Sashe 245
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na kar'ba kuma na gode amma abinda na yanke shine ya sanya mini shi a kasuwa a kar'bi kudin domin idan har zai cigaba da aiki da sunana akwai matsala babba a tashe shi daga aiki idan ya so na nemi plaza na saya na fad'ad'a harkokina na kuma sanya haya a wasu wuraran."
Ya Falmata da annashuwa ta furta." Wannan tunanin naki ya yi Amina.
Ya kike gani Yagana hakan ya yi ko?"
Ta furta." Ya yi sosai Ubangiji Allah Ya dafa miki amma ta wace sigar za ki tunkare shi har ki gaya masa ya sa a kasuwa ya baki kudin."
Na furta." Ni ma ban san ta sigar da zan gaya masa ba wallahi tunda yanzu fad'a yake ta yi kan cewa ba ya yi mini gwaninta duk abinda ya yi mini na alheri sai na gwasile na ce ga yadda nake so."
Sahura da ta gama sanya kayanta kuma tunda muka fara maganar ba ta ce komai ba sai yanzu ta furta." Sister na taya ki murna sosai Ubangiji Allah Ya yi ri'ko da hannunki lallai kin cancanta da fiye da abinda ya fi haka ma, an yi gwagwarmaya kuma an tari kalubale mabambamta amma ni a shawarce ki bari a kwana biyu lokacin da kuke dad'i da shi sai ki gaya masa tunaninki idan kin ci sa'a zai amince tunda gaskiya yana da sau'kin kai a wasu lukutan."
Anti Yagana ta ce." Ni ma tunanin da na yi kenan ki bari a kwana biyu kun samu nutsuwa dake da shi cikin lumana sai ki gaya masa abinda ki ke so."
Na sauke ajiyar zuciya a hankali na furta.''In sha Allah."
Yusura ta tashi daga bacci ta shiga toilet ta fito na ce ta janyo mana akwatinan kayan nan.
Ta d'auko su d'aya bayan d'aya aka bud'e kaya ne masu kyau da kud'i kuma ta duba quality sosai babu wani k'aramin abu a ciki ko na son zuciya ban san dai iya adadin kud'in da ya bata ba amma ta yi kokari kuma sun yi kyau kayan kwarai
Muka gani gabad'aya Ya Falmata 'yar gayu mai son abu mai kyau sai yabawa take yi da kayan.
Muka gama gani yarinyar ta mayar da su inda suke.
Gaza ha'kuri na yi na sauke ajiyar zuciya ina duban anti Yagana na ce." Nabila ce fa ta had'o kayan nan."
Ta yi kasa'ke da alama ba ta gane Nabilar da nake magana akai ba Sahura ta yi caraf tana ce wa." Nabila wadda na sani 'kanwar Hajiya Maryam mai rasuwa."
Na gyad'a kaina ina kallonta.
Anti Yagana da sauri ta ce." Kamar Yaya dama ba shine ya sayowa yaran ba?"
Na ce." Kudi ya bata ta sayo musu anti Yagana mu zube lamarin nan a fefe mu kuma aunashi da ma'auni na hankali da adalci shin me kuka fahimta don Allah?"
Ya Falmata ta yi shiru domin bata san bada'kalar da ta faru ba fadi take yi aikuwa kaya dai sun yi kyau Amina ina ganin ko ke ce abinda za ki sayo kenan domin dai babu abinda babu kuma kowacece wannan ba ta yi cuta da almundahana ba
Anti Yagana ta ce." Ba ki gane ba ne, ita wadda ya bawa kudin kayan k'anwar wannan matar tasa ce fa Maryam da ta rasu mahaifiyar yaron nan Adamu da suka kawo kayan tare da Yusi."
Na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba
Ta d'an yi shiru na wani lokaci sai ta ce." Ba ta da aure ne?''
Ta gyad'a kanta tana fad'in." Bazawara ce tana zaune gidan yayarta tana business da kuma kula da yaran.
Shi babban ma Salim baya gari ita kuma Nusaiba tun iyayansu na raye suka yi mata aure sai shi wannan karamin Adamu."
Na ce." Yana ta jaddada mini cewa business d'in da take yi kenan kuma da a sayi kaya a waje gwara a saya a wurinta.
Ke anti Yagana kin san wuya da masifar da muka shiga dalilin Maryam ko, me kike tunanin zai faru yanzu tunda shi ba shi da tunani bai gane cewa sonsa take yi ba."
Ta dinga girgiza kanta tana fad'in." Lallai mutumin nan to ina ruwansa da ita idan ba yana so ya d'auka ba shi yanzu don girman Allah sai ya yi zawarcinta duk matan da suke duniya."
Ya Falmata ta yi shiru fuskarta ta canza da wani yanayi ta ce." Wata'kila wannan kyautar da ya yi miki yana so ne ya kashe miki baki kin ga ai idan ya yun'kuro domin auranta baki da bakin magana to mutumin da aka bawa kamfani na miliyoyin kud'i.
Ai ya jefi tsuntsu da dutse biyu ne.
Zuru na yi ina kallonta Ya Falmata macace mai tsinkaye sosai ni ban ma ta'ba yin wannan tunanin ba, amma har yanzu zuciyata bata gama aminta da cewa zai iya yin zawarcin Nabila ba idan an yi duba da irin muguwar wahalar da muka ci domin dai ba shi kad'ai ya shiga tasku ba har da mu gabad'aya Allah ne ya sa da kwanansa a gaba.
