe ka wallahi, na yarda ni ma a kashe ni, ni ce ajalinka tunda ba zaka bari na huta ba."
Fad'a sosai muka dinga yi tiki tiki yana yun'kurin tashi ina sake turmushe shi nauyina gabad'aya na saki a kansa ina kuka.

Cikin tashin hankali da nishi tare da fitowar numfashi ya fizge a guje ya dira daga gadon yana kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!

Bai fita ba yana tsaye a bakin kofar d'akin ya ki'dime sosai ko da ya ga na sake durfafoshi bai yi yun'kurin bude kofar ya fita ba.

Ina isa kuwa ya kama ni da karfin da ban san yana da shi ba.

Cikin rawar murya da tsananin damuwa yake fad'in." Yi ha'kuri, ki yi hakuri na ji na yi lefi, amma ki fahimce ni ki bari na gaya miki abinda yake zuciyata kafin ki kashe ni din."
Na yi shiru hawaye na fita daga idona, ina jan hanci na ce ." Wallahi ba zan sake yadda yarana su zauna a hannunka ba" Ya ce."
" Ki fahimce ni Amina, ban za'bi bangare daya na ajiye daya ba.

Ni kaina lamarin ya sanya ni a rud'ani ba kad'an ba.

Shirun kuma da na yi ba ina nufin na goyi da bayan maganar Salim ba.

Ina bincike ne da kuma hanyar da zan kawo gyara.

Akwai nauyi mutuka da gaske na tunkareki da maganar nan.

Akwai kunya na titsiye yaron nan Kamalu ina neman hujja akan maganar Salim.

Kada ki zarge ni bayan ba ki san menene a zuciyata ba.

"Na gaya maka wallahil-azim ba zan yarda da kanzon kurge ba.

A wannan ga'bar ko ni ko kai, Kamalu da Yusi fa ba su rasa madogara ba.

Sannan Ubansu ba makwad'aici ba ne, ba mazinaci ba ne, sannan ba b'arawo ba ne.

Banga dalilin da zai sanya a dinga jingina musu manya manyan sharri ba.

Ban nemi ka rike mini yara ba.

Haka zalika ma ban nemi matarka ta ri'ke mini yarana ba.

A ba ni kayana mana dole ne, zan iya rikesu mu rayu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali."
"To ni kuma muddin a karkashin ikona ki ke yaran nan babu inda za su je muna tare har abada, tunda ina tare dake ni ba zan iya rabuwa dake ba."
Na dube shi ina gyada kaina na ce." Haka ka ce ko?''
"Kwarai kuwa, haka na ce, sai ki yi duk abinda za ki yi tunda ke ba za ki rarrasu ba.

"Zan kuwa yi, ai ba kai ka haifar mini su, baka da wani ji'bi dasu don haka baka da hujjar da zakace dole sai ka rikesu anan zan nuna maka karfin ikona."
Ya ce." Sai ki nuna din ina jiranki..'' Daga haka ya cika ni tare da jan tsaki ya juya ya fita yana fad'in." Sakarai kawai kullum kina girma kina cin tasono."
Silalewa na yi a k'asan d'akin na yi zaman dirshan na dinga tikar kuka.

An dake ni an hana ni kuka kuma an bi ni da bakar magana.

Wace irin masifa ce wannan mutum bai haifi yara ba ya ce lallai sai ya rike su.

Ina cikin wannan yanayin Hauwa ta shigo sanye da hijabi a jikinta idonta jawur!

Na tashi tsaye da sauri Ina kallonta gabana na fad'uwa.

Minal ta dire mini a gabana tana fad'in.'' Ga takwararki nan Amina ubanta ya ce na tafi gidanmu."
Cikin kad'uwa da muguwar fargaba na ce." Ki tafi gidanku akan wane dalili Hauwa?"
"Saboda na gaya miki abinda yake faruwa." Ta fad'a tana juyawa da niyyar fita.

Na bita da sauri yayin da Minal din ta tawo kataf katafi ta rike gefan hijabinta tana kuka.

Na ce." Shine kuma ke sai ki tafi."
"To dama ai kamar akan 'kaya nake wallahi na gaya miki a gajiye nake." Na ce." Ita Minal din mai tayi miki to?"
"Cewa ya yi na ajiye masa yarinya."
Wani takaici ya yun'kuro mini lallai Alhaji Amadu ya mutu ya bar baya da k'ura.

Iyalinsa na nema su tarwatsawa aminin nasa rayuwa.

Na tabbatar da cewa ba kowane ya janyo wannan hayaniyar ba sai Salim.

Na ce." Yana ina maigidan?"
"Shi ya sani.'' Ta fad'a a takaice tare da sake nufar hanyar fita.

Na ri'ke hannunta ina fad'in." Babu fa inda za ki je Hauwa."
Dariya ta yi irin ta takaici ta ce." Ai ba ke ki ke aurena ba Amina, maigida ya ce na fitar masa daga gida zaman me zan yi."
Jan hannunta na yi muka zauna kan gado na dau'ki Minal na d'ora mata a cinyarta sannan na d'auki wayata.

