Sashe 258
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babu jin kunya ta dinga yi mini godiya daga lokacin na sake tabbatar da cewa muguwar kwad'ayayyice mai son abinda duniya Allah ne ka'dai yasan abinda Hauwa ta had'a mata domin tafiya dashi wanda kuma nake da tabbacin cewa shi kansa maigidan ya yi mata sallama mai kyau Allah Ya kyauta ya rufa asiri yanzu zamani ya lalace tundaga lokacin dana ganta a shekarun baya tana yi masa yarfen magani a kafar bane na tabbatar da cewa bata da hali kuma bata tsoron Allah kuma za ta iya aikata komai a kan biyan buk'atarsu tunda ai ba zata za'be shi ba ta ajiye 'yarta ba duk wannan jidali da koke-koken da take yi akan abin duniya ne tana taya 'yarta kishi tana kuma yi wa 'yar uwarta ciki daya zagon 'kasa a yanzu idan ya fadi ya mutu
Na kudi ne littafin kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.
damuwarta kad'an ce tunda ba ita ta haife shi ba mahaifiyarsa da yaransa sune suka yi rashi.
Bala'in damuwar da suka shiga a lokacin da cikin nan ya zube ba zai misaltu ba domin an same shi ne da k'yar ni ma na gazgata maganarta bai fiye kwanciyar aure da ita ba domin da yana yi da ita ka'in da na'in zan samu sasaauci ta wannan fanni amma Allah ne da kullum duk ranar girkina sai ya neme ni idan har ba mu yi sunna ba to akwai dalili mai karfi wanda ya assasa rashin faruwar hakan koyaushe cikin doki da sambatuna yake ya sha fad'in shi kullum tamkar sabuwar budurwa nake a wurinsa abin ya yi ta ba ni mamaki haihuwa biyar ciki har da biyu sau biyu tun ina d'aukar maganarsa da dad'i ne na shau'ki har na gazgata domin da dukkanin gaskiyarsa yake fad'in hakan.
To wannan shine dalilin da ya sanya su shiga tashin hankali a lokacin da cikin ya lalace har suna neman rabuwa saboda ganin kada a yi biyu babu yanzu kuwa na tabbatar da cewa ko da bata samu kula ta fannin auratayya daga wajansa ba to za ta cigaba da hakuri tunda ta fara samun abinda take buk'ata.
Hadiza wata uku a gidana ta murmure haskenta ya dawo ta yi ki'ba jikinta ya fara cikewa domin dawowar masu aikin gidan na hana ta yin wata wahala mai yawa sai dai duk da haka takan yi mini d'awainiya da yaran amma ba sosai take shiga kicin ba.
Hakan ya yi mini dadi sosai domin ta fara sakewa na saya mata sabuwar waya domin ta kara d'eba mata kewa da mantar da ita irin wahalar da tasha a baya wajan zamanta a gidan kurkuku idan tana ba ni labari irin wahalar da ake sha ni kuka ita kuka daga karshe ma na ce ta daina gaya mini domin yadda ta ba ni labarin wani ma'aikaci da ya dinga farautarta a lokacin da bai samu hadin kanta ba kullum sai ya sanyatawa kwashe busashen kashin band'akunan gidan da hannu kuma ba zai bata sabulu ta wanke hannunta ba haka idan an kawo musu abinci za ta ci bayan ta wanke da ruwa kacal tana gaya mini hannunta har sai da ya kame da d'oyin kashi.
A d'akinsu kuwa mutum biyar sai da suka mutu saboda wahala tasha kwana da gawa a d'aki daya.
Tun daga lokacin na ce ba ni son labarin saboda shiga tashin hankali nake yi na ce ta dage da addu'a tare da neman afuwar Ubangiji tsautsayi da mugun ji da gani asara tare da danasani Ubangiji Allah Ya kare mu.
Ranar wata lahadi ya kasance girkina ne maigidan bai tashi a bacci da wuri ba sai bayan sha biyu na rana yana tashi kuwa ya ce mini towo zan yi masa kuma da hannuna miyar zogale.
Aka duba kicin kaf babu zogale dole sai an shiga kasuwa Masa'udu ya je gida ganin iyalinsa tun sallah bai dawo ba shi kad'ai ne ya yi wannan nisan zaman domin ko su Taburni da Mairo satinsu hud'u suka dawo bakin aiki bayan sun je sun gaisa da iyalinsu tare da yi musu alheri daga cikin alherin wanda yake ri'ke da su.
Mairo da Hadiza sune suka shirya shiga kasuwa sayo zogale dalili Taburni da Baba Tabawa na aikin abincin rana.
Suka shirya suka tafi Sukairaju ya kai su na hada musu da sautin tsamiya domin ya dingi shan kunun tsamiya ko bayan wucewar Ramadan sai ya ce a dama masa kuma ba dare ba rana duk lokacin da buk'atar son shan kunun ya bijiro masa wadda muke da ita tana daf da k'arewa da zo'bo tunda ana yi masa baya shan lemo mai gas.
Ba su yi awa d'aya ba kuwa suka dawo da komai da komai har da daddawa duk da ban buk'ace ta ba dalili ina da ita da yawa kuma mai mugun kyau wadda Hajja ta sanya aka yi mini ita mussaman lokacin haihuwar su Hassan da Magaji ya zo ya kawo mini kwalli da garafuni ya had'o mini da ita manya mai dadi a miya.
