← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 248 OF 276

Sashe 248

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin ban yi magana ba ya sanya ya ja goron numfashi kafin ya furta." Ni yanzu karfina duk ya 'kare kun karar mini da shi bana ji jin zan iya ajiye mata uku a yanzu kuma kowacce tana jira na kwanta da ita ni na fara gajiya wallahi."
Duk yadda na kai ga dannewa sai dariya ta subce mini na ce." Haba kaine fa na ji kana fad'in babu abinda ya fi wannan sabga dadi a duniya kuma sai kace ka gaji."
Ya furta." Da gaske na gaji Amina duk da sunna ce mai kyau ai duk fafutukar da na dinga yi a baya wallahi ina son haihuwa ne, Ubangiji Allah Ya ba ni sai godiya yanzu ma ban ce ba ni so ba ina neman kari ina nufin abinda aka yi a baya yanzu ba za a yi ba."
Na girgiza kaina ina kallonsa kafin na ce." To sai ka ce mata me?"
"Na ce sai na yi shawara tukkuna."
Na yi 'kasa da kaina ban sake cewa masa komai ba saboda takaici wace shawara kuma ya fito fili ya gaya musu gaskiya daga ita Nabilan har wadda ta yi kamun k'afa da ita tunda babu buk'atar aurenta a ransa babu amfanin yi mata yawo da hankali.

A daran dai wani lamari ne ya kasance a tsakani na dashi mai armashi da wahalar mantawa.

Soyayya bata tsufa muddin za mu had'u muka zama tamkar sabbin ma'aurata ah to me za a fasa tunda da rai da lafiyar da kuma sauran kuruciyar shima duk fadi yake yi ai yana shiga hannu ya fara makyarkyata tamkar wa
ni d'an magyaru!

GARKUWAR MATA ta gama gigita lissafin attajiri sai ya dawo ustaz a daran yabo da kalaman soyayya a cikin harshen labarci ya dinga zuba a yayin da jikinsa yake tsananin neman abinda duniyar ta ginu a kai.

Allah Ya sa mu dace Amin.

Kwana biyu haka muka dinga gwangwajewa Muna shan soyayya a kuma wannan lokacin ne dana samu dama na gaya masa bukatata kan kyautar da ya yi mini da farko ya ce a a bai ba ni don na sayar ba yanzu haka ana ko'karin sabunta takardun wajan da sunana don haka babu niyyar sayar da shi a tsarinsa.

Na yi ta ko'karin ganin na ganar da shi nufina ya ki ya ce idan ba ni so kawai na gaya masa ba zai yi mini kyauta ba kuma na canza masa tsari ba ana cigaba da gudanar da abinda ake yi a kamfanin duk abinda ya kama na shiga da fita mallakina ne.

Ganin bai amince ba sai na kyale shi.

Da yaje ya yi kwana biyu a gidan Hauwa ya dawo na ce masa ina so ya ba ni rancen kudi tunda dama wanda na samu na wurin larabawan nan suna hannunsa bai sa mini cikin acct dina ba.

Babu wata fargaba ya tambaye ni abinda zan yi da kudi kuma nawa nake buk'ata.

Na ce miliyan hamsin.

Ya jima yana kallona kafin ya furta." Me za ki yi da su?" Da mamaki sosai a tare da shi ya yi mini tambayar."
Na ce." Kasuwancina zan kawo nan garin zan kama shaguna cikin wuse market na zuba kaya tunda yanzu raba 'kafa ake yi."
Ya ce." Yaushe za ki biya ni?"
Na ce." Mu yi a rubuce shekara uku ko hud'u, in sha Allahu rabbi zan biya ka kudinka."
Ya gyad'a kansa yana kallona kafin ya furta." Ki ce kawai na baki kudi Hajiya kai tsaye amma ai kin san babu rance a tsakaninmu ko?"
Na gyad'a kaina ina fad'in." Da akwai mana idan da yarda da amana ko kana ganin ba zan iya biyanka ba?"
Girgiza kansa ya yi kafin ya ce." Za ki iya tunda me nema ce ke amma ki bari zan yi shawara akan hakan.

Zan kuma sanya miki kudinki da suke hannuna."
Na 'bata rai tare da cewa." Tunda sai ka yi shawara za ka ba ni me yasa ba za ka amince da shawarata ta farko ba abin nan ni ka ce ka bawa to me yasa ba za ka bari na yi iko da shi ba ashe kyautar ba har zuciyarka ka yi mini ba tunda ka hana ni na yi iko da shi."
Ya furta.'' Ai ni ban baki don ki sayar ba, kin ga kuwa babu wani dalili da zai sanya ki ce mini na ba ki umarnin sayarwa, amma dai yanzu tunda na ji hanzarinki ki bari na yi tunani tukkun ko an gaya mini haka ake tafiya kai tsaye komai yana buk'atar nazari da tunani."
Shiru na yi ban sake yi masa wata magana ba, muka cigaba da tafiya a haka shima bai sake tashin maganar ba ya kuma sanya mini kudina da suke hannunsa kamar yadda ya fad'a.

Ranar wata lahadi da sassafe na hau saman na same shi da yake a d'akina nake kwana wataran ya biyo ni mu kwana tare ranar da yake da ayyuka kuma ko ya biyo ni yana fita idan muka kammala uzurinmu.

