Sashe 232
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta kuwa ji dadin yadda na sanyota cikin lamarin hakan ya nuna mini cewa Ummansu Saminu iyakarta take nuna mata akan sabgar.
Ban yadda na gaya musu ga yadda al'amarin ya kasance har auran ya juya kan Usaini ba bayanin da na yi Babanmu haka suma na yi musu cewa yarinyar a can k'auyensu mijina take wato bunkure kuma na je naga gidansu da mahaifinta fitaccen malamin addinin musulunci ne.
Ummansu Hadiza ta saki jikinta sosai muna ta hira yayin da ita kuma Ummansu Saminu na fahimci hakan bai yi mata dadi ba sai ma ta tashi tana fad'in bari ta d'ora abinci.
Ta shigo bayan fitarta da kamar minti goma tana fad'in." Hadari ne a garin nan fa wata'kila yau mu samu ruwa." Ummansu Hadiza da sauri ta ce." Allah Ya sa ai kwana biyu mun sha zafi."
Ta share ta ba tace komai ba ta d'auki wani dan bokiti ta fita.
Na dube ta a sanyaye sai ta ba ni tausayi kad'an wato abinda ta yi wa Mamanmu a can baya ne yanzu take ganin sakamako.
Ban ji dadin irin wannan zaman da suke yi ba ai na d'auka sun girma masu yi wa wasu fad'a ne ni kaina abinda yake faruwa tsakanina da Hauwa baya yi mini dadi ko kad'an don dai babu yadda zan yi ne, amma babu abinda ya fi zaman lafiya dad'i Ubangiji Allah ka ba mu ikon zama da kowa lafiya kada mu cutar da wani domin shi sharri d'an aike ne.
Hadarin ya taso sosai iska ta fara tashi garin ya turnuke farkon damuna muke ciki ga dukkanin alamu za a samu ruwan sama da wuri
Yaran suna tsakargida suna wasa sun samu sake da yake tsakargidanmu akwai yalwa na ji Ummansu Saminu tana fad'in." Ina Gambon taku take ne ko dai ta fita."
Ummansu Hadiza ta leka tsakargidan daidai lokacin da Usaina take k'walawa Minal kira bata gidan da gaske fita ta yi gabad'aya ba mu ankara ba, suma yaran da suke wasa tare ba su lura da lokacin da fice ba.
Na kudi ne don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba
Na tashi da kiran sunan Allah gabana na fad'uwa hijab dina na zura dalili na cire shi jin abinda jikina ya kasa d'auka zafi sosai da kyaikyayin jiki ban sani ba ko dan na jima ina rayuwa cikin ac ne oho amma dai yau yini guda duk na burkice dalilin hadarin da ya had'o da kuma zafin da ake tsugawa.
Muka fita tare da Ummansu Hadiza ma'kota ta dinga shishshiga ni kuma na fara duba yara da suke wasa a layin ban hangi rigar Minal ba.
Kafafuna suka dinga kyarma.
Ashiru ya rufe kwantena ya bazama.
Kasa cire kafata na yi na koma soro na tsaya ina kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Twins kuwa da suka fahimci Minal 'bata ta yi sai kuka Hassana tana fad'in." Kuma bata da lafiya ko Usai."
Ta daga kanta tare da zura yatsa a baki tana tsotsa hawaye na fita.
Na sake karyewa k'warai da gaske tsautsayi ne ya sanya ni taho da yarinyar nan, na tabbatar da cewa idan ba a ganta ba daga nan zuwa dare ubanta da uwarta dole su ji a wannan ga'bar da muke ciki da ni da su na rashin samun daidaito bai zama lallai su yi mini uzuri cewa tsautsayi ne ba.
Za a ce me yasa nawa yaran ban sake sun fita sun shiga lungunan da ba su sani ba sun 'bace.
Ina nan tsaye cikin tararrabi kimanin minti ashirin Ummansu Hadiza ta dawo daga yawon shiga makota babu Minal babu dalilinta
Muka koma cikin gidan jikina a mace k'warai da gaske Ummansu Saminu ta sauke abinci ta ce." Ya kamata ki sanar da babanta Hajiya Amina."
Na zauna saman turmi a nutse ina fad'in." Bari mu jira dawowar Ashiru ba ni tsammanin yarinyar nan nisa ta yi.
Ina rufe baki kuwa sai muka ji kukanta daga soro na tashi tsaye da sauri.
Ashiru ya shigo da ita a hannunsa ta yi wujiga-wujiga ta ci kuka ta k'oshi har da tabon fad'uwa a goshinta da alamun jini kad'an
Na kar'beta da sauri ina dudduba jikinta gabana na ta fad'uwa ta ri'ke ni tamau tana shasheka ina jin Ummansu Hadiza na tambayarsa a Ina ya same ta ya ce tsallaken titi wani mutum yana yawo da ita a han
nu zai nausa da ita titin tudun yola
Na zaunar da ita tare da cire mara riga jikinta da zullumi da fargaba na tube mata wando pant na duba gabanta alhamdulillahi babu wata alama.
Ummansu Saminu ta juye ruwan da yake cikin fulas din shayi na surka na yi mata wanka ta zuba musu abinci suka ci cikin rashin dad'i ta b'ingire ta kama bacci.
Na kasa cin komai saboda tashin hankali tabon da yake goshinta shine ya fi d'aga mini hankali kuma har yanzu zabura take yi. alamun a tsorace take har yanzu.