Anti Yagana ta ce." Hakan za ta iya kasancewa ya yi da wannan niyyar ne, amma abin ya ba ni mamaki wallahi, wai me yasa wasu mazan ba su da tunani ne?"
Sahura ta furta." Sai ki tsananta da addu'a Amina ni kaina wallahi na tsorata wad'annan mutanan sai kace mayu ita ta yi ta gama ita kuma wannan zata kutso kanta ba wani abu ta hange ba sai dukiya ce sun zama annoba wallahi.
Anti Yagana ta dubi Ya Falmata da mataccen jiki ta shiga bata labarin irin abubuwan da suka faru baya kafin rasuwar Hajiya Maryam din.
Ta dube ni tana fad'in." Ki ajiye kayan kada ki yi wa yaranki amfani da su.
Ya bada wasu kudin kafin mu tafi mu sayo musu sannan ko ya ba ki takardun kamfanin nan kada ki kar'ba har sai ya gaya miki abinda yake tsakaninsa da ita irin wannan fa sai dai ki ji an d'aura tunda haka ya yi lokacin auran 'yar uwarta."
Shiru kawai na yi ban iya cewa komai ba. muka yini muna tattauna lamarin shima tun jiya da daddare da ya fita bai sake shigowa ba.
Sai bayan la'asar duk muna falo yaran suka sake shigowa a karo na biyu wannan karon har da Masa'udu kowanne kafad'arsa sa'be da dilar atamfa suka jibge dila biyar a gefe sai wasu manyan kwalaye hud'u da suka shigo da shi suka tattara kayan waje daya.
Suka fita jim kad'an Hauwa da inna Uwani har da yaran gabad'aya suka shigo a gidanta suka yini, alamu sun nuna itama Inna Uwanin bata jima da sauka ba kuma kai tsaye gidan yarta ta sauka.
Hakan kuwa ya bawa Hajja haushi domin a takaice ta amsa gaisuwarta yayin da ita kuma take ta washe baki da Hasan a hannunta tana yi mini sannu da barka da arziki ina amsawa tare da kallonsu daga ita har Hauwan nema suke yi su mayar da mutane shashasai
Jim kan da zamansu shima ya shigo ganinsa sanye da kayan shan iska irin wanda ya saba sanyawa idan yana gida
ya tabbatar mini da cewa bai fita ba gabad'aya amma bai shigo ba sai yanzu.
Ya zauna a ka shiga gaisawa nan na ji yana gayawa Hajja bacci ya yi tun safe shiyasa bai shigo da wuri ba.
Ya Falmata ta fara tashi ta shiga d'akina.
Da kamar minti goma anti Yagana ta bi bayanta Sahura da Yusura dama suna ciki ba su fito ba.
Sauran kuwa suna can sashen ba'ki tun safe da muka gaisa na ce su koma can su yi zamansu sai sun fi sakewa.
Ni ma ban yi dogon zama ba na tashi na bar musu yaran gabad'aya.
Ina daf da shiga d'akina mai sunan Mamana ta fito Hajiya Saratu kenan da yake d'akin Hauwa na da suka sauka ita da Hajja tunda asali d'akin da suke yada zango idan sun zo Khalil ne a ciki yanzu ta tsaya cikin raha tana fad'in." Uwargida kuma uwar biyu sau biyu." Dariya na yi na ce." Hajajju kenan ina yini." Ta amsa da kulawa tana fad'in." Na ce bari na fito nasan yanzu Falmata tana nan ta fara bada labari."
Ina dariya na furta." Yanzu kuwa ta shiga d'aki yau tun safe bata jin dadin jikinta zazza'bi ne amma ta sha magani da sauki."
Na fad'i mata hakane kawai domin ban san abinda zan ce mata ba bayan haka dalili tunda suka zo ake yin wannan zaman a yi hira a yi wasa da dariya amma tunda na gaya musu abinda yake faruwa jikinsu ya yi sanyi mussaman ita din.
Kishi ne da su haka Mamanmu take da wannan kishin da rashin son kishiya yanzu nan duk sai su damu.
Gashi dai ba ita za a yi wa ba jin labarin wahalar dana sha a baya ya sanyayyar mata da jiki gabad'aya ma kyautar da take ta murna an yi mini ta daina burgeta don tunaninta yana gaya mata danne mini kirji zai yi kawai sai dai mu ji d'aurin aure.
Na shiga d'akin na samesu suna sake tattaunar maganar Ya Falmata duk ta yi wani kicin-kicin da rai na ji tana fad'in zaman ya isheta yau kwana bakwai tunda yara sun amsa sunansu su yi shirin tafiya kawai.
Na zauna gefanta ina fad'in." Wane irin tafiya kuma Ya Falmata ku bari a k
rasa shagalin sunan mana.
Tsaki ta ja kafin ta ce." Mijinki haushi yake ba ni Amina wallahi sam shekarunsa ba su amfanar da shi komai ba gabad'aya ba shi da tunani da hangen nesa."
Dariya ce ta kama ni ganin yadda ta hak'ikance tana ta fad'a.
Na shiga wanka na fito na shirya jikina sosai d'aya daga cikin sabbin d'inkunan da na yi wanda Sahura ta zo mini da su.
Still dai maganar suke yi anti Yagana tana fad'in." Wata'kila ma ita ya bawa kudin raggon suna tunda yau da ake da kwana bakwai a al'ada ya kamata a ce an yankawa yara rago duk da ba a ce dole yin hakan farilla ba ne.