← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 276

Sashe 96

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina ruwanka da bibiyar abinda ya shafe ni.

Gwaggwo dai mahaifiyar mijina ce wanda mutuwa ta yi mana kutse ta shiga tsakani, na tabbata kuwa a duniyar nan ba zan sake katari da namiji mai nagartarsa ba.

Kana ta bina da sharri, ka yi nan ka 'bata ni, ka bi nan ka 'bata ni, to ta Allah ba taka ba, ka ja tsumman rayuwarka, ba ma buk'atar ko kwabonka, ba na son munafurci ni."
Cikin nutsuwa kamar bai ji zafin maganganuna ba ya ce.'' Ai na mayar dake dama na yi ne domin ya zama gargadi a gare ki.

Kuma ba don ke nake tsaye akan abinda ya shafeki ba, saboda wasu dalilai ne, ke ki ka haifi Yusuf amma ya fi ki hankali, kuma saboda shi din na shiga lamarin, ai na san kakarsa ce ko ba itace ta haifi Aminu Salihi ba."
Cikin takaici da b'akinciki na furta." Ban mayu ba, wallahi ban mayu ba na saku har abada ni dakai dama can ba a son raina aka yi ba, ba zaka tozartani ba wallahi ko maza sun kare a duniya ba zan zauna da kai ba, kuma ko mutuwa Gwaggwo ta yi menene abinda ya dame ka, babu ruwanka ba na son munafurci fa." Na sake maimaita kalmar munafurci domin na tunzurashi.

Bai tunzuru ba a tsanake ya ce." Sai ki yi kuma ni dai na mayar dake shekaran jiya na yi sakin jiya da safe kuma na kudire a raina na mayar dake yanzu kuma na sanar miki, don haka har yanzu kina karkashin ikona."
Da sauri ya yanke wayar kamar ya san abinda yake bakina mai muni ne tabbas da bai kashe wayarsa ba sai dai ya ji ruwan ashar a kunnansa saboda yadda zuciyata take a tunzure.

Na kasa motsi daga inda nake gumi na yanko mini tsabar tashin hankali kamar yadda ya fad'a a musulunce na mayu tunda ko jini daya ban yi ba kuma ka'idar musulunci jini uku ne na fita daga idda.

Hawaye masu zafi suka fara karakaina a kumatuna.

Anti Yagana ta shigo d'akin da karsashinta ganin yanayin da nake ciki ya sanya ta d'an yi sanyi ta tsaya tana fuskantata..."Menene kuma?" Tambayar da ta yi mini kenan.

Cikin k'unci da takaici na ce." Anti Yagana a wannan karon dole ki yi hakuri na d'auki mataki da kaina domin siyarwa kaina mutunci.

Yadda na lura da mutumin nan bashi da mutunci ko kad'an kuma yana yi wa mata kallon wulakantattu idan ba haka ba me zai sanya ka saki mace haka kawai babu hujja mai karfi saboda kawai jin dadi gobe kuma ka ce ka mayar da ita addinin bai ce haka ba Anti Yagana ki zauna ke kanki ki dubi lamarin nan a tsanake kada soyayyar da kike masa ta sanya ki danne lefinsa ba fa daidai ba ne abinda ya aikata mini."
Jiki a mace ta ce." Na sani wallahi Amina, kuma bayan ke wallahi tallahi babu wanda ya kai ni jin ciwon sakin da ya yi miki, ni yadda na fahimta kamar bashi da ilimin addini mai zurfi boko ce kawai take dawainiya dashi shiyasa yake ganin kamar abinda ya aikata ba wani lefi ba ne.

Abu na gaba kuma kin san shi, abinda ba na sha'awar ya kasance da ni a rayuwata wallahi kema ba na sha'awar ya faru dake, ba na yi miki sha'awar zawarci da lissafin aure don ma Allah Ya takaita gidan alhji Muntari ba ki haihu ba, wannan dalilin ya sanya nake ta dannarki ki yi hakuri ki zauna kowace mace tana da kalubale."
Na ce." Anti Yagana kada ki ce na ki jin maganarki wallahi na fahimci abinda kike gudu, amma dai don girman Allah wannan karon ki kyale ni da mutumin nan kada ki shiga ciki ki ja bakinki ki yi shiru kawai ki zuba mini ido."
"To wane shiri za ki yi akansa kin san dai shi namiji ne ke kuma mace tunda kuma ya ce ya mayar dake bafa yadda za ki yi dole ha'kuri ne naki."
Na sani anti Yagana ba shirin da zan yi akansa amma ba zan koma ba kamar yadda yake tsammani wallahi sai ya tako kafarsa garin nan."
Ta gyada kanta tan
d'an murmushi ta ce." Abu ne me sau'ki ai tunda yana sonki za ki gan shi kuwa.

Ban ce mata komai ba har ta kama hanya ta fice daga dakin.

Tun cikin dare na kammala shirye shirye na don haka gari yana wayewa na fito a kintse da zummar d'aukar hanya tunda d'akin da nake yana da bandaki ban fito ba sai da na shirya tsaf tukkuna.

Gabad'aya suna falon ana shirin karyawa hadda maigidan a zaune bai fita ba dama ba kasafai yake fita da wuri ba idan juma'a ce.

Fitowata ta d'auki hankalinsu gabad'aya na gyara yanayina don ba na so ta dakatar da ni daga kudirin da na yi.