Sai da na yi sallar la'asar tukkuna na ci abincin dafuduka ta shinkafa har da kifi da ruwan pure water.
Na d'auki wayata domin kiran Ayuba ya zo ya d'auke mu na mayar musu da 'yar su.
Ina laluben lambar direban shi kuma ya kira hannuna ya shiga rawa na daga ban iya cewa komai ba saboda tashin hankali sai nake ganin wata'kila labari ya riske shi abinda zuciyata take raya mini kenan duk da cewar yarinyar ba a san 'yarsa ba ce amma zuciyata ta kasa tsayuwa waje daya.
"Yanzu haka Hauwa tana Dambatta na sanya an kaita Ayuba zai zo ya d'auke ku saboda ganin garin da hadari ina fatan kin kammala uzurin da ya kai ki."
Na sauke ajiyar zuciya a hankali na ce." Na gama." Ya kashe wayar bai sake cewa komai ba.
Na dubi yarinyar har yanzu bacci take yi suna kusa da ita sun kasa sakin jikinsu kamar ma sun gaji da zaman gidan suna so a tafi.
Ko da na tambaye su amsar da suka ba ni kenan mu tafi.
Na sauke ajiyar zuciya wadda ba zata lissafu ba.
A haka na mayarwa da yarinyar kayanta dana cire mata.
Ummansu Saminu ta shigo d'akin tana fad'in." Har yanzu ba ta tashi ba ko?"
Kaina kawai na iya daga mata.
Ta d'an dubeta cikin nazari kafin ta ce." Har yanzu a tsorace take kin ga ni duk da tana bacci jikinta rawa yake yi tana zabura wata'kila garin gudun hadari da iska ta fad'i ko wani ya gwabgeta gashi hadarin ya washe ba mu samun ruwan ba Allah sarki ai an auna arziki ma tunda ba a yi nesa da ita ba.
Na lura yarinyar ta fi yan'uwanta rawar kai in ba haka duka fa suna zaune a tsakargida suna ta wasa a tare amma fitowata daga kicin na ga babu ita a wajan ta fita kuma maimakon ta tsaya a waje ta nausa.
A takaice na furta." Tsautsayi dai kawai amma sam ba da ita na yi niyyar zuwa ba wallahi Babansu ya kawo mini ita cikin mota tana kuka sai ta bi ni."
Ta gyad'a kanta tana cewa." Hakane abinda ya yi kiranta kenan da mutuwa ce ma haka za a shigo da gawarta."
Gabana ya fadi jin abinda take fad'i itafa dama can haka take ba ta tauna magana kafin ta furta gabagadi ce.
Allah Ya kiyaye.
Daga yau ma ba ni ba zuwa ko'ina da yarinyar duk rigimar da za ta yi kuwa balle wani tsautsayin ya faru.
Ashiru ya shigo yana gaya mini ga Ayuba can ya zo.
Na ce ya d'auki yarinyar ya kaita mota.
Na tashi da bismillah muka fito tare da yaran Ummansu Hadiza ta fito daga d'akinta da carbi da alama ba ta jima da idar sallah ba fad'i take yi yarinya kun zo lafiya lau za ki tafi da tabo a goshi abin nan bai yi mini dadi ba wallahi Amina Allah Ya kiyaye gaba."
Na amsa da Amin Ya Allah.
Akwai gyare-gyaren da nake so a yi muku a gidan amma dai zan yi waya da Babanmu tunda yau din bamu samu haduwa ba
wata'kila ma gobe ko jibi a fara aikin saboda ba ni son a ja dogon lokaci cikin satin da za mu shiga nake so a kammala komai mu d'auko amarya ta tare a d'akinta.
Ummansu Saminu ta dago labule da sauri ta fito tsakargidan ta tsaya ba ta ji dadin yadda na tsaya muna sake tattaunawa da Ummansu Hadiza ba.
Ita kuwa sai dariya take yi tana nuna farinciki a zahiri dai ko da tana jin haushi da bakinciki ba ta fito fili ta nuna ba tana ta daurewa hakan ya kara tabbatar mini da cewa lallai ta tuba kuma duniya ta koya mata hankali sannan neman zaman lafiya da sulhu take yi a gidan.
Muka shiga mota Ayuba ya ja muka d'auki hanyar gida zuciyata cike da zullumi haka zalika ma jikina cike da rashin kwari da karsashi ban iya 'karya ba kuma ba zan fara akan wannan dalilin ba domin kuwa ko da na yi domin na kare kaina watarana abinda na rufe zai iya bayyana ga yaran nan da bakinsu ba ya yin shiru ga kuma tabo na daujewa a goshin yarinyar ko shi ya isa ya nuna aya.
Don haka idan ya nemi dalili zan gaya masa.
Yarinya dai ban yi niyyar zuwa ko'ina da ita ba ya kawo ta cikin mota ya ajiye tsautsayi ya kira ta ba kuma a son raina ba.
A gidan muka same shi shi kadai zaune a falo da waya a hannu alamu sun nuna dakon jiranmu yake yi.
Ayuba ya dire yarinyar a k'asa dama shi ya daukota tunda har da muka iso bata tashi ba sai yanzu ta fara wuri-wuri na ri'ke hannunta da kyau ganinmu a gida ya sanya ta d'an nutsu ya juyo yana kallonmu.
Ayuba ya juya ya fita da sauri.