Sashe 225
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna nan birjik a gari wad'anda jima'in kawai suka sani duk dare babu fashi sai sun yi amma ba su san hanyar da za su kula da abinda jin dadinsu ya haifar musu ba domin kuwa jin dadin ai shi yake kawo albarkar 'ya'ya bayan an rabauta da shi.
Aka shiga gaishe-gaishe da tambayar bayan rabuwa.
Daga lokacin ne ya dan samu nutsuwar bud'e bakinsa da ya yi masa masifar nauyi kasantuwarsu da malamin a d'aki ya kasa duban wajan da yake zaune saboda tsabar jin nauyi da kunya tare da zullumin abinda zai biyo bayan uzurinsa.
Ya zurawa Malam Nuhu ido yana nuna Dr Iliyas cikin ko'karin jaddada jarumtarsa ya ce." Wannan sunanshi Dr Iliyas Musa k'wararran likita ne da ya karanci fannoni da dama yana aiki a babban asibitin nan kano wato Malam Aminu."
Malam D'aha ya sake mikawa Dr Iliyas hannu suka yi musabaha a karo na biyu bayan wadda suka yi da farko a lokacin da suka same shi shi kadai a zauren nasa.
Malam Nuhu Shima ya mik'a masa hannu baya suka sake yin musabaha cikin dai karamaci da kulawa.
Wajan ya d'auki shiru na d'an wani lokaci.
Kafin ya yi gyaran murya ya cigaba da cewa." Wato Malam Nuhu na ji dadin zuwanka a yanzu saboda wani babban uzuri wanda ya assasa mini rashin nutsuwa da kwanciyar hankali da tunanin yadda zan tunkari Malam da wannan uzurin da duka ya shafe mu gabad'aya."
Shiru ya sake ratsa wajan a karo na biyu babu wanda ya tanka Malam Nuhu dai kacokan ya mayar da hankalinsa gare shi yana sauraransa.
Ya nisa kafin ya sake tattago jarumtar da neman rinjaye dangane da abinda yake faruwa ya cigaba da cewa." Wani abu ne da ya zama ruwan dare ko kuma na ce babban kalubale da rikicewar tunani ga ma'aurata wad'anda Allah Ya jarabta da hakan.
Kasancewarku mutanan karkara nasan dai da wahala a ce wasu da suke rayuwa a wannan garin ba su gazgata cewa rigafi ya fi magani ba.
Kuma hausawa suna cewa taya Allah kiwo ya fi Allah na nan."
Malam Nuhu ya ce." Yallabai ya kamata ka yi magana kai tsaye domin wallahi gabad'aya ka sanya ni cikin nazari da zullumi." Ya dubi malamin yana fad'in." Ko ba haka ba ne Malam?"
Malam D'aha ya gyad'a kansa cikin nutsuwa ya furta."Tun zamansu a wannan wurin na fahimci da akwai abinda yake tafe da su domin dai tunda aka fara hidimar nan Alhaji Tajo bai ta'ba bugo mini sammako irin yau ba sai kwanaki biyu da suka wuce da ya zo da kansa ya d'auki Hajara ya ce da ni za su je asibiti a zaman da nake yi a yanzu ina sauraran ji daga gare shi ne ko Hajara tana d'auke da wani ciwo wanda mu ba mu san da shi ba sai yanzu."
Malam Nuhu ya ce." Ya Malam Hajara kalau take domin tunda aka haifeta a gidan nan bata ta'ba kwanciya wani mummunan ciwon da zai gigita mu ba.
Kusan a yanzu ma duk ta fi yaran gidan kuzari da hankali."
Ya gyada kansa amma bai ce komai ba.
Suka dai zuba masa cikin yanayi na damuwa gabad'ayansu domin ga yanayin yadda ya fara yi musu magana sun san lallai akwai matsalar da take shirin faruwa.
Ya sauke ajiyar zuciya kafin ya cire shakku da jin nauyin malamin ya dubu idonsa sosai ya ce ." Malam a gafarce ni idan har na yi lefi ina neman afuwa.
Ban zo nan na d'auki Hajara na kaita asibiti domin a yi mata wani gwaji na mummunan ciwo ba face samun nutsuwa da ita domin ingantuwar auranmu da kuma samun yara masu albarka da wadatar lafiya."
Na kudi ne littafin nan kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Ya gyada kansa yana fad'in." Babu cutuwa ko cin zarafi tsakanina da zuri'ar Alhaji Ibrahimu kai din daidai kake da wannan da yake zaune a gefanka." Ya nuna Malam Nuhu.
A daidai lokacin Malam Rabi'u ya shigo da daurikan goro kusan bakwai ya jibge a gefe d'aya.
Yazo ya zauna a ka gaisa da shi yanayin da ya gan su a cikin na alhini da zullumi ya sanya ya fara tambayar d'an uwansa lafiya.
Malam Nuhu ya furta." Lafiya ba lafiya amma dai mu saurare daga Alhaji Tajuden."
Duka suka zuba masa ido sai ya cigaba da cewa." Ina godiya Allah Ya gafarta Malam wannan da yake zaune da na gabatar muku da shi shine likitan da ya yi mana gwajin jini da yarinyar nan Hajara cikin kwarewa da irin hikimar da Allah ya huwace musu ya tabbatar mini da cewa akwai matsala domin kuwa jini na dana yarinyar nan bai yi daidai da yadda ake buk'ata ba.