Na ce ita din ma da suka sayo ba za ta'ki ba za ta yi amfani.
Tsaf na shirya masa towon shinkafa da miyar zogalen kamar yadda ya buk'ata na yi amfani da zallar tsoka na k'aramar dabba wurin had'a miyar da ta ji gyad'a da manja ta yi kyau sosai tana ta tashin k'amshi.
Cikin santi ya ci towon nan wurin malmala biyu kad'an ne bai cinye ba ina ta yi masa dariya ganin yadda yake sud'e hannu ina fad'in idan baka koshi ba sai a sa wani bai ce mini komai ba ya sud'e yatsun hannunsa tas ya shiga toilet domin yin burush
Bayan kwana biyu ya je gidan Hauwa ya yi kwanakinsa ya dawo yake gaya mini wata magana.
Jikina ya yi sanyi sosai na zuba masa ido a hankali na ce." Hadiza fa ka ce, bai duba shekarunta ba kwanaki biyar kawai ta ba ni shekara arba'in da biyar muke ni da ita ba budurwa ba ce.''
A nutse ya furta." Akwai haramci ne cikin abinda Annabi Muhammadu S.a.w ya yi.
Kada ki yi mana sa'bo hajiya shima Sukairajun ai ba saurayi ba ne ya ta'ba aure."
Na zuba masa ido sosai da mamakin jin maganarsa.
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Ya ta'ba aure shekarun baya a can mahaifarsa mutumin Zamfara ne kin ta'ba neman labarinsa a wajena?"
Na girgiza kaina a hankali ina cigaba da kallonsa sai ya cigaba da ce wa.'' Ya zo nan kano cirani muka hadu da shi a titin Yahya gusau watarana tun kafin na yi shura a duniya yana sayar da fetur da kanikanci ya gyara mini mota a lokacin da lalace daga lokacin ya zama wanda nake bawa gyaran mota a duk lokacin da ta samu matsala muka yi sabo sosai har dai ya zama direbana kafin Ade da D'ahuru Sukairaju yaro ne mai Amana da nutsuwa da kuma girmama mutane ya gaya mini ya yi aure amma matar ta rasu wurin Haihuwa sasha zuwa garinsu wurin mahaifiyarsa kafin ta rasu.
A duk lokacin da ki ka gan ni tare da Ade to Sukairaju ya je ganin gida tunda duk 'yan uwansa suna can garin.
Kuma ba na tsammanin Hadiza za ta girma shi sai dai su yi daidai a shekaru to menene aibu shine ya gaya mini da zata amince sai ya aureta shi yana sonta duk da na gaya masa abubuwan da suka faru a baya ya amince da hakan, don haka ina nema masa auranta a wajenki tunda kece uwar dakinta idan kin ce a yi za a yi."
Na yi kasa'ke ina kallonsa kafin na ce." Allah sarki wallahi ni kam ba ni da jayayya ko na kawo tasgaro muddin Hadiza ta amince zan fi son haka tunda har ka yabi kyawawan halayensa kuma ni ma na sheda hakan idan tana sonsa sai mu sha biki."
Ya yi dariya yana kallona kafin ya ce." To ta wace hanyar ki ke ganin za a sanar da ita halin da ake ciki, kin ga ni yayata ce da kunya na tunkareta ko."
Na d'an harare shi ina fad'in." Yayarka fa ka ce." Ya gyad'a kansa yana fad'in." K'warai kuwa ko da yini guda ta girme ki ai sunanta Yaya Hadiza a wajena."
Na yi kasa da kaina ina murmushi na ce." Shikkenan to ni zan gaya mata in sha Allahu rabbi za ta amince."
Ya furta." Da na fi kowa farinciki kuwa, ni kuma na yi alkawari zan yi iyakacin bakin kokarina.'"
Na gyada kaina ina fad'in." Ubangiji Allah Ya tabbatar da alheri." Ya kama hannuna yana cewa." Amin Ya Allah."
Ai a daran na same ta da maganar ta dinga dibi-dibi da 'kyar ta bud'e baki jikinta a mace babu wani karsashi da sukuni a tattare da ita ta kalle ni sai na hangi k'walla mai yawa cikin kwarmin idonta ta ce.............
In sha Allahu da ni daku mu sanya rai saura 8 chapter littafin nan ya kammala Allah Ya taimake ni ya kuma yi riko da hannuna dan isar Annabi.
Ina miko godiya kwarai da fatan kowa ya sha ruwa lafiya.
Ubangiji Allah Ya kar'bi ibadarmu ya 'yantar damu.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...
BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*170*
Shiru na yi ina sauraranta a yayin da take gaya mini abinda yake damunta har tana zubar da hawaye na damuwa da kunci tare kuma da fargaba.
Jikina ya yi sanyi sosai domin dai na riga na gama fahimtar manufarta ba wai auran ne abin gudu a wajenta ba abinda zai haifar bayan yin sa shine take ji wa tsoro da zullumi.
To ai babu wata cuta da Ubangiji bai yi maganinta ba duk da infection wani irin ciwo ne da yake saurin dakusar da mu'amula da auratayyar da aka gina cikin tsananin so da sha'kuwa.
Bayan rashin ha'kuri daga b'angaran ma'aurata abu na biyu da yake saurin kassara aure da lalatashi shine infection mussaman idan an yi katari da cewa macace taje da shi ta shafawa namiji abin sai ya yi muni da tsanani aure ya gurgu'de ba tare da yaje ko'ina ba.