Na same shi suna bidiyo call da Kamalu shigowata d'akin na ji yana fad'in." To ga tanan ma ta shigo Amina zo ga Ustaz sunan da yake kiransa da shi kenan tun lokacin da ya dawo daga makarantar horon da muka kai shi ni da Hamusu.

Na zauna cike da wani irin farinciki.

Tunda ya tafi ba mu gaisa ba kusan wata uku da wani abu bana jin ma sun yi magana da Hajja don da sun yi din za ta gaya mini......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*164*
Mama ya kuke ina fatan duk kuna nan lafiya."Na kasa 'boye murnar ganinsa cikin suttura da nutsuwa tare da wata iriyar kamala ta mussaman na amsa idona a kansa.

Lallai Ubangiji shine isashshe idan har mumini ya yarda da kaddara da jarabta ya kuma kar'bi abinda Allah ya wanzar a rayuwarsa tabbas hakuri da tawakallin da ya yi zai haifar masa da wani irin farinciki da murmushi na mussaman daga wajan Ubangiji.

Yana zaune yana kallonmu shima fuskarsa a sake da alama ya ji dadin ganin yanayinmu ni da yaron ya dinga murmushi bai dai tofa ma komai ba a cikin maganar da muke yi har muka kammala ya juyo kansa suka yi magana kad'an kafin mu yi sallama gabad'aya ya kashe wayar yana kallona har yanzu da murmushin a fuskarsa idonsa a kaina ya furta." Na jima ban gan ki cikin nishadi irin wannan ba Giwa, ke ko kunya ba ki ji irin ta iyaye da yaransu na fari."
Ni ma da murmushi a fuskarta nake kallonsa haka kawai sai na ji wani bala'in sonsa ya kara ninkuwa a cikin raina.

Tabbas da sanya hannunsa da kuma kokarinsa tare da tasirin addu'ar da muke yi Kamalu ya kai matakin da yake a yanzu.

Na hangi abubuwa da yawa a tattare da yaron kuma ni ma na yarda bayan wahala sai dad'i kamar yadda da yawa mutane ke fad'in akwai haske cikin lamarinsa ina ji a jikina yaron zai zama abin alfahari gare mu bakid'aya..

Na ce." To ai ni ba mutuniyar da ba ce, addu'a kawai fa na yi masa akwai abinda na yi na rashin kunya bayan wannan?''
Ya girgiza kansa yana kallona bai ce komai.

Na kama hannuwansa a hankali na sanya idona a cikin nasa na ce." Ba ni da wata kalma da zan yi amfani da ita wajan nuna godiyata a wurinka.

Ka cancanci duk wani abu a wajena na gode Allah Ya saka da alheri yadda ka tsaya mini akan yaran nan ka ke yi musu wahala da jiki da dukiyarka Ubangiji Allah saka da alheri.

Yaranka Allah Ya kula da su."
Ya matse hannuna dake cikin nasa a nutse ya ce." Babu buk'atar godiya a tsakanina dake Amina ni ma ai kin yi mini alheri, kin cancanta kuma abinda ki ka haifa da wani namijin na sha gaya miki ki sa a ranki kamar da ni ki ka haifa, ni ne ubansu har yanzu kuma abinda nake ban yi domin a yi mini godiya ba ina neman aljannata ne."
Na ji idona ya ciko da ruwan hawaye kuma duk yadda na kai ga ganin na hana su zuba sai da suka kwaranyo ina so na yi magana na kasa kawai sai na fashe da kuka.

Ya kuwa ki'dime jikinsa har yana rawa ya d'an rungume ni a jikinsa yana fad'in." Menene kuma abin kuka abinda zai b'ata mini rai kenan me aka yi da za ki yi kuka Amina?"
Na kasa cewa komai saboda maganar ma da yake yi ta sake raunatar mini da zuciya na dinga yi cikin k'aramin sauti ya matse ni tsam a jikinsa yana dago fuskata tafin hannunsa yasa ya dinga goge mini fuska.

Na daure da yar rawar murya na ce." Na dai gode kuma ba zan fasa godiya ba Allah Ya saka da alheri."
Ya yi shiru bai ce komai ba sai shafa fatar hannuna yake yi ya kama hannun ya sumbuta a tsanake ya furta." Godiya za ki yi ga Allah ki kuma ajiye a ranki cewa yaranki ba za su yi maraici ba muddin ina raye.

To wannan ya wuce da sati uku muna zaune kalau zuwa yanzu hankalina ya d'an fara kwanciya dangane da lamarinsa da Nabila domin kuwa bayan rantsuwar da ya yi mini tun farko kan cewa ba zai aureta ba ya sake yin wata tare da jaddada mini cewa ko da Allah ya sake k'addara masa aure to ba ya tunanin zai auri mace kamar Nabila saboda a cewarsa ya hangi tarin matsaltsalu mabambamta daga wajenta.

Ranar dana kar'bi girki ya shigo da yamma anan gidana ya yi wanka ya shirya ya ce mini akwai ba'kin da ya yi yanzu zai fita zuwa guesthouse din shi..

Yana tsaka da kimtsa jikinsa Hajja ta kira ya daga suka gaisa da yake handsfree ne duk Ina ji tana tambayarmu da yara ya ce mata kowa lafiya sai na ji tana fad'in.
Chapter 248 · 0% Book details