A tsanake na ce." Anti Yagana na shirya fa zan tafi kamar yadda muka yi magana jiya wallahi da Gwaggwo na kwana a cikin raina."
Tana kallona ta ce." To kin gayawa mijin naki ko dai ?"
Eh kawai na ce mata a takaice.

Yadda ta zuba mini ido shi ya tabbatar mini da cewa ba ta yarda da amsar dana bata bata
Yusi yana gefe a zaune ya yi nairainarai da ido saura kiris ya fashe da kuka dan tun jiyan nan dana mare shi bai zo wajan da nake ba.

Kallo d'aya na yi masa na kawar da kaina daga kansa domin Ina so na horar dashi akan abinda ya aikata ko don gaba ya kiyaye furta abinda ba shikkenan ba.

Cikin sigar zolaya Babansu Fadila ya ce." Madam ba gaisuwa ne ko na yi wani lefin ne kuma."
Cike da jin nauyi na ce." Yi hakuri wallahi na d'auka dana fito na gaisheka, gabad'aya hankalina ne baya jikina."
Ya ce." Amma dai kya bari ki karya tukkuna sai ki tafi, da za ki bari ma akwai motar da zata tashi karfe goma sha daya na safe sai na kira direban yanzu."
Na ce." Anya kuwa zan bari ai ka barshi kawai zan iya shatar motar ma gabad'aya babu damuwa.

Cikin dai zolayar dai da ya saba da sigar wasa ya ce." Au na manta Hajiya ce fa uwargidan a wurin Yallabai."
Murmushi kawai na yi na dubu anti Yagana tana tambayata yaushe zan dawo.'
Na ce." Nan da sati guda in sha Allahu zan dai kira ki idan zan taho din."
Ba ta ce komai ba ta fara tsiyaya kunun gyadar cikin wani madaidaicin fulas tana fad'in." Ki tafi dashi ko a mota sai ki kurba kina dai sauka ki kira ni."
Na ce." To shikkenan in sha Allahu......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.

Normal What'sapp group kuma na #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*62*
Ganin halin da ya shiga ya sanya mini muguwar fargaba domin kuwa tunda nake dashi ban ta'ba ganinshi a cikin yanayi na rud'u da tashin hankali ba.

Tabbas lokacin rasuwar baby Nana ya shiga damuwa sosai amma sai nake ganin wannan lamarin ya fi d'imauta shi fiye da wancan din.

Jikina babu kuzari ko na gamin gafara na kama hanya domin fita daga d'akin saboda ban san wacesa irin fitina zamana zai haifar ba.

Fargabata da tsananin damuwata kada ya fitar da maganar domin kuwa ya fi ni gaskiya da hujja mai karfi dalili ni tun farko na d'auri kaina da ban gaya masa ina da ciki ba.

Idan kuwa zan kafa hujja da cewar ai na zubar da shine domin gudun haihuwar mai sikila ba kowa ne zai fahimce ni ba, da yawa ma wasu za su ga ai don ina da yaran ne ya sanya ni yun'kurin zubar da ciki ba tare da damuwata ba.

Amma fa muddin an zauna an dubi lamarin ta fuskar adalci za a fahimci abinda nake nufi.

Wannan kadai itace hujjata ko da kuwa maganar ta fasu na tabbatar da cewa ya fi ni hujja mai karfi domin masu k'adaita Allah da tauhidi ai za su ga gangancina domin kuwa tun fil'azal ai haka iyaye da kakanni suke yin auransu su haihu lafiya ba tare da wata rikitarwa irin ta yahudu da nasara ba.

Kai tsaye d'akina na wuce na kwanta don ba zan iya zaman falon ba dalili kwata-kwata bana cikin hayyacina ga jikina babu k'wari don har yanzu jirin bai gama sakina ba.

Anti Yagana ta shigo d'akin ta same ni a kudindine a cikin bargo lokacin ma kuka nake yi amma mara sauti sai na yi saurin rintse idona ina goge hawaye a fakaice bata fahimci komai ba tunda daga bakin kofa ta tsaya tana tambayata ko jikin ne na ce mata a a Ina hutawa ne sai ta juya ta zata fita tana fad'in bari ta kawo mini abinci na ci sai nasha magungu
Da kyar na iya cin loma biyar shi ma sai da ta matsanta mini tukkuna na ci sai da ta tabbatar da nasha maganin kan ka'ida tukkuna ta fita daga d'akin.

Sai bayan ishi'i su Hajja suka tafi bayan sun shigo sun yi mini sallama tare da fad'a mini cewa za su sake dawowa domin sake duba ni cikin satin da za mu shiga.

Ina daga kwance muka yi sallama cikin kulawa yadda suka nuna damuwarsu a kaina hakan ya faranta mini sosai sai dai can kasan zuciyata ina jin fargaba kad'an idan har suka samu labarin abinda na yi shin da wace fuska za su dube ni.

Tunda na fito daga dakinsa ba mu sake haduwa ba sai da garin Allah ya waye anti Yagana ta matsa mini lallai sai na rage kwanciya na fito falo na zauna kan kujera hakan zai k'arfafa mini gwiwa domin idan ina yawan kwanciya kasala da ciwon jiki ba za su barni ba.
Chapter 96 · 0% Book details