A irin hasashen da suke yi da kuma yadda muke gani a kan wasu da Allah Ya jarraba da samun yara masu d'auke da wannan cutar mai kisa farar d'aya ya sanya shi din ya ba mu shawara a matsayinsa na jami'in lafiya dakatar da abinda ake shirin yi a yanzu dalili anan kuwa shine za mu kasance ni da yarinyar nan cikin yanayi na damuwa da tashin hankali a duk lokacin da Ubangiji Allah Ya ba mu rabo na haihuwa yaranmu za su zo d'auke da wannan lalura ta sikila wadda take kisa a take ta kuma wahalar tare da jirkita hallita da matsancin ciwo mabambamta idan kwana bai k'are ba."
Shiru kamar an yi ruwa an d'auke babu wanda ya ce uffan amma gabad'aya jikinsu ya yi sanyi ban da malamin da wani murmushi ne ma na mussaman a saman le'bansa.
Dr Iliyas ya yi kundubala ya dubi malamin da wasu takardu guda biyu a hannunsa yana bud'a su ya ce." Ya Malam a matsayin mu na likitoci muna yin iyakacin bakin kokarinmu akan kowace irin ma'asala domin mu dora jama'a akan hanyar da za su samu mafita da kuma wadatar lafiya.
Babu nufin yi wa Allah shishsigi domin shi Ubangiji shine ya d'an sammana sani daga cikin abinda mu ba mu sani ba sanin abinda yake kudira sai shi buwayi gagara misali."
Malam D'aha ya zuba masa idoo yana sauraransa.
Ya cigaba da cewa."Yawaitar wannan ciwo da yadda masu d'auke dashi ke shiga gagari da k'unci na rayuwa da azaba mai tsanani a duk lokacin da ya motsa ya sanya kungiyar manyan likitoci daga 'kasashe daban-daban mahukunta da kuma gwamanti had'a karfi da k'arfe domin yin bincike akan dakile hanyar da wannan lalurar za ta cigaba da yaiwata a kowane sassa na fad'in duniyar nan gabad'aya.
Binciken da k'wararru suka yi tare da taimakon Allah Ya sanya suka gane cewa mataki na farko da za a d'auka domin dakushe yad'uwa da haihuwar yara masu d'auke da wannan lalura yin gwaji na jini domin sanin matsayin namiji da mace a duk lokacin da za a k'ulla auratayya wanda muke kiransa da (genotype) Ta wannan hanyar ne kawai za mu duba mu ga cancanta da dacewa wad'anda suke so kulla aure domin yin rayuwata ta din-din tare da samar da yara masu ingantaciyar lafiya.
Daga lokacin da muka fahimci cewa As da As na da mutukar had'ari a matakin jini ko Ss da Ss Muna yin iyakacin bakin kokarinmu wajan ganin mun hana su kulla aura ba don komai ba sai don gujewa 'kin juna da tsanar junansu da za su yi a nan gaba dalili kuwa anan shine suna fara haihuwa za su ci karo da jinyya mai tsanani daga albarkar da suka samu.
Iyaye na kasance tamkar majinyyata marasa nutsuwa da fargaba a duk lokacin suka dubi abinda suka haifa a kwance cikin mawuyancin hali na ciwon ga'bobi da kumburi da 'konewar jini zafin jiki da koke-koke Mu likitoci muna yin misali da ciwon nakud'a irin na mata ga yaro ko yarinyar da suka tsinci kansu a cikin wannan yanayin.
Nakud'a idan Allah Ya sau'kakawa mace cikin dan k'aramin lokaci zata haife abinda yake cikinta sa'banin mai d'auke da wannan ciwon a duk lokacin da ya motsa masa yana ficewa ne daga hayyaci tare da jefe zukatan iyaye rayuwar ce ko mutuwa.
Ya nisa cikin sauke ajiyar zuciya ya cigaba da cewa." Ita wannan cutar ana gadonta daga iyaye biyu wato uwa da uba kamar yadda na yi muku misali da farko idan ya kasance an samu rashin daidaituwar jini uba ya kasance As uwa ma ta kasance As to akwai yiwuwar su samar da yara masu dauke da cutar kuma mafiakasari yaran da za su haifa duka za su rinjayi masu lafiyar yawa.
Akwai misalin Ss da Ss shima kamar As din ne akwai buk'atar ha'kuri da juna tare da neman mafita daga kowane bangare domin gujewa samar da abinda zai zama damuwa da zubar hawaye a gaba.
Kamar yadda Yallabai ya yi bayani da farko kafin ba ni damar magana ni likita ne massanin fannika da dama da suke da ala'ka kowace lalura kuma ina yin iyakacin bakin kokarina wajan ganin na bayar da shawara akan abubuwan da su kawo rud'ani da cutar da wani bangare.
Shin yaya ake gane cewa an haifi yaro da wannan cutar dalili anan shine yaro yana karami ba shi da bakin da zai fad'i cewa ga wajan da yake masa ciwo sai dai kuka da kumburin jiki kafafu da cikinsa da kuma jirkitar launin idanu daga fari zuwa ruwan dorawa (yellow) alamu na farko kenan sai yanayin suffa da rashin kuzari ta wani gefan tafiyarsu ma tana bambamta da irin ta masu cikakkiyar lafiya.