Kiransa na yi bugun farko ya d'aga kamar yana jira.

Littafin nan na kudi ne Hajiya kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba
Na ce." Yanzu kai don girman Allah ba ka ji kunya ba, tsofai tsofai da kai kake aikata irin abun yara?"
"Mai na yi kuma?

Ke ba kya jin nauyin furta mini maganar da duk ranki ya so ko Amina?''
Na ce." Hauwa dai ko babu aure tana da 'yancin zama na dindindin a gidanka, to balle bayan wannan alakar akwai ta aure da zuria a tsakaninku, da ka ce ta tafi gida kai ba ka ji nauyi ba?"
"Bata da wani 'yancin zama a gidana sai na so, tunda ba ta ji nauyin shure maganata ba, ni ma babu wani nauyinta da zan ji, kuma ina ruwanki matarki ce?"
'Dan sassautawa na yi domin kuwa ba zan so a ce dalilina sun samu matsala ba.

Na ce." Idan saboda ta gaya mini wannan maganar nan ya sanya har ka yanke mata wannan hukuncin ka yi hakuri ka ji."
Shiru ya yi bai ce uffan ba.

Na ce." Ka janye abinda ka kudirta akanta domin kuwa sam bai dace ba."
"Kin yarda ta yi ba daidai ba yanzu?"
Shiru na yi ban ce komai ba.

Ya sake maimaita maganarsa nan ma ban ce masa komai ba.

Ya ce." To tunda bakinku daya kin ga kuwa babu amfanin zama da macan da bata buk'atar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Hauwa kawai ta tafi gidansu kafin na gama yanke hukunci ta san matsayinta, tunda har za ki iya d'aukar fillo ki toshe mini hanci don na mutu ai lamarin babban ne a wurina Hauwa ta samu nasarar tayar mini da husuma ni kuma zan d'auki matakin da ya dace a kanta."
Gwiwa a sanyaye na kashe wayar ina kallonta babu damuwa a tare da ita tace." Ai na gaya miki Amina mutumin nan kaf dabi'unsa sun canza muddin akan lamarin matarsa ne yakan iya cin mutuncin kowa."
Na ce." Babu da inda za ki je." Ta yi shiru tana kallona ina laluban wayar Hajja bugu daya ta daga.

Cikin rawar murya na gaisheta ta amsa tana fad'in duk kuna nan lafiya ko Amina."
Na ce." Lafiya lau Hajja don Allah ki yi masa magana matsala suka samu da Hauwa shine ya ce wai ta tafi gida."
cike da mamaki ta furta." Hauwa ta tafi gida akan wane dalili?"
Shiru na yi ban ce komai ba.

Cike da kulawa ta ce." Amina ki gaya mini menene yake faruwa kin ji ko kada ki rufe mini komai.''
Hawaye suka silalo mini na ce." Hajja Hauwa ba ta yi masa komai ba wallahi, asalima ma matsalar ni ta shafa saboda kawai ta gaya masa gaskiya shikkenan yake jin haushinta."
Ta ce." To gaya mini wace matsala ce, ni zan yi maganinta, Hauwa kuma ki gaya mata kada ta fito."
"In sha Allah, gata nan a kusa da ni, na hana ta fitowa."
"To hakan ya yi ina sauraranki." Tafad'a cikin nuna damuwa.

A nutse na fara gaya mata tun daga farko abinda yake faruwa har zuwa yanzu da ake wannan rikicin.

Hajja ta jima cikin alhini da takaici kafin ta ce." Ki yi hakuri a matsayinki na babba kuma uwa.

Amina tabbas ko ba ki fad'a ba nasan idan za a tona zuciyarki to tanan cikin kunci da b'acin ran wannan lamari.

Ki jure lallai kuma ya zama dole a yi wa tufkar hanci saboda gudun abinda zai afku anan gaba na rashin dadi.

Zan nemi shi zai kuma zo nan inda nake akan maganar nan domin ni kaina ban yarda da hakan ba.

Sannan duk abinda zai yi muku kada ku saurareshi.

Ki jadaddawa Hauwa cewa da yawuna ban amince ta fito ba.

Ke kuma ki yi hakuri kin ji ko, nasan abinda da ciwo a zucci amma in sha Allahu gaskiya za ta bayyana kanta.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.

Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*83*
Na ce." Ai ba ta yi lefi ba gaskiya ta fad'a domin shine zama na amana.

Kuma wallahi a yanzu ni Amina Hauwa ta fiye mini kai sau dubu tunda ka nuna mini zahirinka na gani, ni duk wanda za a had'a kai dashi a k'yamaci abina, ba na daukarsa a matsayin masoyi babban ma'kiyi nake kallonsa."
Da wani irin yanayi a tare da shi ya furta." Idan na fahimce ki kenan kina kallona a matsayin ma'kiyinki wanda ya za'bi Maryam da 'ya'yanta ko Amina."
Na ce." K'warai kuwa wallahi tallahi ba ka cikin jerin masoyana tunda har ka iya yadda da cewa Kamalu zai aikata wannan mummunan lamarin.
Chapter 123 · 0% Book details